page 15

63 9 0
                                    

Aneesah Mala, a 28 year old lady born of a Kanuri father and a Shuwa Arab mother. Mahaifinta ya kasance National security adviser na kasar Nigeria a shekarun baya ayanzu kuma shine Chief of staff na presidential villa gaba daya, ya rike makamai manya manya kuma yana kan rikewa dan yanada position yanzu haka a UN, mahaifinta ya kasance Babban aboki ga mahaifin Massa wato shehun borno sannan kuma mahaifiyarta kanwa ce ga mahaifiyar Massa, wato dai Massa cousin din Aneesa ne.
          Iyayen Aneesa su 2 kawai suka Haifa ita da kanwarta Nanah, iyayensu are filthy rich ,suna da mahaukatan kudi da shi kansa Alhaji Mala bai san iyakarsu ba, he is a multi billionaire amma duk Rabin kudin shi kanshi yasan bata tsarkakkiyar hanya ya Samu ba,
       Aneesah cikakkiyar ba amurkiyace sabida anan aka haifeta, anan ta tashi tayi karatu da duk komai nata na rayuwa. Zuwa Nigeria saidai suyi shi jifa jifa shima sai idan kakarsu ta matsawa Alhaji mala sai ya roki momynsu ta lallaba yaran kafin a taho nigeria, Aneesa macece mara tarbiya da da'a ba kamar kanwarta Nanah that is naturally gentle and calm, tashi acikin turawa da rashin tsayayyar uwar da zata dora su kan tafarkin addini shi ya kara daguza rayuwarsu , sudai suna amsa sunan musulmi ne amma manyan farillan musulunci basa aiki dasu  ko kadan ballatana aje ga kananun ayyukan da musulmi ya kamata ya dabbaka a rayuwarsa.
        Basu taso da komi ba sai tsananin jin dadi, hutu da Kuma Sanya boko agaba da duk wani alamarin yahudu da nasara. Aneesah mala bayan degree da masters din da take dashi a Computer science tana da sauran certificates na ilimi sunfi guda 10, boko kawai takeyi daga wannan sai wannan har tayi nasarar samun aiki a National Aeronautics and space administration (NASA) tun tana yar shekara 23, Nasa wajene da su kansu turawan ba kowa yake samun privilege din yin aiki a wajenba , samun aikinta a NASA shi ya kara fito da ita ainun fiye da da, she became so powerful and independent at a very young age bayan tulin dukiyar da babansu yake da.
         Aneesa tun tana college tayi signing da wata kungiyar mata dake fighting for Gender equality ( feminism) ,sun fara kungiyar su da kadan da kadan har yanzu tayi karfin da duk duniya ansan da organization din da irin yakin da sukeyi akan mata, this made her become so in fluential musamman a social media. 

Prince Massa na daya daga cikin yan uwansu da suka sani kuma suke dan hulda dasu sama sama sabida kasancewar iyayensu aminai kuma yan uwan juna ta bangaren momynsu, ta san Yarima Massa sabida kowa ya san su a borno sune masu garin, duk da tafi sanin kannenshi mata amma bawani can sosai sabida banbancin tarbiyya, Mahaifinsu Massa mutum ne nagari, adali kuma nagartaccen sarki kuma uba ga yayanshi, duk da kasancewar shi abokin Alhaji malah amma bai bari yaranshi su shaqu dasu ba dan baya son irin tasu rayuwar sam. Matarshi ba haka taso ba amma tasan shi baa yi mishi dole kuma baa kawo mishi wargi cikin iyalinsa.
        Yarima Massa shima a Anan USA yayi karatun degree shi na farko Dana biyu a fannin Aeronautical engineering ( Masu gyaran duk wani abu daya shafi jirgin sama)  amma ba gari daya da gidansu Aneesah ba, jifa jifa yake kawo musu ziyara gidan musamman lokacin Azumi da kuma Sallah babba da karama ko kuma Idan Alhaji Malah yazo gari.  Agidan ko yazo baya shiga shaanin Aneesa saidai Nanah, itace suke gaisawa harma su tattauna kan batutuwa da yawa,  Share Aneesa da yakeyi ashe hakan ba karamin bata ranta yakeyi ba dan ita macece mai mugun son attention, tana kaunar taga ana kulata ana binta ita kuma tana wulaqanci kamar ydda takeyiwa mazan kasarsu shan kamshin nan. Sai ta tarar da sabanin hakan for the 1st time Daga wajen Yarima Massa, wannan ya kara Jan hankalinta gareshi dama akwai guntun crushing da takeyi a kansa tun suna yara inda sunje Borno gida.
         Bayan wasu shekaru yarima already ya koma gida ya Fara aiki da Airlines  na kasa har Sannu ahankali ya Fara aiki da airlines manya manya na duniya irinsu Emirates, suna magana da Aneesah ta social media sosai mafi yawancin shi akan kokarinsa naganin ya chanja Mata raayi akan feminism ideas dinta, haka zai shafe lokaci yana nusar da ita tareda koyar da ita wasu abubuwa akan addini sosai iya iyawarsa yana fatan ta gyara, wani abun ta dauka wani abun ta bar shi anan yanda ya rubuto mata ,a lokacin da dan sauranta kafin tayi nisa sosai ta kara wings.
        Aneesah mala got so busy and big bayan ta fara aiki da NASA, ta tsunduma kan shaanin duniya da sauran planets mai makon hakan ya kara mata imani amma sai raunata imanin ta aikin yayi, duk da yanda ta zama babbar hajiya bata fasa maida hankali akan soyayyar ta da Yarima Massa ba, tana jin sonshi sosai sabida kyansa da class dinsa ga kuma riko da addini, waazin da yake mata a kullum yana burgeta duk da bata da lokacin wannan sam, but she feels she's okay with him being religious.

AFIFAHWhere stories live. Discover now