page 8

103 6 0
                                    

Bayan sati guda da bikin Hanan mukayi Jamb, center dinmu daya tare da su iky kuma a ranar tun karfe bakwai na safe mun gama shiri mun fito jiran baba musa ya fito da mota, mun shiga motar sienna mun zazzauna jiran shi amma shiru bai fito ba, yanke shawarar aikan munirah mukayi ta kwankwasa BQ ta kirashi har ta tafi sai gashi ta dawo aguje jikinta yana bari,

" kunsan cewa officer ne zai Kaimu? Wallahi gashi nan ya taho naga ya karbi key a hannun baba musa"

" ooooohh damn it! Ni wallahi bana son abunda yaya yake mana billahil lazi"

Cewar iky tana bubbuga kafar ta a kasa, ni da nake a gaban mota nayi wuff na kwashi jakata da ledar abinci da yakumbo tasa aka zubo mana kamar zamuyi tafiya na koma bayan motar, zamana ke da wuya ya bude gaban motar ya shigo , a take motar ta cika da kamshin turarukansa masu dadi, gaishe shi mukayi daya bayan daya ya hade gaisuwar da kalma guda,

"Kuna lafiya?"

Tun da ya fara tuqi babu wani acikinmu daya kara cewa uffan kamar ruwa ya cinyemu, tafiyar kusan minti 20 ta kawo mu jamb center din, alokacin kuma cikinmu ya kara durar ruwa dan tabbas zana jarabawa bata da dadi musamman exams irinsu jamb,  yaya Aliyu ya fito ya rakamu har cikin center din ya tabbatar da duk mun shiga venue din sannan yace zai je ya dawo ya dauke mu bayan awa 2, lokacin dama 8-10 ne. Lokacin da muka gama muka fito mun tarar dashi kuwa a wajen kamar yadda yace, jiki a sanyaye muka shiga motar dan jamb din wanann shekarar tayi wahala babu karya musamman iky da munirah da suke science students, ni arts nakeyi kuma na fisu mayar da hankali amma duk da haka Government da literature dinmu yayi wahala, 
         Tun a motar muka Fara cin abincin da yakumbo ta tanadar mana wanda dazu da safe da tana insisting akan mu tafi dashi nake ganin hakan baida amfani gashi yanzu ya mana amfani mukai ta ci kamar ba gida zamu ba.

Ta mirrow yake kallonta tana ta cin chips da plantain a dan mitsilin bakinta, mamakin yanda fork din yake shiga bakinta yakeyi....he wish he can record her, she looks so cute. Bai Ankara ba sai tsintar kansa yayi yana murmushi hakan kuma ba karamin tayar da hankalinsa yayi ba, baya son yanda zuciyarsa take jajibo mishi abubuwan da suka dangance ta, ba haka suka tsara da zuciyarshi ba....ba haka ya tsara musu rayuwa ba!

Har suka isa yayi parking motar ya fito, yana jin muryar iky da munee suna mishi sannu, bai amsa musu ba sai da ya jira suka gama fitowa duka sannan ya kafa musu warning akan cewa jamb result zai fito nan da kwana 3, kuma muddin basuyi kokari yanda ya kamata shi da kansa zai  dau mataki akansu, idan kuma sunyi kokari toh da kanshi zai sayo musu duk abunda sukeso , yana gama fadin haka yayi gaba abinshi cikin takunsa mai daukar hankali ,

Cirko cirko mukayi da jin abunda ya fada, harara na bishi dashi bayan ya juya ina mamakin wannan hali na matsi irin nasa,

"Tab wallahi gara tun wuri muje mu sami Abba mu gaya mishi cewa exams dinnan tayi wuya kada ma su sa ran zamu ci wani uban marks"

Iky ta fada dan tafi kowa tsorata, dan bazatayi wa kanta karya ba tasan batayi abun kirki ba,

"Speak for yourself dai iky, nidai nasan InshaAllahu Yar 200 dinnan bazata gagara ba"

Fadin munee tana bawa kanta duk wani hope, ita bata karaya,
Nidai bance komai ba na kwashi kwanukan mu da jakata nayi musu sai anjima na wuce ciki, a raina ina jin ko nayi kokari ko banyi ba babu ruwan ya Aliyu aciki, tunda ban taba jin ance ya cikawa Abba biyan School fees dinmu ba. Har na wuce main kitchen din gidan na juya na koma dan na kai foodflask da plates din hannuna ayi wanke wanke, saka kafata acikin kitchen din keda wuya mukayi karo , tray din hannunta mai dauke da flask din Ruwan zafi da plates na tangaran suka zube tare da farfashewa a kasa kamar an bubbuga da guduma, da sauri nayi baya dan kada na taka,

"Makauniyar inace ke da baki ganin gabanki ?"

Ruman ta fada cikin hargowar barin da akasa tayiwa ummanta, jiya jiyan nan aka sayo flask din ruwan zafin nan da shegen tsada,   abun Kuma ya hadar mata da cewa Afifan da bata kaunar hada hanya da ita ita ta ja wannan asarar

AFIFAHWhere stories live. Discover now