page 32

84 9 0
                                    

I have passed by so many eyes, but I only get lost in yours.
                                   ~Unknown


Abuja,
Nigeria

9:00pm.

Wawakeken gate din aka bude kafin Daga bisani tamfatsetsiyar motar ta shiga da gudu ta daidaita a lot din wajen zamanta. Compound din dallere yake da fitulu ko ta ina kai kace rana ce ma a lokacin ba karfe taran dare ba,  wani Driver ne ya tukosu tun daga airport din bayan sun sauka a jirgin daga birnin maidugurin tareda Yakumbo da kuma yarinyar dake zaune a wajenta zakiyya, driver ya sauko da sauri ya budewa Yakumbo yayin da shikuma Aliyu ya fito ya bude boot din motar, boot din cike yake kaya niki niki na akwatuna a hakan ma wai su Simon zasu taho da wasu a motar shi daya bari a yoben, kaya ne yakumbo ta taho dasu kala kala tun daga nata da diyar wajenta, kayan barka da dangi da abokan arziki suka tarawa Afifan harma da su kwarya da kuma tulin itace na wankan jego, su wadannan a mota zaa taho dasu gobe.

Aliyu yasa hannu yana daukan akwatunan yana fito dasu at the same time yana dariyar abunda yakumbo take fadi na cewa sai an dauko mata kujera ta taka sannan zata iya dirowa daga motar sabida ciwon kafa,

" Sannunku da isowa ranka ya dade"

Wata murya ta firta daga bayansa cikin wata hausa da bata fita kwarai kamar harshen ya nadu da wani yaren na daban, Aliyu ya juya yana dubansa cikin mamaki da kuma kallo na ina na sanka? Kamar imrana ya fahimci cewa ogan nashi bai ganeshi ba yasa shi saurin fadin yana dukawa cikin girmamawa

" Imrana ne , kwana na 4 da isowa na tarar kayi tafiya , hajiyar tana min waya na kamo hanya ai"

"Sannu da zuwa"

Kadai Aliyu ya fadi sannan ya juya dan cigaba da ciro kayan , da sauri kuwa imrana yasa hannu yana fito da kayan cikin azama yana karasawa dasu can bakim kofar falon, Aliyu dai yana ta kallon buzun yanda yake da zafin nama kuma tabbas akwai alamar nutsuwa a tattare dashi, Allah yasani ya amsa zuwan nashi ne kawai dan faranta ran Afifa, sannann bugu da kari yasani gidan na bukatar mai maintaining dinsa na musamman sabida kula da harkokin gida ba aikinsu simon bane, idan yace zai nemi wanda zai iya kuma anan garin abuja yawanci sai Christians din ko kabilu, kuma shi baisan su cika mishi gida a matsayinsa na musulmi dan bahaushe, zai yi kokarin gwada Imrana ta hanyoyi da yawa kuma in yaci jarabawa toh zai cigaba da zama dasu yana musu aikace aikace bayan yasaka masa albashi.

" kai farin yaron nan, maza shiga gida kace su baka kujerar tsakar gida na sauko tunda sadauki yaki ciccibo ni na sauko, yanzu sadauki tsakani da Allah ka doroni a jirgi sannan ka kara doroni a wannan doguwar motar mai kama da tsani, ka kyauta min kenan?" 

Yakumbo ya fadi tana yafito imrana da hannu tana murmushi, shima kuwa yayi dariyar yana fadin

" toh hajiya bari a karbo da sauri"

Yana rufe bakinsa kofar bangaren Aliyu ta bude, saaima ce ta fara fitowa da sauri ta rugo tana ta ihun murna tana fadin

" ga yakumbo! Oyoyo Ga yakumbo!! "

Ta isa ga yakumbon ta rungume ta tsam tana ta murna kafin ta koma kan yar uwarta suna ta tsallen murnan ganin juna, Afifah da murnan ganin yakumbo bayan tsawon watanni ta kusa kasheta a tsaye ta kasa ma takowa zuwa nan inda suke, kwakwalwarta duk ta rabu gida biyu akan shin ta ruga ga sadaukinta wanda kewarsa itama ta kusa karta ko kuwa yakumbon da take tsananin min kunyar ta ganta da tsinin cikin nan? Itafa harga Allah taso sai ta haihu sannann suzo, bataso kowa a gidansu ya ganta da cikin nan, anata ganin ba karamin abun jin nauyi bane.

         Tana sanye da jilbab dinta sky blue kato sosai tundaga sama har kasa ya rufeta ruf baa ma ganin cikin sosai sai an lura, jikinta ya kuma lailayewa yayi jaajir kamar ka latsa jini ya fito, ta dan kara kiba kadan wanda shima ya kara mata kyau ainun, bakinta mitsili yasha janbaki hot red color kamar yadda sadauki ya bukata dazu daya aiko mata da message.

AFIFAHWhere stories live. Discover now