Page 47

78 9 0
                                    

Assalam Alaykum!

Fatan na sameku cikin koshin Lafiya? Nima ina nan lafiya and im so excited to continue this amazingggg journey.....yes, just like you excited too.

************
************
All Roads Leads to you, even those I took to Forget you....

~mahmudDarwish

Diffa,
Jamhuriyar Nijar.

5:45pm.

Sahara (Desert) wani yanki ne da mafi yawan jamaar dake duniya basu taba sanin ainihin yanda halittar wajen take ba har su gama rayuwarsu a duniya su mutu, a lokutan baya saidai naga yankin a finafinai ko hotuna a wayoyi ko mujallu, a Lokutan baya saidai naji labarin yanda take da tsananin zafi da wahala ga masu zama acikinta ko yankin da sahara take. Amma meyasa na tarar da ita sabanin yanda ada muke hashashen ta? Ganin yanda na kamu da tsananin kaunar nazo cikin sahara yasani kara gane cewa tabbas baka shaidar abu saikayi rayuwa acikinsa ko da sau daya ne.......
Tafin kafafuwana da suka nutse acikin yashin ina jin dadin yanda dumin yashin ya lullube kafafuna tamkar na dorasu a saman rushi dake gab da mutuwa bayan ya yini yana ci da wuta, Dago fuskata nayi ina kara duban saharar dake zagaye da kwantaccen yashi duk iya ganinka saika zata a duniya babu wani waje sai nan din, Yayana Ahmad yace wannan saharar idan aka nutsa cikinta har kasar Sakkwaton Nigeria zata kai mutum. But thats not the beautiful part of coming here, The most beautiful part of it shine shaida faduwar rana, I never knew I could ever experience a sunset before, sai gashi tun a zuwan farko da mukayi da yayana Ahmad naga yanda Ranarta game duniya da wani irin girma ta fadi a gabanmu bayan kalar duniyar yayi jajir dashi, I was thrilled by that and I got addicted to coming here every two days.

" Ranki ya dade, ina ganin ya dace mu koma a yanzun"

Kuyanga Fidan ta furta a hankali cikin girmamawa da kankan da kai bayan ta matso gab da ni, Ban ce mata komai ba sai na ciro kafafuna Daga cikin yashin nan ina karkade su har na gama na dago tare da gyara zaman mayafin Laffaya ta mai kalar sararin samaniya ( Kuje ku kalli bangon littafin).
Kuyanga Fidan ta karbo wani jug daga hannun daya kuyangar dake can gefe ta tsugunna ta fara zuba min ruwa a kafar tawa, tana kokarin saka hannunta dan ta cuda nayi gaggawar rike hannun nata dan har yanzu na kasa sabawa da wannan bautar da suke wa ahalinmu, Nasa hannu da kaina na wanke kafar , Kuyanga Fidan tayi maza ta saka wani karamin towel ta goge kafar sanann na zura kafafuna cikin takalmana irin kalar laffayata, Tafiya kadan ta kawo mu bakin wajen da akayi parking motar data kawomu, Mota ce baka wuluk samfurin jeep, Dogarin da aka taho dashi ya bude min gidan baya na shiga na zauna sannan ya rufe, Fidan ta zagaya ta daya bangaren ta shiga itama ta rufe.
A kaida kuyangun gidan sarautar basa zama ko shiga mota tare da ahalin gidan sarauta saidai su shiga tasu motar daban, farkon zuwanmu da Ahmad haka akayi, a karo na biyu da zan dawo na ganni dagani sai direba naga sun shiga wata karamar mota zasubini a baya, a take na sanar da direban cewa a fadawa Kuyanga Fidan ta dawo nan kusa dani mu tafi tare, da kyar Fidan ta amince ta shigo dan gudun kada tayi laifi har saida na tabbatar mata da cewa babu abunda zai faru. Kuyanga Fidan itace babbar kuyangar da masarauta ta zaba min a matsayin mai kula da ni tun daga kan chambers dina, Abinci, suturu da duk sauran wasu abubuwa, Tashin farko jinin mu ya hadu da ita dan nasan zatayi saata a shekaru, she became My new Friend here and my biggest Ally, ahankali a hankali shakuwar mu tayi karfi sosai a iya tsawon wata guda da dan kwanaki da muka shafe nida Kinan.
Mintuna talatin ta dawo damu cikin gidan Sarautar a lokacin anata Sallar magriba a babban masallacin jumaan dake masarautar, Motar mu bata tsaya a ko ina ba Sai Main House inda daukacin Iyalan gidan suke rayuwa da matansu da yayansu, Unguwa ce Guda dake dauke da gine gine na gargajiya yet modernized but in a traditional way, basu yarda sun rushe gidajensu sunyi irin na bature ba amma duk wani kayan alatu na jin dadin rayuwa zaka tsince shi daga ciki, amma daga waje Ginegine ne mai dauke da jar kasa da Kuma olden architecture.
Ina gaba Kuyanga Fidan tana bina a baya mukai ta ratsawa ta faluka da soro kala kala har muka iso ginin da Matar Sarki wato Kanin mahaifina dake mulki, a bangaren matarshi ta farko wato Inna Rasshida nake zama nida Kinan, Sashen nata yana da matukar girma ainun dan shi kanshi yanada parlor tamfatsa tamfatsa guda 3, Dakuna kuwa bansan adadi ba dan daga dakina sai nata ne kawai ake rayuwa acikinsa kasancewar diyoyinta duk sunyi aure sun bar gidan saidai in wasu daga cikin jikokinta sun zo mata kwana. Ban iske Inna Rashidda ba dan haka na wuce dakina kawai still Fidan tana biye dani, Da sauri na shiga sabida nayi kewar Kinan sosai yau through out tunda muka tashi Yarima Ahmad ya zo ya daukeshi suka fita, zuwa yanzu nayi tunanin sun dawo Sai wata kuyanga tace min basu dawo ba.
A gurguje na shiga bayi nayi wanka tare da yin alwala na fito daure da towel, wata sanyayyar Khumra kawai na shafa ajikina batare dana goge ruwan jikina ba, wata dabara dana kara koyo awajen kanwar mahaifiyata Anty Hamama, murmushi nayi dana tuna cewa ta fadamin zata zo cikin wannan satin zasuyi tafiya, na shirya cikin wata Comfy Boubou mai mayafi light brown, daukacin jamaar gidan nan ire irensu suke sakawa ko kuma laffaya shiyasa aka kawomin nima sama da kala 30 kaloli daban daban. Na idar da Salla ina tasbihi da karamin casbahar dake hannuna, jira nakeyi Fidan ta shigo na bata umarnin zuwa a karbo min dana dan nayi kewarshi, banaso Kinan yana yin nisa dani sabida nasan irin lalurarsa kuma nasan yana matukar shan wahala a zagayen da Yarima Ahmad yakeyi dashi tunda bayason mutane.
Farkon zuwana nayi iyakar kokarina wajen fahimtar dasu irin lalurar dake damun Kinan ta cutar rashin Sabo (Autism) amma babu wanda ya fahimceni, saima cewa da sukayi Su sam basu da ita anan wai labarin kanzon kurege ne, Mai Martaba ya bada umurnin a karbo mashi magunguna daga wajen malamai manya masu bada waraka da ayoyin Allah, a sannu wadannan rubutun suka zama ruwan shansa, a cewar Maimartaba kuma tunda Kinan baya son mutane toh tabbas shiga dashi cikin mutane zaisa a nemi rashin sabon a rasa, dalilin dayasa kenan kullum ta Allah sai Yarima Ahmad yazo ya daukeshi ya kuma hadashi da babban dansa dan shekaru 10 mai sunan Youssouf, baa dawomin da Kinan sai dare duk da banaso amma ba yanda na iya, Tun yana ramewa yana min kuka idan ya dawo har kuma adan cikin kwanakin nan naga kamar ya fara sakin jikinsa har yana kokarin bani labarin wasan da sukayi a fada idan sunje.
Saida na tashi nayi Sallar Isha na idar sannan Kuyanga Fidan ta shigo Hannunta rike da tray mai dauke da shayin dayake wajibi shanshi duk rana waton shayinsu na buzaye, Fidan ta ajiye tray din a gefena sannan ta tsiyaya min a wani karamin cup yanata turiri sannan ta miko min hannu biyu sannan tace,

AFIFAHWhere stories live. Discover now