Rufewa.

116 10 2
                                    

          7 years later.
               Mid year
    The 3rd Night of Eid el fitr
     

House No DC439
Maitama, Abuja.

8:12PM.

Daukacin yanayin da harabar gidan yake ciki zaisa duk Wanda ya shigo gidan ya gane cewa tabbas wata yar kwarya kwaryar biki akeyi, harabar ya cika da hayaniyar yan yara dasuketa wasansu cikin annushuwa, yan matasan daga cikinsu kuma nakan wasu kujeru dake zagaye da table suna magana, wasu suna cin abinci wasu kuma rike da wayoyinsu a hannu.
               Daga gefe kuma Servers ne keta shige da fice da abinci da abunsha kala kala harma da nauikan snacks da desserts na alfarma, hadaddun warmers ne da aka zuba abincin aka kuma dauko servers dan suyi hidimar kaiwa kowa abincin yana daga zaune batare da an wahalar dakai ba. Dana nutsa wajen kallon tamfatsetsan harabar ne naga wani katon board ko ince barner dake dauke da Rubutun

"WELCOME TO THE JAJERE'S EID SOIRÉE"

Hakan na nufin cewa iyalan gidan General Mahfuz jajeren ne ke celebrating bikin karamar sallar a wannan dare, zagayawa na cigaba dayi dan na gano mana ina manyan bakin namu suke kuma suwaye suka halarta amma banga kowa ba, gadai round table nan dake dauke da kujeru dayawa kuma da alama anci abinci sosai akansa an tashi, hakanne yasa na cigaba da kurdawa cikin gidan har na samu nasarar shiga kananun falukan wannan gidan ina fita tare da kurdawa ta cikin corridors.......with every step towards them ina cigaba da jiyo muryoyinsu, hirarrakinsu da dariyarsu dake tashi sosai, dagaji kasan koma suwaye aciki tabbas suna enjoying wannan lokacin fiye da duk yanda ake tunani.
              Wata kofa na isa da nake iya hango cewa tabbas nan ne falon da masu gidan suke ciki, kodan sabida takalman dana gani a ajiye masu tsini da flats na maza, da kuma yanda servers din ke shige d fice da trays masu dauke da kayan dadi acikinsu. Abunda ya fara dalleri min ido da shigana falon shine hasken wata katuwar Chandelier data shige min ido kamar zata sauko kasa tayi magana, a hankali kyawu da alfamar wannan babban parlor ya tarwatsa duk wani tunani na yasanu kokonto anya akwai waje mai kyawun wannan gida a duniya.....it was Magnificent!!!
              

"Mhmmmm! I really really like this chicken kashoori! Who made it? Ikram is that you?"

The 30years old AFIFAH JAJERE asked with excitement on her face, har wani lumshe ido takeyi sabida dadinsa dake tsarga Mata, Bata yi kasa a guiwa ba ta juya ga Mijinta ta saka Mishi a baki shima dan ya gutsura yaji. Idonshi na kan wata katuwar Apple iPad dinsa ya gutsura kadan yaci shima yana jinjina kai sannan yace

" I like it"

The 46 years old LIEUTENANT GENERAL ALIYU JAJERE ya fada shima, Suna zaune akan wata kujera mai cin biyu shida matarsa kamar yadda IKRAM da mijinta FARUK , RAIS da matarsa SAADA suke zaune suma a tasu kujerar, MUNIRAH ce kawai ke zaune ita kadai Sabida mijinta bai sami halarta ba dalili na girma da kuma sarautar kasancewarsa Shehun Borno.
           Rais ya kalli Afy da harara a fuskarsa dake cike da gemu yace

"Ikram ce zata yi wannan delicious din a naki ganin? Toh my wife made it with lovee"

Dariya sukayi gaba daya dama saida Afy ta kefta musu ido kafin ta fadi hakan duk dan ta tsokani rais din, tasan already cewa Saada ce tayi kashori din coz tasha yi musu sunaci, hirarsu mai dadi suka cigaba dayi kusan mintuna 15 kafin Afifah ta danna wani dan bell dake tsakiyar table din dake gabanta, seconds kadan wata mata ta bayyana cikin hijabinta tace

" Gani Maamaa"

" Fati ace yaran nan su shigo gida hakannan its getting cold, ina Mahmoud? Abashi maganin murarsa na dare, duk dai kice musu su shigo"

AFIFA ta fadi tana Sanye da wani Luxury fabric burnt orange color dinkin fitted Gown, Tabbas wanda ya San Afifa shekarun baya ba lallai ya ganeta ba a yanzun, bama ita kadai ba, duk Wanda ke zaune acikin parlon nan ya manyanta , masu karancin shekaru sune Rais da Saada tunda dama shi kanin su Afy ne. They have all added weight, looking so matured and as well happy.
              A hankali muryoyin yaran masu kyau dasu suka fara shigowa cikin falon kowa yana nufar iyayensa. Mahmood da Tariq suka nufi Afifah suka rirrike kowa yanason bata labarin abunda ya wakana a wajen, Aisha da Khadee suka tafi wajen Ikram da Faruk,  Mustafa dan shekaru 4 ya isa ga mahaifiyarsa Munira ya dane kan cinyarta ya kwanta ajikinta.
Sukuma sauran manyan wato Kinan, Fannah da Saddiqa da sukeda shekaru sha biyu suka ware waje guda suna tasu hirar data shafesu.
           Kofa ce ta bude a hankali sannan ta shigo hannunta rike da diyarta yar watanni 11 a kafada daya hannun kuma wata siririyar walking stick dake taimaka ma mata wajen tafiya, tayi kyau sosai ta hade cikin wata atamfa Super Holland Dinkin straight gown dayasha adon duwatsu sai walwali take, ta karaso cikin falon fuskarta da murmushi UMMU RUMAN  tace

AFIFAHWhere stories live. Discover now