page 20

69 9 0
                                    

Shehuri

Bornu.

8:20pm

Zaune yake akan hadaddan dining table dake tsakiyar kayataccen parlonsa , Abincinsa yakeci hankali kwance duk da a badini damuwa ce fal ransa, damuwar baa kan komai bace face akan AFIFAH JAJERE! Ya kasa samo kanta sam, ya rasa ina ta dosa ya kuma rasa mai zaiyi riko dashi . shi ba yaro bane hana karya kuma yayi soyayya ba laifi da mata kala kala a lokacin samartakarsa, yasan emotions din mata kala kala akan soyayya, yasani idan mace tana sonka ko kuwa batayi, ya sani idan bata raayinka game da Lamarin soyayya, Unfortunately hakan take ga Afifah, ya gane yarinyar bata raayinshi game da soyayya amma tana matukar girmamashi da mutuntashi fiye da zato,  da bakinta ranar nan ta fada mishi cewa

" Na dade tare da Yaya Aliyu, Na dade da damka mishi zuciyata yaya Massa, nayi maka karya idan nace ba shi nake burin ya zama mijin aure na ba.....amma zanyi tunani kuma ina addua, banason yanke hukunci a cikin gaggawa"

Ta fada mishi lokacin suna tsaye a gefen sashen yakumbo, yazone kafa da kafa dan yasamu amsar tambayarta da taki fada mai, kuma a wannan ranar ya tarkata komatsansa ya dawo Borno, da nufin kara wasu kwanaki kadan kafin ya fara next aikinsa da babban airline dake Kasar kuwait. 
          Ya fahimce ta, ya kuma girmama gaskiya da kuma raayinta da ta fadi mai, amma ko kadan hakan bashine ya hakura ba, shi a nashi ganin shakuwa ce kawai mai yawa tsakaninta da Dan uwan nata, that is bound to happen kamar yadda shima ya shaku da Fauzee lokacin tana gidansu. Ko kadan bai girgiza da jin hakan daga bakinta ba duk da hope dinsa kaso 70% ya zaftare. But koma menene ,he still wants her! Zai hakura da Afifah kadai ne duk ranar da Mahaifinsa ya sanar mishi cewa baba general ya aiko a bashi hakuri, wannan ranar ne zai hakura gaba daya. A lokacin data fada mishi haka murmushi kawai yayi yace mata,

" Nagane Afifah, kiyi addua sosai, kiyi tunani and follow what your heart choses!"
      Ya fada tare da bata wata karamar Leda da yazo da ita, wani siririn Diamond Bracelet ne acikin akwatinsa....ya siyeshi a wani auction daya taba halarta a London a shekarar 2019 ,
yanata ajiyarsa ya rasa wa yafi cancanta ya bawa, ireiren wannan kyaututukan yayiwa mahaifiyarsa bila adadin , haka kannenshi mata, Aneesah doesn't want anything from him,ko ya bata a inda ya ajiye anan zaizo ya sameshi. Until he met Afifah, and he feel the bracelet was meant for her. Bracelet din an sayar dashi a wajen bajakolin ragowar kayayyakin da aka Samu a jirgin ruwan nan na ' TITANIC". that bracelet was sold for 5 Million a kudin nigeria!
         
Bude flask din waina yayi, ya dauki guda biyu ya rufe sanann ya kuma bude wani flask din ya debi miyar kubewa danya da taji naman talotalo zako zako kamar zasuyi magana,  yanaci kamar kunnensa zai tsinke, yanason Abinci, yanason abincin su na gargajiya da duk wani nauin abinshansu musamman kunun gyada, gyadar ma irinta mutanen Chad. Tablet dinsa dake gefe ta fara ruri alamar shigowar Face time, kuma ba kowa bane yake kiransa da wannan sai NINA, da sauri ya goge hannunsa da tissue ya dauki tab din ya ajiye ta yanda zata zauna kamar computer ,fuskar diyarshi ta bayyana a ciki ta washe bakinta tana fadin

" Daddyyyyyy"

" Hello Princess!"

Ya fada yana kai lomar waina at the same time yacigaba da hira da diyarshi cikin farin ciki da annushuwa , a hankali ya soma jin damuwar dayake ciki tana bin iska tana silalewa,  wayar telecoms dake manne daka can gefe jikin bango ta soma ringing, kararta ya cika falon,  daga falon Yagumsu ne, ta dawo kenan.
Ya ta shi ya je ya dauki wayar ya kara a kunnensa,

" Salam alaikum Ranka ya dade , Yagumsu ta shigo kamar yadda ya bukata a sanar dakai dawowarka"

Aka fada daga cikin wayar,

"Okay"

Kawai yace Sannan ya koma ga Nina sukayi sallama ya kashe wayar ya shiga bedroom dinsa, wani bedroom mai shegen kyau dauke da set of Royal furnitures Cream and burgundy color, abu mafi kayatarwa aciki shine zagayyayen gado mai circle shape dauke da ubanpillows sunfi goma, Massa ya cire kayan jikinsa ya chanja yana duban gadon, shi kanshi yana son gadon, a ranshi yana takaicin all these Masculine Strength in his body, all the warmth in this Magnificent bed amma babu mace, Babu mace da zata moreshi....what a waste!

AFIFAHWhere stories live. Discover now