page 39

91 8 2
                                    

Friday,
2Pm

Texas.

Karamin coffee cup na 5 kenan ta shanye tun bayan zaman ta anan  awa 2 da suka shude , wato tun karfe 12 Aneesah Malah ke zaune a St.Louis park kamar yadda sukayi alkawari zasu hadu da tsohon mijinta Yarima Massa, sha biyu daidai a kan karamin table din dake gefen garden din tayi mata kamar yadda aka san aladar bature da muntunta alkawarin lokaci. Ta kalli agogon hannunta yafi sau dubu tana kuma kallon kofar tana jira taga ta ina zai bullo amma shiru babu shi babu labarinsa.
            Abun ya bata mamaki matuka sabida tasan shi, daace bashida niyyar zuwa da tun a hypermarket dinnan zai fada Mata kai tsaye cewa bazai zo ba, sannan African time sam ba halayyarsa bace shima yanada girmama lokaci kamar yadda akasan duk wani mutum daya jima tare da Bature, amma yanzu da awanni biyu cur suka shude babu shi babu alamarsa ta gama yanke cewa bazai zo din bane, daman already yayi blocking dinta daga kiransa da duk wasu platforms da zasu iya magana tuni tun bayan ya rubuta mata takardar saki.
           Waiter din tayiwa alama da hannunta alamar yazo, ya kuwa taho da bill dinta na kofin coffee 5 data shanye, isowar waiter din gabanta yayi daidai da tozali da abunda ya haskaka kirjinta, ruhinta harma da rayuwarta gaba daya, batason lokacin data mike tsaye ba ta rufe bakinta da tafukan hannayenta tana kallonsu suna doso ta, kuka ne ya kufce mata a hankali sabida ta kasa rikeshi,

Yarima Massa ne rike da hannun Diyarshi Nina suna tafiya a hankali, Duk sunsha Jackets na sanyi sabida tsananin sanyin da akeyi a garin, shi akwai alamun Kaftan acikin rigar sanyin yayin da itama Nina aka sanya mata wata Sky blue long sleeve dress har kasa da takalminta mai kyau , wani abun karin shaawa da shigar Nina shine madaidaicin hijabi iya kafada daaka sa mata.
Yarinyar tana ta murna sabida yau daddynta yaje da ita masallacin jumaa gashi kuma ya kawo ta park dan tayi wasa, tana ta tsalle tana shawarar wani abun wasan zata fara hawa duk bata lura da mahaifiyarta dake can daura dasu ba, ahankali idon Nina ya sauka akan mamanta da tayi kusan wata 9 rabon data ganta ko taji muryarta ba, tsayawa tayi cak daga gefen Daddynta ta buya tana kallon Aneesa dake ta tsiyayar da hawaye,

" Nina, Ninani.....come to me"

Uwar ta fada tana durkusawa akan guiwowinta, fadin irin kewar diyarta guda jallin jal da tayi baa ma magana, amma deep down kunyar Ninan takeji, she gave up on her daughter, she sacrificed her daughter in exchange of freedom, ta yarda ta bada yarinyar duk dan sabida Massa ya saketa, does she even deserve to miss her daughter?
         Batayi tunanin yarinyar zatazo ba sai ganin tayi ta taho da gudu ta shige jikinta tana fadin

" Mummyyyyy"

Jin hakan yasa Aneesah kuma rushewa da wani irin kuka da yasata zama dirshen akasa tana rungume da Ninan, kissing din ta take aduk inda ta samu tana fadin

" I'm so sorry, I'm so sorry baby,"

" where have you been mummy? I know you busy with work right?"

Nina ta fada tana kallon fuskar mamanta, a lokacin hawayen Aneesah ne ya tsaya cak daga zuba dajin abunda Nina ta fadi, tun yarinyar batafi shekara 2 ba take yawan fada mata cewa ta rabu da ita aikin office ya mata yawa, babu shakuwa ko cikakkiyar soyayya tsakaninta da yarinyar, she has deprived her on daughter alot of things ciki har da breast milk. Yarinyar babu alamun tayi wani missing dinta can sosai, tadai tunata a matsayin wanda da suke rayuwa tare gida daya da nanny dinta dake Mata komai.
        Massa dake tsaye yana kallon ikon Allah yaja kujera ya zauna tare da kiran waiter ya kawo musu tea mai zafi snnan ya kawowa Nina milk latte, har waiter din ya kawo babu wanda yace wani abu tsakaninsu sai Nina dake ta matsa mai akan ya kaita tayi wasa, wata mata yagani zata wuce da danta shima zaiyi wasa sai ya roki alfarma ta hada da Nina , baturiyar cikin farin ciki tayi welcoming dinsu ta kuma hada danta da Nina dan suyi wasa, wajen ya rage dagashi sai Aneesah, yana dan sipping tea dinshi yana kallonta kadan, ta rame sosai.... Gani yayi tasa hannu a jaka ta bude wata roba ta zubo da kwayoyi kusan guda 4 ta bude baki ta kafa ta shanye babu ko ruwa, abun ya kuma daure mai kai.

AFIFAHWhere stories live. Discover now