SHAFI NA SHIDA

79 5 0
                                    

*MAI SAƘO*
   *(GARIN NEMAN GIRA..)*

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*

 Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8

   06.

Meenal sukuku ta wuni washe gari har zuwa bayan la'asar cousin's ɗin nata mata basu wani damu da ita ba after all sun ɗan girmeta sannan kuma ta cika shariya batada sakin jiki, ƙarfe huɗu da rabi Bashir ya shiga ɗakin da ta ke a kwance a sameta ta lumshe ido kamar me bacci duk da ba wai baccin ta ke ba

"Kee" ya kira ta a ɗan tsorace ta tashi zaune jin muryarsa lokaci guda gana gyara rigar jikinta "kinyi salla?" Ta ce "Nayi." Ya ce "To tashi shirya mu fita." A hankali ta ce "To yaa Bashir." Juyawa ya yi ya na cewa "Don't waste my time Meenal." Da sauri ta sakko daga kan gadon ta ɗauki wani desighner ɗan kwalin turawa ta ɗaura a saman sumar kan data baza saman kafaɗunta sannan ta saka wani ubansun wage hill ta ɗakko wata desighner side round bag ta saƙalo daga wuyanta ƙarƙashin gashinta zuwa shoulder ya crossing in between her big boobs ya tsaya side sannan ta shafa lip balm da zallan eye liner a idon ta ta fesa turaruka na tashin hankali ta fito tana taku ɗaiɗai duk da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar cewar ba shakka batada walwala, ta yi kyau ainun na kallo ka lara kallo amma shigar sam ba ta yaran musulmi ba, Ba kowa a parlour ya sanya ta fita ta wuce parking space inda anan ta ke tsammanin ganin Bashir, daga sama har ƙasa bash yake kallonta har ta ƙaraso kusa dashi, yana kallonta ya ce "Meenal are you insane! Wait where on earth do you think you are going dress like this?" Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli simple dresssing da ta san ta yi, lafin tece

"Yaa Bash what's wrong with my dressing or you want me to wear to something classy sorry kace nai sauri shiyasa na fito a haka." A ƙufule ya ce

"So you are just big for nothing ko? In your own tiny brain and empty skull you think wannan ne wayewa ko? My friend go and change to something worth your body as muslima." Jikinta a mace ta juya cikin gidan ba jimawa ta fito sanye da ɗamammen wando da wata round neck crop top sai ɗankwalin still da ke kanta ta canja takalminta zuwa wasu fine and classy unique lowpass farare ƙal, sake baki ya yi hangota tana tahowa har zuwa sanda ta ƙaraso kusa da shi, a cikin rashin walwalar da take don har ga Allah har lokacin abubuwa biyu tsaya a rai na farko dai ganin da Bashir ya mata ya gayawa Zuhair ya sanya ganajin kunya da nauyin dukkansu na biyu kuma rashin kallon abubuwa da ta saba kalla ya saka takeji a jikinta tamkar mara lafiya, kallonsa ta ke ta ce "Yaa Bash is this ok?" Yana wurga mata wani kallo ya ce "ke bakida atamfa ne wai ko wani kayan bahaushe sai wannan tsigaggun kayan?" A hankali ta ce

"Bana zama comfortable duk sanda na saka shiyasa Momy ta daina ɗinkamun banida anan yanzu sai a gida, yana saurin takurani yaƙi shiga jikina." Tsaki yaja kafin ya ce
."get in." Ya buɗe driver's sit ya zauna ya ja suka bar gidan.

*************
   Ta jima tsaye a wurin tana tunanin ta inda zata fara ga ƙarfe tara ta wuce kuma wayar bakanikenta yaƙi shiga, tsaki taja a karo na barkatai, mai  adaidatan ne ya tsaya kusa da ita ya ɗan leƙo kai waje sannan ya ce "Hajiya zakije wani wurin ne?" Dubanta ta mayar a kansa sannan a raunane ta ce "Wallahi bawan Allah kaga dafa office nike kuma kawia motar ta mutu nayi iyakar dubana ban gane menene matsalar ba kuma makaniken da ke dubamun motar wayarsa a ƙulle ya ke."

"Subhanallahi Hajiya bara inzo in duba miki duk da ba kayan aiki a tare da ni amma ai ni ɗinma makaniken ne wannan keken ba hawa nike ba sosai ba sai dare idan na baro wurin aikin kanikancin nawa." Cikin jin daɗi ta ce "Kai wallahi daka taimakamun saboda gaskiya na makara a komawa gida." Gyaran parking ya yi sannan ya sakko ya shiga duba motar ba jimawa ya fito yana kallonta kafin ya ce "Hajiya gaskiya wank electrical problem ne dole sai an nemo ruwaya ni panalbita ne a garejin ban ƙware a wannan panning ba abin da zai faru ki bawa masu shagunan tsaron motarki idan ya so muje inga gidanki in ajiye idan kin amince fa kenan sai in kira wani ruwaya yanzu yazo ya duba inyaso zan maida miki motar har gida." Shiru taɗan tunani tare da ƙarewa motar kallo kafin ta yi magana ya ce

MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)Where stories live. Discover now