*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
Payment details
8103943903
Opay
Ssfiyya Galadanchi
N500
Vip 1k.30
Baba ta shaɓa ado sai Zariya ta tafi inda Aminya suka zauna zamar tsara biki Aminiya na kallon ta tace "ƙawas kinga ai boka yace baya jin sihiri ita sabida tsabar kusanci da Allah shegiyar, wannan duk kinga makirci nane ya kamata ga amince da aurennan to gaskiya idan shawarata zaki bi kar aurennan ha wuce ranar juma'a idan kuma kikayi wasa wannan shegiyar kawar tata ta zugeta sai kkma neman sanadaki, kinga dai wannan ma Allah ne ya bamu nasara akansu don haka tun wuri kisan abinyi." Tana duban Aminiya kamar yanda take kiranta ta ce " To ba shagalin biki kenan?" Kyabe baki Aminiya ta yi
"Wane irin shagali kike magana ke ina ruwanki da shagali Fisabilillah banda dai neman magana da son jafa'i? Ki rabu da su kawai kina komawa kice juma'ar dama rana i ta gobe kenan amma gaskiya dubu hamsin zaki bani." Baba na murmushi ta ce "Aminiya raina fansa ne agareki abin da yafi hamsin ma yaune ake tare aminiya da ba dan ke ba da tuni bamu aika uwarsa lahira ba ai sha kuruminki kamar kinyi kisa a gaban ɗan sanda." Dariya suka kwashe da shi Aminiya ta ce "Boka yace bazamu taɓa nasarar aiki akanta ba amma yace tanada sauƙin mai da rauni muyi amfani da rauninta mu kwashi rabonmu." Baba tace mutumin fa shine ki indi ko meye na kamfanin su yanzu ke har kike maganar wata dubu hamsin nan gaba ai sai dai ke kiyi kyauta da dubu hamsin don kinfi ƙarfin miliyan ma." Shewa suka ƙarayi sannan ta ce"Shi kuma sakaran ya zamyyi da shi yanzu?" Aminya ta ce "A a shi ai tun asali mejin magana ne yaro me biyayya ina ruwansa da boka? Kedai kawai kici gaba da danne duk wata ƙyayyarsa da kike ji ki samu ki tara abin da kika tara a wurinsa idanma kinga cewar samun bame yankewa bane kawai ki lafe aci arziki." Nan suka wuni suna abu ɗaya sai yamma Baba ta dawo ta tashi fitinar aure juma'ar sama.
Cike da takaici Dr. Fatee ta kalli Nasare kafin ta ce "Kada ki aikata abin da zai curar da ke Dr. Koda ace wasiyyar yallaɓai ne ke taki zuciyarfa?" A hankali ta dubeta sannannta ce "Wallahi Sister Fatee ina masifar son Saif,.son da inaga ko kaina bana yiwa irinsa bansan ma yaushe nayi developing this strong feeling ma Saif ba, nayi nayi in yakice sa a raina na kasa." dr. Fatee tana jinjina kai tace "To ai Dr. Anyi me wuyar na farko dai kinga kina son shi na biyu kuma yanada halaye nagartattu matsalar biyu ne anan, farko dai shi bamu san nashi ra'ayin ba na biyu kuma wallahi wannan uwar tasa is up to something sai ki ƙara riƙe addu'a ba saiti akanta and she is up to no good." Dariya me sauti Dr nasare ta yi "Ina ma kika sani wai cewa tamun in bata kuɗin yayin biki ita da 'yan uwanta da kawayenta kiji fa? Matar datace ba shagali." Dariya suka yi sannan cikin sako serious face Dr. Nas tace "Ina da wani damuwa." Dr. Ta kalleta alamar tana jinta
"Saif ya fara rainani wallahi kinga yanzu so biyu yana cemun Hauwa bayan haka ya kira Nasara so ɗaya to yanzu ma sai ya ƙi kiran sunana kawai sai dai sannu da zuwa ko ina wuni idan mun hadu duk bama wannan ba wai Siaf yau zan fito har na shiga mota fa Iliya zai kawoni yacemun wai in fito zeyi magana da ni sai kinga fuskarsa kamar wani ubana kinsan me ya ce mun?" Dr. Fatee ta na dariya tace sai kin faɗa itama tana dariya ta ce "Cemun ya yi wai in riƙa saka hijabi." Suka kwashe da dariya Dr. Fatee ta ce "Wannan Chemistry ƙatoto da ke tsakaninki da yaron nan sai dai muyi shiru abinmu amma yana bada kala, yaro ƙarami da kishi." Dr. Nas ta ce "Ba ƙarami bane fa he s 35 yama kusan36." Da mamaki Dr Fatee ta ce "But he looks younger than his age." Suka saka dariya nan dai suka rabu, ai kuwa tana zuwa gidan ta tarar yana zaune tare da Baban Audu suna cik gyaɗa dafaffiya suna hira kallo ɗaya ya yiwa motar ya ɗauke kansa, befi mintuna goma da shigarta ba ta kirasa a waya
![](https://img.wattpad.com/cover/377851722-288-k995098.jpg)
YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
General FictionRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????