*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
Free pages na gab da ƙarewa kuɗinsa N500 ne ba yawa yi ƙoƙarin mallakar naki lafin free pages su ƙare.
8039424298
Opay
Balkisu Musa
07084161619.17.
Saif ne a gidan yau wuraren karfe 11 na safe, yayi yayi ya jure ya kasa jurewa wata uku bai saka Meenal a ido ba kuma yaji ance ta zata fara zuwa school a bakin antinsa. Knocking ya yi ba kowa a parlour tana ɓangarensu a kwance kamar ko yaushe, me aikin da ta shigo don ta gyara parlor ce ta tako ta buɗe masa, sun saba gaisawa ada idan yazo kawo saƙo ko karɓa, gaidashi ta yi sannan ta ce "Gashi Dr. Sun fita bata kuma bada wani saƙo in ajiye maka ba." Murmushi ya sakar mata kafin ya ce "Wurin Meenal nazo ai tana ciki." Ɗan jin ta yi sannan ta ce "Meenal tana ciki saboda batada lafiya ai ta fara zuwa makaranta tun sati uku da suka wuce kasan yanzu an zama yan mata aji huɗu take." Batare da ya kalleta ba ya ce "Nasani jeki tasomun ita mu gaisa." Hanya ta bashi ya shigo ciki sannan ya nemi kujera ya zauna , shiga tayi sai kuma ta dawo bayan mintuna kaɗan ta ce "Wai bazata iya fitowa ba amma ka shigo." Ɗan jim ya yi sai kuma ya miƙe ta rakashi har Kofar ɗakin sannan ta juya zuwa aikinta, a zaune ya taradda ita bakin gadon kallon guda ya mata ƙirjinsa ya mugun dokawa, tayi wata mahaukaciyar rama tayi fari fat kamar zabaya, kana ganinta kasan batada lafiya." Da sauri ya zauna a kusa da ita cikin tsantsar kulawa ya ce "Mimi were you sick dama?" Murmushi ta yi sannan ta ce "Yaya Saif sannu da zuwa." Yana mata wani kallo ya ce "Bakida lafiya Mimi whats wrong with you? Bakya ɗaukar wayana daga bayama sai idan na kira wayar a kashe baya shiga kwata kwata, mena miki ne ? Idan har saboda ban cika alƙawarin dana ɗauka. bane kiyi haƙuri yanzu na shirya zanyi abin da kike so." Murmushi ta yi mai wani irin ciwo, at her age tasan baƙin ciki, at her age tasan ta saɓawa Allah me muni irin haka bata ƙi kowa ba sama da yanda ta tsani iyayenta, bata taɓa sanin cewar 'ya'ya na tsanar iyayensu ba sai yanzu, ita da Zuhair kwata kwata basa magana amma yana iya dubata so ashirin a rana, da kanta ta tabbatar koma me ya mata yafita shiga damuwa, ya rame ya lalace, gata a kwance kusan 3month duk wanda ya ganta yasan ta rame kuma batada lafiya amma ace banda su mom kullum sai suce Typhoid ko malaria, da ƙyar ta ce "Su Dad bazasu aura5r da ni ba yanzu Yaya Saif, karka damu kaji, kuma wane auren ma nida zan mutu kai bakaga banida lafiya ba." Wani irin kallon mamaki ya mata kafin ya ce "Wane irin mutuwa kuma Mimi? Waya gaya miki cewar ciwo mutuwa ne ai kowa ma yana ciwo amma ke meke damunki." A hankali ta ce"Cewa aka yi Typhoid ce da malaria." A hankali ya ce "To zance Babarmu ta miki kunun sanga sanga shine maganin Typhoid kinji, da zaran kinsha yau zuwa jibi har ƙwallo zaki iya yi." Kallonsa kawai ta ke sai kuma ta ce"Yaya Saif ance duk wanda ya aikata Zina wuta ake sakashi ko?" Hannunta ya riƙo
"Muddin aka ce inhar ya mutu yana kan wannan aikin be tubaba to ba abin da zai hana a saka shi a wuta, amma idan mutum ya tuba da nufin bazai ƙara aikata zunubi ba to in shaa Allah sai kiga Allah ya yafe masa kwata kwata." Shiru ta ɗanyi sai kuma ta ce "To shikenan na gode." Kallonta kawai ya ke ya kasa cewa komai ko mahaukaci ya kalli Meenal ya san bayan rashin lafiya akwai dakuwa a tattare da ita amma ya zaiyi? Ya kula bazata yi magana ba har abada indai akan damuwarta ne amma zai mata addu'a in Shaa Allah. "Na zone kawai inganki Meenal zan koma amma gobe zan zo kinji." Ya ƙarashe maganar yana miƙewa Kallonsa kawai ta ke amma ta kasa cewa komai har ya juya zai fita muryanta ya na rawa ta ce "Yaa Saif " juyowa amma bai dawo ba ta ce "Idan mutum yanajin nauyi a ƙirjinsa kuma yana kasa baccin dare kamar dai wani abu yana damunsa amma be san ko meye ba me ake yi?" Murmushi ya sakar mata sannan ya ce " Alwala zakiyi Mimi ki yi sallar nafila acikin dare ki roƙi Allah yafiyar kura kurenki idan akaai ƙaddarar da ta faɗa kanki you try as much as you can ki roƙi Allah ya musanya miki da mafi alkhairi bazan tilasta miki gayamun damuwar ki Mimi, amma ki gayawa Allah duk dare kiyi tsayuwar dare, koda bakida wani laifi da kike ganin kin aikata mara kyau ki riƙe istigfari sabida mu 'yan adam masu aikata laifuka ne har a cikin rashin sani, ki yawaita yin istigfari da wanann zaman shirun gwara ki lazimci istigfari da salatin annabin Rahma yanada kyau karanta "Allahumma ajirni mina naar so uku, Allahumma inni as'alukal janna so uku sai kuma Allahumma inni a'uzu bika min azabal ƙabar, ki dage da yiwa Allah kirari sosai ki roƙeshi akan ya yaye miki dukkan damuwar da ke cinki, in Shaa Allah zakiji sauƙin koma meye, ba lallai sai cikin dare ba yanzu ma zaki daura alwala ki ɗauki al'kurani ki karanta domin shi alkurani waraka ne akan dukkan komai." Wani irin sanyi taji jin maganganunsa a hankali ta ce "Na gode in shaa Allah zan fara daga yanzu." Sallama ya mata ya fita a gidan ranshi a ɓace.
YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
Aktuelle LiteraturRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????