SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

96 3 1
                                    

*MAI SAƘO*
   *(GARIN NEMAN GIRA..)*

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*

 Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
*FREE PAGE*

Paid book to subscribe 8103943903 Opay Safiyya Galadanchi. 07084161619.

*Munada yajin maza da zai taimakawa Oga ya yi lasting on bed, bai kamata kina fama da kanki ba kullum kina kashe kuɗi kina gyara jikinki akan 30 seconds man ba, Please buy this our very own power rangers powder which is 100% natural ingredients ki gode mana later.*

    23

Wani irin faɗuwa gaban Zuhair ya yi da sai da ya dafa bangon da ke kusa da shi tsabar jirin da ya ji yake ɗebar shi, Dr. Umar ne ya bar abin da ya ke ya yo kanta shi da nurses biyu, Zuhair kasa yin komai ya yi har zuwa sanda aka ɗauke mahaifiyar sa zuwa emergency room saboda a yi stabilizing na condition nata, musamman Dr. Ashraf shine ya ke duba ta shine kuma likitanta sabida Zuhair duk ƙwarewarsa jikinsa yana saurin mutuwa sai yay ta kuka kamar ba saboda ita ya zaɓi wannan ɓangaren ba. Zuhair banda bugawa ba abin da ƙirjinsa ya ke gaba ɗaya ya hargitse ya shiga damuwa da rikici mara misaltuwa, duk da hakan bai hanashi tsayawa tsayin daka wurin ganin cewar an tsayar da zubar jinin da yarinyar ke yi ba.......

*WAIWAYE*

*SHEKARUN BAYA.*

Tun bayan da Mimi ta rasu Saif bai ƙara zama mutum ba har aka yi watanni biyu, ya rasa kuzarinsa, yauma kamar kullum suna zaune shi da mahaifiyarsa a parlon challet da suke zaune ta kalleshi da damuwa a fuskarta kafin ta ce "Yanzu kai Saif haka zaka zauna? Ace kwata kwata ka dawo wani iri bakada wani aiki sai zuwa kai matar wani ƙato wurin aiki da kuma ɗakkota sai kuwa cefane a haka zaka ƙare a wahle yanda ubanka ya ƙare kai ke nan ma dake kayi karatun boko." Ɗauke kansa ya yi daga dubanta saboda yanda maganar ta cake sa a ƙirji, cikin kyaɓe baki ta ce "Saifullahi ka ci gaba da neman aikin gwamnati yafiye maka wannan tambaɗewar sa lalacewar a gindin tsohuwa." Baice mata komai ba shi dai har ta gama bayananta a hankali ya gyara zamansa daga kishingiɗen da ya ke sannan ya ce "Babanmu zan nema amma don Allah ki daina sako sunan Baba a maganarki don Allah." Tsaki taja gajere sannan ta miƙe tabar wurin, shiɗinma barin wurin ya yi ya wuce part ɗin Anty ransa a ɗan ɓace, da sallama ya shiga ba kowa sai Ayiya da ta fito daga kitchen ga akama ita ma wucewa zatayi ɓangarensu gayar da shi ta yi ya amsa yana cewa "Ina Anty?" Tana murmushi ta ce "Anty ta shiga wanka tun ɗazu nasan ba jimawa zata fito." Kan ya yi magana Antyn ta fito cikin shiga ta Alfarma kallo ɗaya zaka mata kuwa ka tabbatar tana cikin tsananin farin ciki, shi ɗinma duk da damuwar da ya ke ciki bai hana shi sakin fuskarsa ba ganin for the first time in a while Antynsa tana farin ciki, a hankali ya ce "Anty yau farin ciki ake agidannan any good news." Tana  murmushi saboda yanzu ita da su Saif kaman 'yan uwan juna bata taɓa treating nasu as wasu 'yan aiki ko masu ci a ƙarƙashinta ita 'yan uwa take nema kuma har cikin zuciyarta ta aminta da su tana washe haƙora ta ce "Kid bro oya guess what." Yana dariya ya ce "Dubu nawa zaki bani if i guess right?" Da wani super excitement ta ce "500k." Dariya ya yi itama Ayiya ta dara sai kuma ya ce "Is Our Odogu on his way." Wata irin dariya ta kwashe da shi mai sauri da bai taba ganin tayi irinsa ba sannan ta ce "Kaga Allah you cheated did you both speak kan cewar zezo? ." Zama ya yi kafin ya ce "Anty kawai ki bani kuɗina ba wani cheat anan." Zama ita ma ta yi tana gyara ɗankwalin kanta kafin ta ce "Caca dai haramunce." Ayiyah duk ta fisu kwashewa da dariya jin Anty ta nemo mafita a cikin sauƙi, da wani irin yanayi mai cike da shauƙin nuna zaƙuwa a maganar ta tana kallon Saif ta ce "Kid bro Yallaɓai ya ce mu sameshi train station ya kusa isowa, he really took me by surprise don Allah muje, kasan ina fushi dashi ai be barni naje ba kuma shi be zo ba as he ptomised"  Miƙewa tsaye ya yi yana dariyar da ke ƙara masa kyau kafin cikin zolaya ya ce "Yau dole ki mana rabon kudi Anty muje kawai a shirye nake ai ba zamu bar yallaɓai yana jira ba ai."

MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)Where stories live. Discover now