SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA

45 3 0
                                    

*MAI SAƘO*
   *(GARIN NEMAN GIRA..)*

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*

 Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8

Free page.

   26

Ƙofar ɗakin ya buɗe mata sai da ta fita ya ɗaga key da ke nan kan table ya rufe ɗakin sannan ya ruga reception yakai musu key kafin ya tafi waje ya tarar tana tsaye jikin motar ta saka abaya baƙa ta yane kanta da zallan mayafin abayar wani kalan kyau ta masa sai ƙamshi take zubawa kawar da kansa ya yi sannan ya buɗe mata gidan baya ta kallesa cikin dakakkiyar murya ta ce "Saif yaushe muka fara haka da kai?" Shi ɗinma ya tsatsareta da idon sa dake nan manya masu kyau ya sha mur sosai cikin rashin kulawa ya ce "Nace fa Anty?" Hatsala ta ƙara yi ta ce "A bayan mota nike zama dama idan muna tare." Yana wani shu'umin murmushi ya ce "Ba haka bane you will be more comfortable a bayan ba wanda zai dameki." Kallonsa sosai take tana so ta gano inda zancensa ya dosa amma ya kakkafeta da ido har hakan ya yi tasiri a gaɓɓan jikinta ta yi hanzarin zare nata idon a nashi tana shirin basarwa ta faɗa mota a fusace ya rufe mata yana murmushin dake ƙara masa kyau duk sanda ya yi, ya zaga ya zauna ya tashi motar ya doshi babban kampanin na mijinta na sarrafa taliya da macaroni dake da office anan abuja wanda head office nasu yake can a lagos. Tunda suka fito a motar  ake kallonsu sai yanzu itama ta kula da wnai arnen suit da ya saka yaci cover sue black sai ƙyalli ya ke ya yi kyau ainunz sumar kannan tasha gyara da mayuka an wani ɗaureta a tsakiya da wani siririn roba gashinan wani kalar kamar balarabe a haka wai direba ne? Amma tun yaushe yanzu ta fara gano cewar fushi yake saboda ta ce ya dameta ohh shi kuma haka ya ɗauka take nufi?? Har suka isa ɗakin taron kallonsu ake sai da kowa ya bayyana sannan aka fara gudanar da meeting inda daga bisani ta tabbatar musu cewa ƙaninta Saifullahi shine zai zama MD na wannan wurin ta musu introducing  nashi anan aka shiga hidima dashi duk kansa ya ƙulle nan masu kawo wancen su kawo haka ya zauna wuni ɗaya da tulin aiki a gabansa ta kuma sharesa don fushi itama take wannan Chemistry ɗin hmmmm
  Har suka yi sati ɗaya da kwana biyu a garin kowa jin kansa yake kowa ya ɗauki fushi, barinma yau ɗinnan da wannan ne karonsa na uku yana zuwa hotel ɗin sa dare yana samunta da wani mutum dake aiki a Company wanda shine Deputy treasury manager, yau ma ransa a ɗan jagule ya ƙarasa suka gaisa sannan ya wuce ciki ya karɓi key ya wuce ɗakinta ya zauna a parlour ya rasa ma dalilin dake haddasa masa suyar zuciya ji yake kamar ya mutu tsabar fitina, sai wuraren 10 ta shigo ɗakin, tana knocking ya buɗe mata ta shigo ya tsatsareta da ido ya kuma ƙi bata hanya ta wuce kallonsa take da mamaki ganin abin da yake idon sannan sunyi jajir kamar gaushin wuta ɗna faɗuwa gabanta ya yi amma sai ta dake ta ce "Saif meye haka?" Sai a sannan a ɗan saaisaita nutsuwar sa yana mata wani kallo ha bata hanya ta shige ya juyo batare sa ya shirya fitowar kalamanba ya tsinkayesu "Shi kumwa wannan me yake zuwa yi kullum ne wai? Duk abin da zai faɗa ba zai faɗa a office ba sai kin dawo masauki ya biyoki duk dare." Cikin rashin nuna damuwa da yanyinsa ta ce "To kai kuma ina ruwanka da shi ko da ni? Duk abin da kaga bai faɗa a office ba ka gane is personal mana yaushe muka fara haka da kai Saif? Ina ruwanka da personal abubuwana hakan yana nufin cewar na baka dama da yawa ko ka rainani son ranka, harka isa kazo ka ajiyeni kamar wani ubana kana tuhumata dalilin tsayuwa da wani what nonsense?" Da ƙarashe maganar muryarta a sama, wani kalan runtse idonsa ya yi jijiyoyin kansa suna wani irin rikitaccen harbawa, jikinsa yana karkarwa idon nan koda ya buɗe su sunyi jajir yama rasa takamaime meya haddasa masa shiga wannan yanayin shin maganganunta ko kuma tsabar ɗacin ganinta tare da wani dayake, sake lumshe idonsa ya yi yana rarrashin kansa tare da ƙara jaddawa kansa cewar ina ruwanka? Ajiyeta kayi? Wannan ai wuce wurine? Duk waɗannan maganganun a ransa yayi a sarari kuma cikin kamewa da danne zuciyarsa ya ce "Kiyi haƙuri ranki ya daɗe bazan ƙara ba." Tsaki me ƙara taja kafin tace "Har yaushe nayi lalacewar da zaka ajiyeni kana tuhumata akam wanda yazo wurina? Ina ruwanka da rayuwata ko kai makahone baka fahimtar ni da kai ba sa'anin juna bane sakarcin banza." Shiru ya yi harta gama sannan ya ce "Kiyi haƙuri." Bata kulashiba har ya fita tanajin yanda ta buga ƙofar tabi ƙofar da kallo sai kuma jikinta ya yi sanyi, ya zamar mata dole ga gyara masa zamansa don taga kamar tunda aka yi maganar aurennan yake wani jin hayaƙi akansa, babu shakka Alhaji Mukhtar zata bawa dama ya turo akai ƙarshen maganr da zaran sun ɗauki tsawon wata biyu suna fahimtar junansu......
  
    Saif a wannan daren kasa bacci ya yi da safiya kuwa sai wani mugun zazzaɓi ya masa dirrar mikiya ya rufeshi sosai har ya rasa madafa, kasa zuwa office ɗin ya yi saboda zafin zazzaɓi sai wuraren 12. Sannan Anty Nas ta kirashi kamar ya share zai kuma ya ɗaga kiran tare da yin sallama cikin fada ta ce "MD meye haka? A office yau ya kamata mu gama abin da muke mu koma kaduna akwai babbabn aiki a can ɗin tayaya zaka ƙi fitowa har yanzu." A hankali ya ce

MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)Where stories live. Discover now