SHAFI NA GOMA SHA BIYU

58 4 0
                                    

*MAI SAƘO*
   *(GARIN NEMAN GIRA..)*

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*

 Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
Ina matan da suke kashe kuɗinsu ba dare ba rana suna gyara amma mazajen suna nan en 30 seconds??? To taho ga POWER RANGERS NA KAWO MIKI

Akwai wani haɗaɗɗen maganin maza wato idan kika bawa namiji yaci bazai samu sukuni ba a duk daren sai aikin nafila da noma. Kuma abin burgewar maganin just 4k bayan haka zai miki lasting for almost 3 to 4 months don ba'acinsa da yawa sunan Maganin POWER RANGERS.... Ɗan kaɗan zaki baɗa a shayi ko a miya.

07084161619
SOKOTO NATIONWIDE DELIVERY
  

12

Meenal har azahar bata fito daga ɗakinta ba saboda kuka shi kuwa kimtsawa ya yi ya fice agidan don yanzu har ƙanwar tashi haushinta ya ke ji, bai dawo gidan ba sai yamma can.

    Saif bai samu ƙanwarsa a gida ba ta tafi islamiyya hakan ya sa yana gama yin cefanen da zaiyi ya koma gidan Dr. nass, da Sallama ya shiga parlour ya tarar bata ciki wayarta ta kira akan ya dawo ba'a ɗauki lolaci ba sai gata ta fito fuskar nan duk ta kumbura idonta sunyi luhu luhu, kallon mamaki Saif ya bita da shi a hargitse ya miƙe tare da ambatar "Subhanallah Aunty bakida lafiya ne." Kwanciya kai tsaye tayi akan doguwar kujerar parlour tana rufe ƙafarta da hijab ɗin jikinta sannan ta ce

"Lafiyata  ƙalau Saif kawai dai yanayi na ne ya canja ina ƙanwar ta ka take?" Zama ya yi kafin ya ce "Sanda naje gidan ta tafi islamiyya me zan ɗaura miki?." Murmushin takaici ta yi "Haba Saif yanzu Fisabilillah kana namiji ina mace sai kai girki? Duk ayyukan zan iya kawai dama ina tsoron idan na fita aiki na dawo ga kuma aikin gida amma karka damu na kira a nemomun me aiki, sannan for the meantime zan mana girki." Yana murmushi ya ce "Noo Anty i will takecare of you kamar yanda na yiwa me gidan alƙawari, ke da kike zuwa aiki kuma ga damuwan kaɗaici sannan kiyi girki kafin me aikin ta zo zan dafa na yau anjima zan ɗakko ƙanwata ta tayaki kwana anan." Zaune ta tashi sannan ta ce "A bazan iya kwana ni kaɗai banajin motsin kowa ba dama idan haka ya faru sai dai in kwana asibiti ai ko kuma gidan ƙawata Ruƙayya so ka kawota Please."

"Mezan ɗaura yanzu." Gyaran zamanta ta yi "Anything local dish." Da ke dama kitchen ɗin ya saba  shiga kai tsaye ya wuce ya jere duk abinda ya dace a wurin dayaga ya mai saboda iyakacinsa dama kai plate sannan ya kalli Gas ɗin ba irinsa bsne a challet ɗinsa sam, nashi camp gas ne, duddubawa ya yi da ƙyar ya gane wanne ne na wanne ya daura ruwa shap shap ya yi tuwon semo yana hada kayan miya bayan ya ɗaure tafashen nama da ganda da offals, yana aikin yana tuna rayuwar da yayi a wani gidan abinci as helper har ya dawo cook ɗin gaske school ne ya rabashi da wurin ba don ya so ba. Veg soup mai yawa yayi tasha nama, kifi,ganda da offals, wani container me murfi ya saka kusan half of miyan aciki sannan ya juye sauran a wamers tuwon ma ya saka wani a cikin fridge wurin da baya ƙanƙara sannan ya fito ya jere sauran a dining. Komawa ya yi ya ɗaura tafasar wani naman ya dawo ya kawo plate's da komai bata falon hakan ya sa ya ɗan zauna kusan 40mns kafin ya kashe naman ya ɗaura stew ya rage wuta sosai ya wuce zuwa challet ɗinsa wanka ya yi ya sauya kayan jikinsa zuwa wando da riga mara nauyi ya dawo, har lokacin bata fito ba kai tsaye wucewa ya yi kitchen ya sakawa stew few spices dake kichen sannan ya zauna a dining ya kirata a waya ba jimawa ta fito duk ta gama ramewa kamar wacce ta shekara tana ciwo wannan karon ma da hijabi take as alwasy kowane lokaci da hijab zai ganta indai yana wuri akwai kamun kai sosai a al'amarinta. Nan take ya zuba mats tuwon shima ya ɗeba ya kawo mata ruwa kawai ya zauna suka fara cin abincin ta yi shiru kuma sai wasa take da abin cin yau kawai ta yi wani iri matar she is so lovely ya kalleta sosai ya ce "Anty don Allah ki yi haƙuri ki rage wannan damuwar, kenfa likita ce kinsan condition ɗinki ba irin wanda ke buƙatar bawa zuciya wahala bane ba, abincin ma wasa kike dashi don Allah ki daure kici." Yanzu kam kasa riƙe hawayan idon ta ta yi, duk sanda ta tuna yanda Yallaɓai baya iya taɓuka komai a shinfiɗa jikinta sanyi yake sosai saboda ta ƙwallafa rai da samun haihuwa ada tana ganin cewar idan zan iya koda 1mns acikinta haihuwa rabone wata ran zata damu idan da rabo amma the way abubuwan ke tafiya yanzu da zaran ya raɓeta sai ya kawo baya iya shiga jikinta ya ƙara ninka mata damuwar rashinsa ainun! Kenan batada rabon ganin ɗanta a duniya daga kenan zuri'arsu sunanta ya mutu murus! Batada wanda zai tunata yay mata addu'a, kuka sosai ta fashe dashi ta zari tissue da ke wurin ta duƙar da kanta ta fashe da kuka tsayawa Saif ya yi yana kallonta jikinsa duk ya yi sanyi, daga wannan kukan sai tari nan da nan ta sarƙe dadai yaga abin ba mai yiyuwa bane tashi ya yi da sauri ya tafi wurinta ya riƙe ta ya ɗebo ruwa a glass cup ya Kai bakinta kasa sha ta yi saboda tari da kyar ta kurba kadan, Saif ba ƙaramin shiga tashin hankali ya yi ba , da ƙyar tarin ya lafa mata idon nan ya yi ja sosai shi ya taimaka mata suka shiga ɗakinta ta kwanta yana ganin yanda jikinta ke wani irin rawa, har zai fita ya juya ta riƙo hannunsa ya juyo ya fuskanceta da kyau a hankali ta ce
"Ka kiramun Dr. Rash kaji Saif banida lafiya." Cikin ruɗewa ya soma neman wayarta ganin be gantaba kuma tana neman kasa magana ya ce "Anty don Allah ki bari muje asibitinku." Shiru ta yi tana ƙara takurewa wuri ɗaya tsabar sanyin da take ji, ganin haka kawia ya fice daga ɗakin da gudun fanfalaqi ya tashi motar ya nufi asibiti. Neman izinin ganin Dr..Rash ya yi aka tabbatar mai ta wuce gida, tunda ya taɓa karɓowa Dr. Nas saƙo a wurinta a gida kawai yabi gidan nata, Ya ɗan ɓata kusan 5mns kafin a bashi iznin shiga, kamar ranar a kwance ta tarar da ita parlour kanta akan cinyar Dr. Malik suna kallo. Sadda kanshi ya yi kasa sannan a cikin girmamawa ya ce "Dana Dr. Nasaree ce ba lafiya nayi nayi muje asibiti taki zuwa tace in kiraki naje asibitin bakya nan shine nazo gida." Da hanzari ta tashi zaune tana ƙoƙarin gyara hular kanta dake a cirew dama, "Oh Gosh meke damunta." Shiru ya yi don ba xai ce gashi ba ta kalli Maleek "Honey zance gidan Rash please kasan yanayin ciwonta ai." Gyaɗa mata kai ya yi kafin yace "Kije tare da Meenal to." Meenal da sai a lokacin ta ɗago kanga ta zubawa Daddy ido ya ce "Baby tashi ku tafi ki raka momy dama kince zaman ya isheki." Wandone a jikinta fa top sai hular kanta takalminta kawai ta daka ta zari wayar ta, Mom kuwa First aid box kawai ta ɗauka ta saka mayafi adamn doguwar rigar jikinta Saif ya ɗauke su suka wuce, Mom kaɗai ce ta shiga ɗakin Dr. Nass Saif da Meenal zama a parlour suka yi. Kusa da shi Meenal ta zauna tana mai murmushi kafin ta ce

"Whats your name bro?" Kallonta ya yi acikin style ya ɗan matsa daga kusa da ita lafin ya ce "Saif Saifullah." Tana murmushj ta ce "Your name is so sweeet, My name is Amina, Meenal, Mimi." Kallonta ya yi yana murmushi "All these names for one person." Dariya me sauti ta yi "Yea Dad call me Mimi, mom call me Meenal and My big bro call me Meenal or Mimi its only that Granny that use to call me Amina or Bakamore sometimes she even call me Ƙatuwa ba hankali, but don't mind her ta cika masifa." Murmushi kawai ya sakin mata kafin ya ce "Ahh tanaji da ke ne ai." Hannu takai ta shafa beard ɗinsa a hankali ta ce

MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)Where stories live. Discover now