*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
05.
Tun da ta gaisa da granny da yayansu Bashir ta wuce ɗakin da suke sauka ita da su Sawwa da Intisan bata ƙara fitowa ba har dare. Sai da granny ta aika kiranta sannan ta fito ta gaisheta don zuwa lokacin ta rage mata rashin kunya sosai. Tana duban ta tace "Intee na kitchen tana soya naman kaji kije ki taya ta har zoɓo ku haɗa anyi late na dinner sosai tunda gashi har anyi isha." Da ladabi ta ce "To Granny." Miƙewa ta yi ta juya zuwa kitchen Yaya Bashir yace"Shin wane ajin wannan girman turan take?" Zuhair na dariya ya ce"Tana js 2 muka shiga 100level ai yanzu ba gashi mun shiga 300level ba ita kuma ta gama junior sec school, amma kaga bai wuce mana 2weeks da fara zuwa 300level ɗinnan ba na fahimci wahala xamusha gaskiya." Dariya Bashir ya yi kafin ya ce "Haka ne muma a wurinmu amma yarinyar ku saka mata ido a yanayin dresssing sabosa girman jikinta zaka ɗauka ta kai 18yrs ɗinnan kalli yanzu kowa da suturan kirki ta kama jiji ta ɗaɗɗame kamar wata chidera." Murmushin takaici Zuhair ya yi kafin ya ce "Girman jikin ne sikar komai da an mata ɗinki wata uku ya matse ta shiyasa." Kallonsa kawai Bashir ya yi cox waye bai san duniyancin mahaifiyarsu ya tabbatar cewar da saka hannunta yarinyar ta sangarce haka gatanan kamar ba musulma ba. Miƙewa ya yi ya nufi kitchen ɗin Intee na ganin yanayin fuskarsa ta ja baya tana kallonsa a taƙaice ya ce "Ke intee jeki huta barta ga ƙarasa aikin." A tsorace Meenal ta kallesa cikesa tsoro nan take idon ta ya kawo ruwa ta ce
"Yaa Bash wallahi ban iya zoɓo drink ba don Allah ja rufamun asiri." Ta ƙarashe maganar muryarta yana rawa saboda sanin halinsa." Kallon Intee ya yi ya ce
"Jeki zauna kina nuna mata duk yanda zatayi nima bani kujera." Haka suka zauna ana nuna mata yanda zatayi har ta kammala komai." Jikinta banda rawa ba abin da ya je suna kammalawa suka kai komai dining sannan da sauri ta wuce ɗakinsu har kowa ya hallara dining ita bata fito ba Granny kuwa ta hana kowa zuwa kiranta har aka kammala ta wuce ɗakinta bayan ta musu sallama. Bashir ne ya tashi ya nufi ɗakin da take ciki ya tarar tana kwance sanye da kayan bacci riga da wando dogo rigar ma na da tsayi har kusan rabin bombom ɗinta, tana jin an buɗe ɗakin an rufe ta juyo ganin Yaa Bash da sauri ta mike tsaye gashin kanta a baje ya sha relaxer, ƙare mata kallo ya yi daga sama har ƙasa sannan ya ce
"Ubanwa kika raina da kika kasa fita lunch?" Muryarta yana rawa ta ce "Yaa Bash kayi hakuri ni ban raina kowa ba kawai lafiyace bandan ita na ƙoshi?" A fusace ya ce "Wuce muje kici abinci." Da sauri ta fara tafiya ya ce "Kee" waigowa ta yi kamar zata fashe sa kuka take ji ta ce "Na'am." A tsawace ya ce "Ba za ki rufe gashinki ba haka zaki fita, da sauri ta dawo ta ɗauki net cap ɗinta ta saka sannan ta wuce a dining ya zauna sai da ta gama cin abinci sannan ya ce "Me ya sa kika koma ɗakin da kike yanzu." Cikin saburcewa ta ce
"Yaa Bash kawai dai wallahi ba komai bane dalili." Shiru ya yi yana kallonta kafin a hankali ya ce
"Meenal kinsan cewa yanzu you are no more a kid ko?" Da sauri ta gyaɗa masa kai ya ci gaba
"Then why are you behaving like one?." Ya ƙarashe maganar yana kafe ta da ido rashin fahimtar inda ya dosa ya sanya ta langwaɓar masa da kai shi kuwa yaci gaba
"Ke musulma ce Amina meyasa kike ɗabi'unki kamar ba musulma ba kuma hausa Fulani? Ɗazu ba mayafi kikazo gidannan shekarunki sha huɗu fa gaki da girman jiki kuma ko ba'a faɗa ba na tabbatar kin girma ina nufin kin balaga, Please little sister ki gyara kinji gobe zamu tafi zan saya miki wasu abubuwan amma bazamu shiryaba idan bakya son suturta jikinki da kyau." A hankali ta ce
"In shaa Allah Yaa Bashir ba zan ƙara fita ba mayafi ba." Hannunta ya riƙo kafin a hankali ya ce"Yauwa ko ke fa." Yana kallonta nan da nan taji wani irin kasala ya saukar mata, wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki mara misaltuwa da sauri ta ɗauke idon ta a cikin nasa ta yi shiru tana sauraren yanda yake murza tafin hannunta tana jin wani tsoro haɗe da wani abu da bazata iya cewa meye shi ba da sauri ta janye hannunta ya bita da kallo sai kuma shima ya ga rashin dacewat hakan da ya yi, miƙewa ya yi sannan ya ce "Je ki kwanta pray before you sleep." A hankali ta a ce "To." Ta juya ya bita da kallo ganin sauyawar yanayinta har ta shige ɗakin, sauke ajiyar zuciya ya yi shima ya juya, a ɓangaren Meenal kuwa da ƙyar wuraren 1 bacci ya ɗauketa.

YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
Ficción GeneralRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????