*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
19.
Saif da Zuhair waje sukayi kai tsaye mota Zuhair ya jingina da ya fashe da kuka kamar ranshi zai fita, jikinsa har rawa ya ke yanda yake kuka saida securities suka taso suka yo kanshi jin Lfy nan dai kawai Saif ya ce "Karku damu ƙanwarshi ke batada lafiya sosai shiyasan nan suka mata fatan alkhairi suka juya, cikin rarrashi Saif na ƙoƙarin ɗagashi ya ce "Be strong please and stop crying like a baby, shekarunka 20 fa you are man enough to handle situation irin haka kaji." Rage kukan yayi amma ya kaisa dainawa mota suka shiga amma haka duk sanyin AC Zuhair gumi ya ke kamar wanda ya haɗiyi kunama... Mom ta yi iyakar yinka akan taga ta tsayar da uban jinin amma ta kasa tana ganin yanda Meenal ke lullumshe ido kamar zata yi passing out, a hankali ta soma ja baya tana kallon jinin jikinta na wani irin rawa kamar mazari, a hankali Meenal ke cewa "Allah na tuba, Astagfirullah wa atubu ilaik, yaa Allah me nakeji a jikina haka kamar ba nawa, Daddy, Momy, yaya Zuhair yaya Saif kuzo ku tofamun addu'a duhu nike gani kamar na makance fa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya Zuhair ka gani ko, kaga abin da son zuciya ya ja mana ko? Yaya Saif ya ce zai rufamun asiri ya ce shine ya yi cikin ba kai bane ya ce idan su Dad sukaji kamun ciki ina ƙanwarka zasu iya bindiga su mutu in rasa su ni kuwa bana so su mutu, remember we promise to take this secret to our graves karka saɓa alƙawari idan Momyna taji zata yi fushi dani, bana so tasani, so ɗaya tak! Kuskure ɗaya tak yaya Zuhair ya rosa komai." Ta fashe da kuka tana laluben wurin tsabar duhun da take gani batamasan me take cewa ba, Wani irin shock momy taji don sai yanzu take ƙara auna maganganun Mimi na ɗazu, sai yanzu ta tuna yanda ɓar Zuhair ya ɓace sanda take gayamai Mimi nada ciki, wani kalan murɗawa cikinta ya yi ta fara shararo gumi, batare da ta damu da jinin dake hannunta ba ta shafe zufar goshinta tare da dawowa ta gyara zaman tabarau na idon ta... Gyaran murya ta yi Mimi da batamasan me take faɗa ba ta ce "Yauwa Momy haskamun ƙasana meke zuba ne haka kamar fanfo ji nike kamar 'yan hanjin cikina na zazzagowa zasu fito ga wani dubu don Allah ki kumna fitila." Da sauri momy ta kwasheta sai wurin Dad...........
*Dawowa cikin labari.*
_Sake karanta page 1 don tuna inda muma tsaya_
Oga Milton ya kalli Dr. Fati jikinsa a sanyaye ya ce "Call Dr. Nas immediately her pulse is not going well, it keep giving red light jinin kwata kwata tana zuƙewa ne kamar bama sakawa its showing 10% kalli screan ɗin and her body is sooo cold." Dr. Fati fa kalli nurses dake wurin a nutse ta ce "Bring stretcher and take Zuhair to emergency immediately it's panic attack." Sannan ta shiga neman layin Dr. Nass da ko shiga kiran beyi ba ta hango tahowarta kamar zata tashi sama, kai tsaye wurinta ta shiga ta soma neman yanda Stabilizing naga da ƙyar after 3 hours ta farfaɗo, Saif na bakin ƙofar ICU sai kallon wurin ya ke yana so ya shiga amma ba halin shiga har zuwa sanda Dad ya iso kallo daya zaka masa ka tabbatar cewar yana cikin tashin hankali, ƙonewar jinin Amina is a bad sighn, haka ya taka har wurin da Saif yake suka gaisa sannan kai tsaye Saif ya bishi ciki, kallo ga bisu da shi sai kuma kamar ana kiran sunanta tabi ceiling da kallo, kallon yanda heart beat nata da pulse ke sauka sosai Dad keyi jikinsa duk ya yi sanyi shi likita ne patient sun sha mutuwa a gabansa ko ba'a gaya masa ba ya san cewar chances of survival na Mimi is very low, yana cikin wannan tunanin injina suka fara ƙara ya juya yana kallon yanda take yi ficewa ya yi daga ɗakin ya barta da saif daya matsa yana kallonta ya riƙe hanunta dakenan sanyi ƙalau ya soma karanta mata La'ilah illah! Haka ya dinga mata har at her last breath ta Allah ya bata ikon amsawa lokaci guda kuma iginan suka tsaya cak!!! Tare da numfashin Meenal Saif ya fashe da kuka, acan zuciyar sa yana murnar cewar Meenal ta cika da kalmar shahada a bakinta wata ƙila Allah ya duba kyakyawra zuciyar data ƙare da shi ne, wata ƙila ubangiji ya duba yanda ta ke tsoron sake saɓa masa ne ta hanyar ƙin amincewa da zubar da cikin wata ƙila Allah karimun Raheem ya karɓi tubanta ganin cewar ta yi tuban gaskiya, kafi kai Saif ya yi a jikin gadon yana nanafa kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...... Jikinsa gaba ɗaya baya masa kamar nashi, wani kalan mutuwa jikinsa ya yi da zaka ɗauka shiɗinma lokacinsa ya yi, kasa koda motsawa ya yi bare ya yi yunƙurin fita sanarwa da wani wannan mummunan labarin me cikeda al'ajabi don kuwa mutuwar Mimi iznina ce ga mai hankali..
![](https://img.wattpad.com/cover/377851722-288-k995098.jpg)
YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
Fiksi UmumRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????