*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
28.
Har cikin gidan ya kai mata kayanta ya ajiye a parlour ya yi tafiyarsa part ɗinsu Babarshi tunda ya shigo take mita yayi tafiya da mace ya shafe kwanaki goma sha ɗaya me suke acan ɗin ta rasa wannan dalilin inda take shiga ba nan take fita ba da ƙyar dai ya nuna mata ai aikin Company ya samu ake koya masa sannan ta sassauta taji batun kuɗi.
Washe garin fanar Ayiya ya tura akan idan ta shirya zuwa office ta fito aikuwa sai ga tanan taci wanka ta centre mirror ya ƙare mata kallo kafin ya sakko ya buɗe mata gidan baya ta zauna sai da ya zauna shima sannan ya ce "Anty barka da safiya." A taƙaice ta ce "Saif." Irin ɗinnan wani malalacin murmushi ya yi yaja suka tafi bayan sun isa batare da ya sakko ba ya ce "Karfe nawa zanzo?" A daƙile ta ce "4." Sakkowa ya yi ya buɗe mata suka kalli juna idon nan nata ya yi luhu luhu yayi ja ko dama ba'a gaya masa ba yasan kukanta tasha daren jiya ɗauke kansa ya yi yana mata Allah ya tsare daga haka ya wuce ya ajiye motar agida ya shiga garage ya ci gaba da sana'arsa bayan ya idar ya taho gida wuraren 3 wanka ya yi ya sanja kaya mahaifiyarsa nata kallonsa ganin kayan aikin daya saka amma bata ce masa komai ba yana fita ya ɗakkota ya gaisheta yanzuma da ƙyar ta amsa ya ce "Akwai abin da zan saya miki ne." Sharesa ta yi shima ya share ta ya tafi ya ajiyeta ya ƙara kiran abokinsa ya karɓi napep ya shiga gari be daso gidanba sai goma a lokacin tana jikin window tana jiran shigowarsa kamar zata kuwata, ganin ya wuce sashinsu ba ƙaramin takaici ya bata ba ta koma ɗaki kawai haka aka shafe zama da sati uku suna zaman nan, ranar kawai yana zaune a gate shi da me gadi sai ga Alhaji Mukhtar ya miƙe suka gaisa sosai ya ce "MD ance bakada lafiya ya jikin?" Yace da sauƙi a takaice shikuma yaci gaba
"Shiyasa tace inzo har gida in kawo maka takardunnan ka duba kayi signing." Murmushi kawai ya yi suka wuce har parlour suka zauna Ayiya ta kirata anan suka gaisa sai kallon Saif take yau kwananta biyu bata fita office ba hakanan tsakaninta da shi sai dai ta hangoshi ga window babban damuwarta ma kayan kanikawan da yake yawo dashi da kuma kaiwa 10 kafin ya dawo satar kallonta shima ya yi duk ta gama ramewa kome yake damunta oho, nan Mukhtar ya fara bayaninsa yana baje takardu, gaba ɗaya sai a sannan Hajiya Hauwa tasan ta tafka babban kuskuren katoɓarar da ta rafka sai a sannan ta fahimci cewar babu shakka Saif ba abin ranawa bane, kusan 6hours sallah kaɗai ke tada su bayan dogon zammannan yana kallon Alhaji Mukhtar ya ce "The last time i check kafin in baro Abuja duk abin da ke akwai na gama fitar da shi ina kuma sane da duk wani shige da fice na kuɗi a wurinnan 105 million is a huge amount bazai yiyu daga sama kawai anata lissafi babu su ba, kai da kuma manager na tresury ba wani kuɗin da zai shiga ko ya fita babu saka hannunku tayaya wannan kuɗin kawai zeyi ɓatan dabo." Daburcewa Alhaji Mukhtar ya yi ya fara rantse rantse calmly Saif ya ce "Deputy." Alhaji Mukhtar ya ɗago ya kallesa ya ce "Na baku daga yau zuwa friday kuɗinnan ya koma a cc na company." Sauke hular kansa ya yi ya soma amfani da hankly wurin ɗauke zufar goshinsa yana jinjina kansa alamar to, ya ƙara dubansa ya ce "Sababbin enginan da aka kawo last month da suke nan babu insurance aka fara amfani da su wani abu ya samesu insurance company basu biyaba saboda baku musu insurance ba wallahi tallahi kune zaku biya damages." Da sauri ya kallesa sai kuma ya hau ban haƙuri cewar za'ayi nan dai Saif ya basu wuri yana ɗagawa ƙofa kawai yaja ya tuna wayarsa sai ya rufe ya juyo ya baro corridor zai buɗe ƙofar parlour kawainya tsinkayi muryar Alhaji Mukhtar "Hajiya Hauwa kina zaune ƙaninki yana turakata kinja baki kinyi shiru yanata zuba iko sai kace wani sarki hajiya kuɗinnan ina zan nemo shi to nidai kowa yazna bazanci kuɗin nan ba sai dai ko manager amma ba ruwana, ina raga masa ne kawai sabida ina sonki banda haka sai dai in bar muki company ku ko yanzu zan iya naman aiki a wani wurin ai." Bata yi magana ba Saif ya shiga palon bece musu komai ya ba kai tsaye wayarsa ya ɗauka sai kuma kawai ya nufi cikin gidan ya wuce parlour ɗinta ya zauna har saida ta raka Alhaji Mukhtar ta dawo parlour tana shigowa ya miƙe tsaye yana mata wani kallo ɗauke kanta tayi ta tsaya itama calmly ya ce

YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
Ficción GeneralRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????