*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
Paid book
To subscribe pay in to 8103943903
Opay Safiyya Galadanchi.22.
Da wani irin gudu Zuhair ya isa asibitin sa hankali a tashe, Allah ne kaɗai ya kaishi lafiya because he was over speeding, da sassarfa ya isa ward ɗin inda yana shiga ɗakin ya tsaya cak yana kallon Oxygen da aka saka mata, jikinsa ba ƙaramin sanyi ba a hankali ya ce "Dr. Umar garin yaya aka barta ta riƙa ggwara kanta a bango?" Cikin damuwa Dr. Ummar ya ce "Wallahi Cmak yanda aka kiraka haka aka kirani, ban san komai a akan wannan." Wani bushashen yawu ya haɗiya masu tsananin ɗaci kafin ya ce "Ok yanzu naga kamar she is conscious ya aka yi."
"Stabilizing nata mukayi and koda na kira muna checking ko akwai wani internal injury kuma ba ko ɗaya kawai mumfashi ke bata wahala kamar dai she is athsmatic." Da wani irin relief ya zauna akan plastic chair da ke wurin ya na kallonta yama kasa cewa komai kusan 40mns yana zaune har Dr. Umar ya fita ya barshi agogon hannunsa ya kalla yaja gajeran tsaki don kwata kwata yau ba asibitin nan ya shirya kwana ba amma ya zeyi? Bazai iya zuwa ko gidansa da ke nan ba ya bar Mimi, ajiyan zuciya ya sauke ya miƙe yana ƙara duba oxygen da ƙarin ruwan da ke hannunta, kusa da kanta ya tafi a hankali ya shiga shafa hargitsatsiyar sumar kanta dake nan kamar ta india sai sheƙi ta ke gata baƙa wulik, cikin raunin murya ya ce "Get well soon chuby, i will pray ki samu sauƙi i will also pray duk wanda ha lalata miki rayuwa idan da gangan ya yi Allah ya bi miki haƙƙinki, Allah ya baki lafiya and tell me where your parents are in kaiku wurinsu kinji Papi's chubby angel." Ya ƙarashe maganar da wani murmushi da ba za ka iya fassarawa ba amma yafi kama da na ciwo irin mai zafin nan da ƙuna, kuma yana yi kamar zata buɗe idon ta ta bashi amsa ta ce yes papi." Wani zazzafan hawaye da ya zubo mai ya share sannan ya goge fuskarsa da hanky ya juya zuwa office ɗin sa anan ya yi wanka ya sha coffee sannan ya sauya kayan jikinsa zuwa Shirt mai round open neck mai ɗan faɗi fara ƙal da wando iya gwiwarsa fari ƙal mai faɗi a ƙasa, madubin idonsa as always yana manne da idon nasa, ya mayar da agogon Exsy a hannunsa ya zari wayarsa sannan ya fito yana ƙarewa garin kallo da yamma ta yi ga hadari masallaci ya wuce acan ya yi sallan magrib ya zauna sai da aka yi isha sannan ya koma ɗakin tararwa ya yi har lokacin bacci take har an sake sauya drip da ake ƙara mata wancen ya ƙare wata nurse ya samu a ɗakin ta gayar da shi cike da ladabi ya amsa kamar baya so sannan calmly ya ce "Any progress." Juyowa ta yi cikin nutsuwa ta kalleshi sannan ta ce "Sir i learn that she is pregnant but i notice she is bleeding now sai dai ba da yawa ba dama ina jiran Dr. Umar ne ko Dr. Ashraf su shigo." Sai a sannan ya kalli ƙasan ta lumshe ido ya yi sannan ya buɗe su fess akan nurse ɗin, ganin yanda lokaci guda launin idon sa ya canja ya bawa nurse ɗin wani kalan goosebumps ta saukar da kanta a ƙasa cikeda tsoro kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce "Nurse Elham are ok?" Da sauri kamar bata fahimcesa ba ta ce "Yes sir." Wani smirk ya saki kafin ya ce "Are you sure?" Gyaɗa masa kai ta yi har lokacin ta ƙi kallonsa kafin ta ce "Sure sir." Miƙewa tsaye ya yi daga zaunen da ya ke "Are you for real?" Sai yanzu ta ɗago kai ta kalleshi cikin ihu ya ce "How dare You nurse Elhm? A pregnant woman i mean a pregnant child is bleeding and instead of you to hurry and get any available Dr. You are here calmly waiting for a Dr. To come and your proudly saying to me that sure you are ok?" Muryarta har na rawa ta ce "Sir its just because naga baida yawa ne just a small bleed." Cikin tsawa ya ce "Is that why you decided to wait till it wosen?" Muryarta har na rawa ta ce "Sir Don Allah kamun rai i was wrong but i promise never to repeat it again." Yana mata wani matsiyacin kallo jijiyoyin kansa kamar zasu faso ƙoƙon kansa su fito ya ce "Pray bansa aka koreki a asibitin nan ba, not even that bansa a karɓe license ɗin ki ba coz for sure na tabbatar cewa ke baki cancanci zama nurse ba now get out grom my sight." Da sauri ta raɓashi ta wuce shi kuwa ya yi hanzarin zuwa dubata ganin ba abin da zai iya duk da bleeding ɗin kaɗan but is a threat ya sa ya zauna a karo na farko ya yi jarumtar kiran Baba indo ɗaga wayar ta yi ta kai a kunne tana zaune gana dirzar goro, shiru ta ji anyi bayan tace Hello so biyu a fusace ta ce "Ni nasna idan ba wagararrun ɗiyan Asiya ba ba wani wagarren da zai kirani ba zai yi magana to idan ma kune kanku kuka yiwa da uwarku don ni indo ba katina ake ƙonawa ba na uwarku ake ƙonawa." Calmly da wnanan muryar tashi mai faɗi ya ce"Baba Indo an wuni lafiya." Janye wayar ta yi daga kunnenta sannan ta mayar ta ce "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wane sabon wagararren basamuden ne kirana da tsohon daren yana shirin fasamun kunne da wannan uwar gangar muryar kamar a kunne na ake shirin busa ƙaho?." Zuhair gyaran murya ya yi ya ce "Baba Zuhair ne ina so ki bawa Momyna wayar?" Tsaki taja sannan ta ge "To ni meye haɗina da kai da wata Momy wai tukunna wacece kuma momy kaga don Allah karka isheni ni gorona nike ci a nutse." A hankali ya ce "Baba don Allah ki yi haƙuri ki kai mata wayar." Tashi ta yi tana cewa "Ba dole in kai mata wayar ba Zuhairu ya zamemun dole don da tsufana bazan taɓa bari ka fasan dodon kunne ba da wannan garahunin gagarumar muryar taka sai kace ta ƙatti dubu aka haɗa maka." Shi dai shiru ya yi har ita wurin Momy kyaɓe baki ta yi sannan ta ce "Ruƙayya ga waya basamuden ɗanki na kiranki." Bata ko ɗago ba ita kuwa ta latsa wurin handsfree ta ajiye mata wayar a cinya don ko Daddy ya kira duk da bata cewa komai haka ake ajiye mata wayar ya yi ta magana har sai don kanshi ya katse, cikin murya mai taushi kamar zai mata kuka "Ya ce Momy na nasan bazaki iya magana na kullum fatana Allah ya baki lafiya ki buɗe bakinki ki ce Zuhair na yafe maka Allah ya maka albarka, Momy kamar kullum ina cikin damuwa kuma ko da ba za ki ce komai ba ba zan fasa gaya miki ba, Momy ina da wata patient gatanan kamar ta haukace ma, Momy o found that she is pregnan 3weeks pregnant someone raped her Momy she is a small a girl bazata wuce 14yrs ba Momyna, she is now bleeding momy bana so cikin ta ya zube i don't want her to undergo MVA na rasa ya zanyi i am even scared to call any gynaecologist kar su ce Babyn ya mutu a cikinta Momy i have strong feeling about her na rasa na meye Please momyna pray for her pray for my Mimi kinji." To his greatest shock and suprise muryan da bai taɓa jiba ya ji yana ratsa dodon kunnensa cikin karkarwa kuma bata fita sosai tsabar rashin magana a rarrabe ta ce "Mmmmmy Mmmmimi iissi ble ble bleedding Zzuzzuuhair?" Da sauri ya zabura ya miƙe zaune jikinsa na wani irin rawa ya ce "Yes Mom Your Mimi is sick she is pregnant and now is she is bleeding." Itama riƙe wayar ta yi tana zabura kamar zaga firge kanta ta ce "Tttttke me to her you here now, i have to save my little Mimi if anything should happen to her I will die." Da wani mahaukacin gudu ya fito daga Ɗakin wayar har lokacin yana kunnensa yana nishi sauri da sauri ya ce "Nothing will happen to her i am just a minute away from you don't worry mom i will come and take you to her right away." Ya katse wayar ita kuma ta fito tana zare zare a parlour tana kallon Baba Indo ta ce "My Mimi is bleeding i need to go save her, nothing will happen to her." Baba indo da ta rikice ta miƙe tsoro ya kamata don Momy bata magana a firgice ta ce "Wa innahu min sulaimanu, na shiga uku ni Indo haukan Ruƙayya ya motsa" cikinta momy ta yi ta yi azamr cafkota ta shaƙe rigarta a bango tana wani kalan zare ido ta ce "Where is her? Where is My Mimi ehhen ?" Baba indo fitsari ta sake acikin jikinta tsabar tsoro saboda ba kowa a gidan sai su biyu da me gadi da ke waje "Ki yi haƙuri Ruƙayya ki ɗauki tawakkali ki barwa Allah Amina ai ta zama ƙwarangwal a ƙabari tuni." Wani shaƙeta Momy ta ƙarayi nan take ta fara kakari Allah ne ya kaɗo Hajiyar da me musu aiki da ƙyar suka ƙwaci Baba Indo suka rirriƙe Ruƙayya nan fa Baba ta shiga tari da ƙyar ta samu ya lafa mata ido wiƙi wiƙi ta fashe da kuka ta ce "Na shiga ukuna ni Indo, yanzu Ruƙayya a kaf garinnan da haukanki ya dawo na duka ki rasa wa zaki daka sai ni da na yi jinyarki shekaru goma sha shida?? To wallahi kinyi asara kuma na barki da Allah muguwa." Tana magana tana tari ta ce "Sai dai uwarki ta yi jinyarki yanzukam Allahu Akbar da ba dan aminiyata ta iso ba sai dai kawai aji Indo na barzahu sai dai azo ana karɓar gaisuwa ana cewa Mahaukaciyar matar Maliki ta kashe uwar maliki dom wallahi ko a lahira ni zaki gani shegiya da jar fatar kamar jimar zabiya." Babu dai wanda ya kula ya Baba indo acikinsu nan sukka shareta ta yi ta masifar ta har ta gaji ta yi shiru tana mayar da numfarfashin wahala, suna ta zaune rirriƙe da ita Zuhair ya shigo kamar mahaukaci shima Baba indo taja baya a gajiye don fa tasha damƙa taji jiki, uwar na ganinsa ta fara cizge jikinta Hajiyar Sama Calmly ta ce "Mahaifiyar ka ta fara magana gashi har ta fara dukan mutane Zuhair yanzu da ba dan munzo ba da sai dai a ɗauki gawar indo." Baba indo ta fashe da kuka "Allahu Akbar ni Aishan me walda." Hajiya ta ci gaba "Ka gayawa Malik ya zo ya ɗauki matarsa wallahi wallahi ba zan iya ba." Shi dai takawa kawai ya yi ya riƙo hannunta ta kuwa daina kokawar kawai ta biyo shi, dama she is always wearing hijab hakan ya sa kofa kawia ya yi da ita ba wanda ya ce mai ƙala banda indo da ke jajen da yanzu ta mutu tana kuka kamar ta goye. A mota ya sakata shima ya shiga ya balbala da gudun besfa ya doshi asibitinsu. Shi ya buɗe musu Kofar suka shiga, nurses biyu da Dr. Bashir suka tarar a ɗakin sun ruhu kan yarinyar data farka yanzu amma kamar abin ya ƙaru mata wani mahaukacin bleeding take mai ban mamaki, Mom tana kallonta ɗaura hannunta ta yi aka ta runtse ido, gaba ɗaya ilahirin jikinta yana ƙyarma nan da nan brain ɗinta ta harba mata abubuwan da suka faru 16yrs back cikin wata irin ruɗewa ta ƙwallah mahaikaciyar ƙara a wurin ta zube a sume....
***************
Zaune take a gaban bokan suna kallon juna kanshi a tsaye ya ce "Hajiya ba abin da zan iya na miki face hai saida kyallen dake ɗauke da jinin hailanta na ranar farko." Sauke numfashi matar da aka kira da Hajiya ta yi cikeda jin zafi ta ce "Boka duk abin da ya kamata inyi na yi amma abin ya ci tura, na yi nasarar dai dana ɓatar da ɗiyar shegen da suka haifa a tare, amma na rasa yanda in raba auren ɗana da tsohuwar guzumarcan duk inda na ɓullo nan sai ta toshe can boka koma menene tunda har yaron nan ya samu arziki da bana ji har abada zai tsiyace don Allah ka kashe mun matar wallahi duk ta saka yarona ya zama tsoho kamar ta dududu nawa yaron nan ya ke amma biyayya ya ke mata kamar ita ta haifeshi ni nagaji." Wata mahaukaciyar dariya bokan ya yi kafin yana mata wnai kallo ya ce "Hajiya wannan matar bata wasa da ibada so dubu idan zan tura ma'aikata sai ta ƙona su sai dai wani abun daban amma banda kasheta, sai idan ɗanki zan yiwa aiki shi ya tsane ya saketa amma fa idan ya saketa zai haukace bayan wata shida kuma har abada shida lafiya." Wata iriyar zufa ce ta keto mata kafin a hankali ta ce "A a boka kar ka haukatar mun da ɗana, barsu a taren ni nasan abin yi, yanzu so nike ka rufemun bakinsa kwata kwata ya daina maganar yarinyar yaji ma kamar baida wata yarinya Lulu a duniyan nan." Boka na wasu surutai da bata ganewa ya yi haukanshi yana kallonta ya ce "A mana sadaka da baƙin bunsuru idan an tashi sadakar a tabbatar anyi da asubahi sakaliya a binne bunsurun da ransa sannan kar a bari wani mahaluki yaga sanda ake binnewa kuma kada bunsurun ya yi kuka sam, sannan kuma idan an ɗauramu akan su munyi nasara waccen tana bacci a lokacin itama zata manta ta taɓa haihuwar wata ɗiya Lulu a duniya kai ba ita bama har ƙannenta da duk wani wanda ya san yarinyar." Godiya ta shiga yi sannan ta ajiye masa kuɗi masu yawa ta juya ta fita murmushi a fuskarta raɗam!!!!!Kallon matarsa ya ke yanda yau ta tashi sakayau ba tunanin komai a ranta ba ita ba hatta Raudah da Mu'az ba wanda ya tashi maganar Lulu shi kanshi yau deep down yana jin kamar tana ranshi amma ya kasa magana game da ita kwata kwata... Kallon Dr. Ya yi da ke nan fuskarta cike da annuri tana sanye da wani rantstsen lace da ya karɓeta sosai fuskarta fayau na wani makeup sai kwalli tana tafiya a cikin ƙasaita sanye a saman rigar lace ɗin ta labcoat ce fara ƙal ajikin aljihun an rubuta Dr. NS, ta ɗaura agogo mai tsada a wutsiyar hannun ta, ta murza ɗauri kwantacce da wani hijabi ƙarami a kanta mai taken a yaƙi shari'a, miƙewa tsaye ya yi saboda ba kowa a parlour sai su kaɗai ɗan side hug ya bata kafin ya ce "Anty." Murmushi ta yi a karo na barkatai kafin ta ce "Yaron Anty." Dariya suka yi a tare kafin ya ce "Anty zan biki a asibitin muyi aiki a tare." Tana caressing hannunsa dake cikin nata cike da so ta ce "Banda rigima Little ɗin Anty ba zan daɗe ba kaji." Murmushinsa me kyau kawai ya rungumeta, har mota ya rakata driver yaja suka tafi sannan ya koma ciki yau kawai jinsa ya ke sakayau kamar baida wata damuwa.
Mom Nu'aiym
Free pages
07084161619

YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
General FictionRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????