*MAI SAƘO*
*(GARIN NEMAN GIRA..)**BILKISU GALADANCHI*
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*
Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8
Payment details
8103943903
Opay
Ssfiyya Galadanchi
N500
Vip 1k.31.
Tunda suka rabu bai ƙara nemanta ba itama kuma haka har aka kwana biyu, ranar monday kenan ya zamana saura kwana huɗu ɗaurin aurensu, tana shirin fita aiki ya shigo parlon tana sanye da abaya me ta ciki da buɗaɗɗiya a waje ta yafa mayafin abayar stethoscope da labcoat ɗinta a hannunta ɗaya ɗayan riƙe da wayarta da kuma hand bag fuskarnan fayau ba komai idon tun daga cikin madubi zaka hango sunyi luhu luhu sun kumbura alamun dai tasha kuka farar fatar fuskar ta yi ja sosai, acikin ƙasa da 30seconds ya gama haddace ta a daƙile ta ce masa "Ina kwana?" Wani smirk ya yi kafin ya ce "Dr. An tashi lafiya." Kallonsa kawia take bata ƙara ce masa komai ba, yana dubanta still ya ce
"Masu pent zasu zo ina da ina kike so za'a yiwa paint ɗin?" Tana janye idon ta a nasa ta ce "Ba kace ba zai anyi ba." Tsatsareta da idon sa ya yi kafin ya sake cewa "Ina da inane za'a yiwa paint kuma wane kala kike so." A hankali ta ce
"Duk gidan kuma it should be nude a parlour saboda kalan furniture ɗin." Yana ƙare mata kallo ya ce "Ba kince zaki sake furniture ɗin ba ." Shiru ta yi ya ce "Do what Suit you Dr. Banida matsala kawai zanyi pent ne its better you stay suna hanya ki zaɓa yanda kike so amiki." Juyawa ta yi ta shiga ɗakinta ta ja hanky ta zauna kusan 5mns tana kukan da ta kasa dainawa kafin a hankali ta jingina jikin kujerar har kusan 30mns sannan ya kirata a waya ta fito nan suka nunna mata colours da design ta nuna inda take son ayi ko wanne they promise kayan gidan ba ruwansu da paint bazai shafesu tunda they are professional's sannan ta fito taga Driver baya nan shine ya ce mata "Ki hau mota muje in kaiki." Da sauri ta taka ta buɗe gaba ta zauna murmushi kawai yay ya shiga motar ya tasheta suka kama hanya kusan 5mns ba me magana a hankali ya ce
"Maganar furniture ni banida kuɗin siyen irin wanda kike so kin sani kuma yanzu ya dakiyi." Shiru ta ɗanyi tsoron take tace zata saya yace wani abu sai can dai tace
"Company da Yallaɓai ya maka magana ai nasa ne dama kawai zasu zo su ɗebe na nan su kawo new one's shikenan." Yana lanƙwasa staring yasha round about ya ce "Waye a wurin." A hankali ta ce "Ba kowa dama ba kai yayiwa magana ba manager ne kawia kuma tunda akayi rasuwar ni be taɓa cemun komai ba ma siyarda kayan da shigowar wasu." Yana mata wani duba ya ce "Ke kuma you are busy finding troubles sama da ƙasa baki tuntuɓesu ba ko?" Shiru tayi ya girgiza kansa kafin ya ce "Ni ina sane da duk abin da suke ai tunda tun tahowar tasa ya Kaini wurin akan in riƙa karɓar komai da suke yi a runuce ina sane dabadan ina zuwa gareji kwanan nan ba ai da duk ina Ganin acan nike wuni zan kira manager suzo su ɗebe wannan gobe da yamma sai muje tare ki duba wani and kitchen cabinet ma nace masu paint su cire miki shi a saka sabo daga company zasu zo su saka." Kallonsa ta yi yanzu sosai "Saif garage kuma wai fisabilillah meyasa kake haka ne don Allah." Bece mata komai ba har suka isa asibitin ta masa godiya ta sauka ta tattare kayanta ta juya iskar dake kaɗawa tana kwashe mata rigar sama sai ta cikin dake nan a matse dam take bayyana tsaki kawai yaja ya girgiza kansa yana rivers ya soma kiran number wayarta bata ɗaga ba har ya tsinke sai da ta nutsu a asibiti sannan ta kirashi back ya ɗaga sa sallamarsa
"Sorry i couldn't pick up the call saboda kaya yayi yawa a hannuna." Tace bayan amsa mai sallama "Dama cewa zanyi idan rigarki ta sama tanada maɓalli ki saka su kina tafiya waccen tana kwashewa jikinki duk a waje."
"Ok in shaa Allah." Bece komai ba ya katse kiran yana jan wani tsakin shegen kishin dake nan yana nanuƙarasa hala tun can dama don baya kula da ita ne yake ganin kamewarta ko kuma hala har yanzu tallan kanta take ta samu wani saboda shi tafi ƙarfinsa..... Dr. Fatee na kallonta ta ce "Dr. Ya aka yi ne?" Girgiza kanta kawai ta yi cikin takaici ta ce "Wallahi Dr. Lamarin nan na Saif mamaki yake bani, ni yanzu har wani shakkar sa nake ina ganinsa ƙirjina ke dokawa sosai saboda tsoronsa, wasu sababbin halayye yake bijirowa dasu masu ban al'ajabi could you believe saboda me ɗinki ya aunani abin da ya manta ne kawia be gayamun ba, wai na sakewa tela jiki yanzu kuma wai don jaraba wai rigar nan in saka maɓallai." Dr. Fatee ta kwashe da wata shegiyar dare tana tafawa ta ce "The Guy is damm hot ai ni sai daga baya nace ƙawata gwara ki aureshi ki cire takaicin rashin samun kulawa a baya sabon jini ne ƙaƙƙarfa dama da ƙuruciyarki a jiki ku mori juna, duk wannan sababin ai na kishine zallah." Taɓe baki Dr. Nas tayi tunawa da maganganunsa bazata iya gayawa Fatee hakan ba baida maraba da daɓawa cikinta wuƙa da kanta tana zaunawa ta ce "Shi dai ya sani." Dr. Fatee ta ce "To yanzu yau saura kwana biyar ba wani aiki a asibitin nan Season 7 in and out spa zamuje kar yaron nan ya rainaki dole muyi gyaran jiki." Ita abin baima zo mata ba haka suka shirya suka fita acan fa fata taga bone sai uban sheƙi take tayi ja ga wani uban ƙamshi don ba kalan mulkan da bata sha ba can aka sassaya mata kayan mata wurin Sweetner zone by season 7 ya rahman Date syrup kadai data sha amma tun a wurin ta fara ɓulbula ita dai Dr. Fatee bata fasa kumbura mata kai ba haka har sai 7 na yamma suka baro wurin a lokacin kuwa tun wuraren 4 wayar Dr. Nas ya ɗauke ba chargy don haka bata iso gidanba sai 8 Dr. Fati ta sauke ta suka yi sallama akan sai gobe zasu koma saboda sai alhamis za'a gama, da ƙafa ta tako zuwa cikin gidan shikuma dake zaune tun ɗazu a hasale yana tunanin wai tukunna ina ta shiga sai tashi ya yi kawai ya jera da ita suna tafiya tana ganinsa ta ce "Saif." Batare da ha kalleta ba ya ce "Daga ina kike?" Tsayawa ta yi ta masa wani kallon kai asuwa sannan taja tsaki a sarari kafin ta ce "Wai Saif me ka ɗaukeni ne? Haifata kayi kome? Ina ruwanka daga inda nake to?" Murmushinsa me kyau ya yi yana kallonta acikin hasken fitilun da suka haske wurin yaga yanda take ƙyalli ga wani tsinannen saasanyan ƙamshi da ke tashi a jikinta da bai saba jinta da shi ba , ya ce "Allah ya baki haƙuri ranki ya daɗe just showing concern." Tana ƙarawa tafiyarta sauri ta ce "Ai kuma kasan cewar niba yarinya bace ko?" Ragewa takunsa sauri ya yi yaja baya a hankali ta wuce cikin gidan tana mejin zafin abin a ranta duk gani take hala zarginta ya ke dayake binta da tuhuma don ma tsabar wulaƙanci yanzu Saif baya gayar da ita sai idan ita ta gaisheshi.

YOU ARE READING
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)
Ficción GeneralRayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????