SHAFI NA GOMA

68 2 0
                                    

*MAI SAƘO*
   *(GARIN NEMAN GIRA..)*

*BILKISU GALADANCHI*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION.*

 Arewa books at: https://arewabooks.com/book?id=6646536dc575fcfa9ee217d8

   10.

Meenal tasha kukan da ta rasa dalilin yinshi ma, wuni ɗaya cur a ɗaki ta yishi har yamma, Bata kuma ƙara ganin Zuhair ba sai bayan da Mom ta sanya aka kirata saboda Dinner suna zaune dukkansu Dad ya kalli Meenal ya ce "Mimi." Ɗago idon ta tayi da suka kumbura tana kallonsa ya ce  " Whats wrong with you did you cry? Your eyes are swollen." Nan da nan ruwa ya kawo idon ta tana kallon Dad ta ce "Daddy Ba yaa ZM bane ya wai yaketamun faɗa just because i hugged him har yana cewa kar in ƙara shiga mishi ɗaki kuma kar in ƙara kwana a ɗakinshi kuma wata rana ni tsoro nakeji kawai sai idan ɗakin momy zan koma da naka." Dad ajiye Fuck ɗin hannunsa ya yi ya ɗaga kai yana kallon ZM da mamaki kafin ya ce "Yaron Daddy wai haka ne?" Haɗe rai ZM ya yi kafin ya ce "Dad Mimi fa ta girma akan me zata riƙa kwana a ɗakina bayan haka bata barin mutum ya huta son jiki kamar mage." Mom ce ta karɓe zancen da cewa

"A lallai ZM girma ya kamaka ka rika wulaƙantamun da yarinya, she is your little sister for goodness sake, if you don't take care of her who will?" Kallon Mom ɗinsa ya yi da some second kafin ya ce"She can also take care of her self mom, shekarun ta nawa." A fusace ta ce

"Just 14? Kanada hankali kuwa? Kai ma da kake namiji shekaru nawa nayi ina kwana da kai da Dad a ɗaki ɗaya? Kai ka zaɓi zaka barmu at the age of 12 kuma ina zuwa dubaka ai, yanzu zan baka amanar yarinyata ta wulaƙanta, na taba hanaka hugging ɗina? Ko ni ban girma ba ko kai baka girma ba, look ZM wallahi ka shiga hankalinka ta rungumeka ɗin sai me? Daga yanxu ma ka daina barmun yarinya ita kaɗai a ɗaki after all the bed can contai more than people which is more than enough for the both of you."  Da mamaki yake kallonta har ta gama Dad ya karɓe

"Wannan ma ai maganar banza ne ai ZM yarinya da 14yrs idan wani abu yaje ya sameta fa ita kaɗai a ɗaki, koda zata kwana ɗakinka banji akwai wani matsala ko don tana mace, na raba muku ɗakine saboda ita pink girl ce kai kuma komai gray if not because of that bazan raba ɗakinba, bahaushe ya gama hure muku kunne kunata shirme da ƙauyanci, here me out and loud now ko da wasa karka ƙara takurawa Mimi idan a wurinka zata kwana shikenan." A hankali jin mahaifinsa ya yi shiru ya ce "Ok Dad bazan ƙara ba in shaa Allah." Miƙewa ya yi yana kallonsa ransa a ɓace ya ce "Better." Sannan yabar dining ɗin batare da ya kammala cin abincin ba Mom ta bishi da kallo kafin ta kalli Zuhair ranta a ɓace tace

"You c what your mental actions caused ko? Kasan halinsa yanxu sai yafi sati yana wannan fushin now follow him ka bashi haƙuri." Zuhair jikinsa a sanyaye ya bi bayan Dad yaje ya bashi haƙuri sai da ya ƙara tabbatar mai ya bar kanwarsa tayi yanda takeso sannan ya haƙura. ZM kai tsaye motarsa ya ɗauka yabar gidan batare da ya shirya hakan ba a wunin ranar cur  be dawo ba sai wuraren 11 na dare.

   A parlour ya tarar da su har Meenal tana zaune akan one sitter da laptop akan cinyarta sai earpeace a kunnenta tana kallon wani korean series ,su kuma kamar ko yaushe suna kallon movie a babban Flat screan Tv manne da juna, Dad na kallonsa ya ce "Mun dawo tun 8:pm Meenal ta ce baka dawo ba tunda ka fita daga ina kake." Calmly ya ce "Na je school daga nan naje wurin karatu." Kallonsa kawai Dad keyi kafin ya ce "Alright now go get some rest." Daga haka ya nufi ciki batare da ya kalli Meenal dake zaune wurin ba ita ma bata ce masa komai ba har ya shige Dad na kallonta ya ce

"Meenal you didn't greet your brother why?"  Tace

"Daddy ai kamar fushi yake dani saboda na yi reporting nashi a wurinku."

"Go and great him ki basa hakuri and ki kwanta its late now." Mikewaya ta yi bayan ta kashe laptop ɗin sannan ta barta laptop ɗin a parlour ta wuce ciki sai da ta rufo ƙodar balcony ɗin sannan ta wuce ɗakinta wanka ta yi da duk abin da ta saba yi sannan kai tsaye ta nufi ɗakinsa da sallama ta shiga ta tarar yana zaune da singlet da wandon pyjama's, zama tayi a kusa da shi sannan ta ce "Yayaa." Kallonta ya ɗago ya yi baice komai ba, rungumeshi ta yi a hankali ta ce "To ka yi haƙuri kaji, tunda kake fushi da ni ko abinci na kasa ci wallahi." Ɗan janye jikinsa ya yi kaɗan daga nata kafin ya ce "Ba komai Meenal kema kiyi haƙuri." Tana murmushi ta ce "Thank you so much swt bro." Nan sukayi shiru ta janye daga jikinsa ta kwanta a saman gadon shi dai yanata zaune bai kawnata ba, Bashir ta kira a karo na barkatai bayan ya daina ɗaga wayarta sai a ranar ya ɗaga kiran yaƙi magana muryarta ƙasa ƙasa ta ce "Yaa Bashir don Allah kayi haƙuri kaji." Sai da ya ɗanja fasali kafin ya ce "Ya wuce." A hankali ta ce "Your not picking my calls your not replying to my WhatsApp messages nor replying my texts messages i was worried bana ma iya cin abinci." Ɗan murmushi ya yi kamar tana ganinshi ya ce "Really?" Gyaɗa masa kai ta yi "Sure mana i missed you when zaka taho kaduna." Shafa berds ɗinshi yay kafin ya ce "Mun kusa fara exam Mimi sai na samu hutu." A  hankali ta ce "Ohh but i miss you so mcuh.' kamar yana raɗa ya ce "Same." Dariya ta yi kafin tace komai ya ce "Hold on a minute." Ya yi holding call ɗin ya ɗauki wani call kusan 2mns 3 seconds sannan ya dawo a hankali ya ce "Sorry Mimi i have to pick the call." Gyaran kwanciyarta ta yi kafin ta ce "kai da waye its late fa." Dariya ya yi kafin yace my girlfriend mufeedah she called to say good night" shiru ya ji tayi kafin ya ce "Hello are you there?." Katse kiran tayi ƙirjinta na wani irin dokawa ta rasa dalilin jin hakan, sake kiranta ya yi ta ɗaga ya ce "Why do you hang up Mimi?" A taƙaice tace "To let you say enough good night to your girlfriend." Dariya ma tabasa ya ce

MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA)Where stories live. Discover now