🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺© Pure Moment Of Life Writer
Wannan shafin nakune 'yan pure moment of life💋Allah yabar k'auna atsakaninmu ameen❤
Page 2
K'ofar gidan alhaji abdullahi bakari acike yake da jama'a,sakamakon d'aurin aure da za'ayi na atif muhammad bakari da kuma mubinat abdullahi bakari.
Guri yayi kyau sosai inda ango yasha farin voyel mai kyau tasha aiki bansan wani kyau zance muku atif yayi tunda mada shid'in maikyaune. Fararen hakwaransa kawai ake gani a waje,wanda yake k'ara masa kyau.
Abokansa kuwa ankon shadda milk sukayi duk aikinsu kusan iri d'ayane. Hmm kusan 'yan kwallo da farin jini karkuga yadda suka had'u abundai se wanda ya gani.
Mubinat kuwa tundata shiga d'aki ta kulle kanta sam tak'i bud'ewa ko wanka tak'iyi,babu yadda ba'ayi da itaba amma sam tak'i bata sauraron kowa. Jitake kamar ta gudu amma babu halin yin hakan,ahankali ta bud'e kofar lokacin datajiyo an fara shirin d'aura aurenta.
Yana shirin fita zuwa gun d'aurin auren sakamakon lattin da shureim yasa sukayi,kawai seyaji an damk'i garensa tabaya ance "ya farhan dan Allah karkaje wannan auren ka d'aukeni mugudu dan Allah."
"Me hakane kikeyi sis mubee,dumekifa ko d'ankwali babu kuma ga mutane pls kikoma ciki kinji?" "No ya farhan wlh bazakajeba bakuma zanje ko ina sedai mutafi tare,wlh bana son wannan auren pls kadakar domin kai kad'ai zaka iya dakatar da auren pls ya farhan." Kuka sosai takeyi,inda 'yan'uwa suka janyeta amma setayi saurin rungume ya farhan tare da damk'eshi gam ajikinta tana kuka.
"Wlh bana sonshi kainakeso ya farhan kaine farincikina dan Allah kusakeni bana son wannan auren ya farhan nakeso dan Allah abba kar'ayimin auren dole kutausayamin dan Allah.
Amal da shureim dai se kuka sukeyi tare da k'anwar atif d'in mai suna aisha.
Mutanen wajema suna iya jiyo kukan mubinat,kuma sam an kasa b'anb'areta daga jikin farhan.
Shikanshi farhan tausayinta ya kamashi,kuma sam yakasa janye jikinshi daga nata kome yakeji aranshi oho. "Stop it sis mubee kinsan me kikeyi kuwa,yakamata ki amince da wannan auren dan Allah kibarni in tafi...katafi? Zuwa ina kena,sedai mutafi tare wlh Allah bazan tab'a sakekaba sedai inna dena numfashi,baka ganewane wai? You are the one that i love ya farhan kaine abun k'aunata soyayyarka na fara ginawa azuciyata ya farhan ina duba halin da zaka shigane bayan kadawo hayyacinka yama za'ace babu wacce zata b'ace a kwakwalwarka seni,meyake faruwa dakaine ya farhan? Nice fa habibtinka kamance wannan sunan "habibti?" Kaine kasamin shi kaine malaminafa...atif ne yajanyeta da kyar ajikin farhan,se ihu takeyi tana banaso karku rabani da habibina dan Allah karka je gun auren ya farhan i love you pls karka fita. Umma ce ta wanketa da mari tace "wai me hakane mubinat,kishiga hankalinki fa,haba umma kemafa kinsan komai dan Allah karku rabani da zuciya domin ya farhan shine zuciya inbashi bani umma.
Hawaye umma takeyi tana cewa nasan haka,amma Allah yayi atif shine mijinki ba farhan ba kisa hakan aranki. Ganin farhan yakai har gate din gidanne yasa ta k'ara kuka tana cewa "habibi" take ya juyo yana kallonta, "iwaly habibi" tana hawaye ta sake furta "yon habibi" ya farhan ina fatan bazaka mance wad'annan kalmominba guda biyu,idan kamance komai tofa inaso ka tuna da wad'annan kalmomin,ka tuna da "innoby habibtee?"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" farhan ya juya ya kalli shureim sannan ya maida kyawawan idanunsa kan mubinat,take kwalla ya cika masa ido domin tabbas ya dawo hayyacinsa daga jin wad'annan kalmomin da habibtinsa ta furta.
Amma ina bazai iya b'ata wannan aurenba adaidai wannan lokacin,hannun shureim ya kamo suka fita gun d'aurin auren.
Mubinat kam seta rungume ummanta tacigaba da kuka yayinda atif ya koma gun d'aurin aurensa cike da damuwa a ransa.
Tunda farhan ya fita yaji kamar zazzab'ine takeson kamshi,domin ya tuna komai. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yaketa maimaitawa azuciyarsa. Ahmad abokinsa ya lura dashi dan haka yazo kusa dashi yake tambayarsa farhan are you okey? "No i'm not ahmad,tell me something auren habibti akeyi da atif dagaske?" Zaro ido ahmad yayi yace habibti fa kace, kana nufin kadawo hayyacinka ka tuna da komai? Kai kawai ya d'agawa ahmad,Alhamdulillah ahmad ya furta tare da niyan mik'ewa yace za'a d'aura aurennan dakai barina sanar da abba...no ahmad karka b'ata wannan auren duk d'ayane ai,nida atif duk abu d'aya dan haka kamance cewa nadawo hayyacina kabarshi aranka batare da kowa ya saniba hakan shizaisa habibti tazauna agidan atif. Ahmad yace naji mai sadaukarwa,amma kai kuma fa zaka iya hak'urin rashintane? Farhan yasa hannunsa abaki tare da fitar da iska yasake shafar hular kansa yace i don know...Hmmm an d'aura aure an gama komai,amma sam farhan baima sam meyakeyiba. Mahaifinsa ya janyo daga gun d'aurin aure bayan ya gama gaisawa da mutane,mota ya sanya mahaifinsa ciki shida abokinsa ahmad sannan yacewa shureim yaje gida yanzu zai dawo,sam shureim yak'i,seyace to kaje ka rarrashi sis mubee zan dawo yanzu mufita dakai kaji? To yace sannan ya tafi da gudu.
Farhan bai b'oyewa mahaifinsa kan cewa yatuna da komai yadawo hayyacinsa,ya gayamasa komai harda kwalla akan rasa mubinat masoyiyarsa dayayi. Mahaifinsa ya tsinci kansa cikin wani irin yanayi,bak'in ciki zaiyi koko farin ciki? Farhan yacigaba da cewa abbi bazan iya cigaba da zamaba ahalin yanzu,dan haka zan koma gun ummi dama viza na yana nan,zanje ind'an huta abbi. Rungume mahaifinsa yayi yana mai zubda hawaye masu zafi,ahmad kuwa se shafar kafad'arsa yake shima yanajin abin aransa.
Mahaifinsa ya aminta da dukkan shawaransu,yasan acan madinan gun mahaifiyarsa da kuma sauran 'yan'uwansa zaifi samu sauk'i akan zamansa anan nigeria.
Da wannan shawaran suka rabu,kuma sunyi alk'awarin bazasu sanar da kowaba...Bayan sallan isha aketa shirin d'aukan amarya mubinat wanda har wannan lokacin tak'i tayi wanka,babu yadda ba'ayi da itaba amma sam tak'i,dan haka aka kyaleta akace zakije kiyita mishi wari ai,ko kulasu batayiba tama bar musu d'akin rik'e da waya a hannunta.
Wayar atif ta kira sekuwa aka d'auka da sauri tare da cewa "hello sis mubee" inaso inje gun ya farhan muyi magana,dad'i atif yaji wato harta farayin biyayya,bakomai yace da ita na amince miki. "Kasanfa dolene idan naje sena rik'eshi naji d'uminsa akusa dani,bakomai sis mubee na amince indai hakan zaisaki farinciki tobakomai kije fatana shine kidena sa damuwa a ranki pls my luv. Ya k'arasa maganar kamar mai shirin yin kuka,katse wayar tayi batare datace komaiba ta nufi d'akin ya farhan da sallama ta shiga.
Farhan yana had'a kayansa shikuwa ahmad yana zaune yayi tagumi.
Idanun farhan take gani wanda yake d'auke da tambaya,mik'ewa yayi yanufo inda take tsaye shima idanunta yakebi da kallo duksun dishe kamarba idanun habibtinshiba masu kyan kallo.
"Ya farhan ina zakaje kake had'a kayanka?"
Idanunsa ya k'aik'aya yace zanje gun ummi nane. "Umminka,kana nufin can saudi?"
Kai ya d'aga mata alamun eh. "Tomeyasa yanzu,meyasa zaka tafi kabarni ya farhan dan Allah karka tafi kabarni kayi hak'uri."
Murmushin k'arfin hali yayi yace "sis mubee ummi bata jin dad'ine kuma tana buk'atana kusa da ita kinga dolene in tafi ko?" Kaita d'aga tare da share kwallan idanuta tace"Allah yabata lfy,yace ameen.
"Yaushe zaka tafi kuma yaushe zakadawo?"
"Gobe zan wuce abuja,jibi kuma zamu tashi." Shuru tayi nad'an wani lokaci sannan ta matso dab dashi ta rungumeshi tanana kuka mai shiga zuciya,wani iri yaji,seya fara k'ok'arin janyeta daga jikinshi "kibari mana sis mubee,kefa matar wanine yanzu."
"Dan Allah ka kyaleni kozanji sanyi araina,kumama aina nemi izinin yin hakan kafin nazo nand'in."
"Kina nufin...dan Allah kayi shuru ya farhan,kabarni inji da abinda yake damuna acikin zuciyata pls."
Farhan yasan hakan baidaceba,amma shima yana cikin wani hali wanda awannan lokacin jin mubinat kusa dashi shine kawai mafita agareshi,dan haka shima yasa hannunsa biyu ya rungumeta tsam ajikinsa yana hawaye.
Sallamar atif ne yasa farhan yayi saurin saketa tare da goge kwallan fiskarshi yamaida kallonsa gun atif,ita kuwa mubinat ko'a jikinta batama san yashigoba tana rungume da farhan tana kuka ahankali...
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...