🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺*©Pure Momment Of Life Writers*
We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.comPage 48
Yau ne su Abbi suka iso k'asar Nigeria bayan an tarosu kai tsaye suka wuce gidansu acan aka yada zango da dukkan 'yan gidan su Mubeenat dama an musu girki dan haka aka tafi musu dashi amma banda ita Mubeenat tana gidan su Amal suna kallo a d'akin Amal d'in inda Sagir yaketa iya shegensa daga parlour amma ko kulashi basu yiba kamar yadda Abba ya gargad'e su.
Ummin Farhan ta damu tana son ganin Habibty,inda Ummanta tace "Ai tana can gidansu Amal wai ita kunyar ki takeji amma gobe zan turo miki ita."
"Hhh Mubeenat dama can akwai kunya ai bare kuma yanzu" cewar Abbin Farhan.
Haka suka yini musu sai bayan la'asar sannan suka koma gida.
Cikin sauri Mubeenat ta dawo gida tana cewa "Umma ya kuka sami su Ummin da Abbi?"
"Lafiyansu k'alau sai tambayar ki sukeyi,dan haka saiki shirya gobe da safe kije ki gaishe su"
"To amma wlh Umma kunya nake ji fa"
"Kunji min iyayi kuma,to kuma shikenan dan kina kunya baza kije ki musu sannu da zuwa ba? Idan baki jeba aisu sa biyoki dan tana son ganinki sosai."
Dad'i sosai Mubeenat taji har cikin ranta,dan haka tasa a ranta zataje goben.Kanta a sunkuye tana zaune a k'asa "Ina kwana Ummi kun iso lafiya"
"Habibty wannan duk kunya ce haka? Nidai bana son irin wannan jin kunya haka ki d'aukeni kamar Ummanki nima, tashi ki zauna a sama"
"A'a Ummi nan d'inma yayi"
"To bari in d'agata tunda tak'i Ummi" cewar Farhan.
Cikin sauri ta mik'e ta zauna kusa da Ummin suna mata dariya yayin da Ummi ta shafi kanta tace "Habibty tun jiya nake son ganinki dan naga Habibina yayi k'iba nasan kuma kece sila me kike dafa mishine haka?"
Murmushi Mubeenat tayi tare da kwantar da kanta a jikin Ummi tana murmushi.
Shima Farhan d'in kwantar da kanshi yayi ta d'ayan gefen jikin Ummin nashi ta yadda suke fuskantar juna shida Mubeenat.
Murmushi kawai suke yiwa junansu sai Ummi ta katse su da cewa "Habibi ka tashi a jikina karka sa in fara kishi fa"
"Kishi kuma Ummi,me yasa zakiyi kishi?"
"Saboda gaba d'aya naga kamar yanzu kafi son Habibty akai na"
Dariya sosai sukayi dukkansu sannan Farhan ya d'ago da kai yana kallon ta "Ummi taya zaki had'a soyayyarki dana Habibty? Ai koda wasa bata ma zo kusa dake ba Ummina,domin k'aunar da nake miki daban ne bana tab'a had'aki da kowa" ya k'arashe maganar yana tsunbatar hannunta.
Dad'i taji sosai tace "Ka sake fad'a dai saboda Habibty taji da kyau"
Mubeenat dai sai dariya takeyi, Farhan ya sake cewa "Ummi idan har ina tare da ke to sam bana tuna Habibty kwata-kwata,amma idan ina tare da ita dolene saina tuna dake wannan shine son da nake miki Umminah."
Tsunbatar sa tayi a goshi tace "Shiyasa a koda yaushe nake godewa Allah daya bani D'a d'an albarka irinka Habibi,ana hubbuka Habibi."
Dad'i yaji shima ya kalli Mubeenat yace "Ana hubbuki Habibty"
Cikin sauri Umminsa tace "Waye?"
Yayi saurin cewa "I mean ana hubbuki Ummi"
Dariya suka sake sawa dukkansu sannan sukaci gaba da hiransu cikin so da k'auna suna kwance a jikin Ummi tana musu nasiha.Satin su guda kenan a Nigeria sai Abbin Farhan ya d'ibesu sukaje gurin danginsa suka kwana biyu sannan suka dawo gaba d'aya da Family nashi dan ayi tambayar auren Mubeenat.
An cika sosai inda ake zaune da Dad d'in su Atif da kuma Abban Amal da dai 'yan'uwa akayi tambaya akan Mubeenat, nan akace dasu an basu tare da tsaida rana nan da wata Uku za'ayi bikin.
Murna agurin wad'annan masoya baya misaltuwa tunba shi Farhan d'inba da yake ganin kamar lokacin bazai zoba.
Kayan tambayan kawai abin kallo ne wanda suka taho dashi daga Madina wane kayan aure,a hakan kuma wai idan auren ya matso zasu zo da kayan aure.
Kowa sai san barka yakeyi akan bikin nasu tare da fatan Allah ya nuna mana.Watan su d'aya suka koma inda suka cewa Farhan zaije Madina nan da sati biyu domin k'arasa shirinsa na can sannan ya dawo.
Shi kuwa Atif baisan yana son Mubeenat ba sai a yanzu dayaga dai da gaske bikin yazo.
Hankalinsa a tashe sosai yaje gurin Hajiya Kaka yana magiya "Dan Allah Hajiya Kaka kiyi wani abu akai wlh bazan iya rasa Sis Mubee ba"
"Atif nayi iya k'ok'arina amma dukka b'ata min shiri dan haka zan gwada ta wata hanyar in hakan zaiyu to"
"To Hajiya Kaka nagode"
Hajiya kaka ta nasar da Dad d'in Atif abinda ke faruwa,amma sai yace mata ai lokaci ya k'ure Hajiya ni kaina naso ace munyi wannan zumunci amma Allah bai yiba dan haka yayi hak'uri.
Babu yadda Atif ya iya haka ya d'au hak'uri badan yaso ba.
Idan ka ganshi kasan yana cikin wani hali dan haka abokansa sukace bazasu bari abokinsu ya shiga wani hali ba,karma daga baya ya kasa yin wasan k'wallon gashi kusan shine ma mai k'ok'arin cikinsu dan haka suka shiryawa Farhan gadan zare ba tare da sanin shi Atif d'in ba.Mubeenat tayi shiga mai kyau inda Farhan yana jiran fitowarta zasuje ya gaida Mahaifiyar Aisha Kabir k'awarta mai rasuwa ta sanadiyar amfani da wasu magungunan mata wanda bamu san dame ake had'a suba.
Kallonta ya tsaya yi dan yadda yaga tayi kyau sosai. "Ya Farhan zan bika nima" cewar Shureim.
"To shiga baya muje" cikin murna ya shige sannan Mubeenat ta zauna a gaba Umma tana musu Allah ya kiyaye hanya.
Tunda motar Farhan yabar gida Abokan Atif suka samu labari ta hanyar wani da sukasa yana bibiyarsa.
"Habibty irin wannan wanka haka har kinsa na fara kishi fa,kar wani ya kalle min ke?"
"Ka kwantar da hankalinka ango to be,domin Mubeenat taka ce kai d'aya tak"
Juyowa yayi ya kalli Shureim dake kwance a baya kamar wanda ya samu gado. Murmushi yayi tare da cewa "Dan dai yau muna da yawane amma dana ce wani abu"
Murmushi tayi tare da cewa "Habibi bana ganin yawan mutane indai ina tare da kai,sannan bana shakkar fad'in abinda zuciyata ta gaya min domin wanda na ajiyeta a cikinsa Mutumin kirki ne kuma abin alfaharina"
Dad'i mara misaltuwa ne ya kama Farhan wanda har yana ganin gara yayi shuru dan idan sukaci gaba to lallai Habibty zata cinye shi da kalaman soyayyarta masu sanyaya mishi zuciya.
"Ya naji kayi shurune my Star? Kodai ka bar min gurine domin inyita baje maka kolina? Indai kuwa hakane to lallai ka sake kakkab'e kunnuwanka sannan ka bud'e min zuciyarka domin in shige ciki nasan duk abinda zai faru a ciki to lallai zaka jishi a kunnuwanka yayin da zansa zuciyarka yin bacci da sassanyar kalamaina wanda dankai kad'ai nayisu."
Hmmm ba Farhan kad'ai ba,harni sadnas gyara zama nayi ina sauraron wad'annan kalaman na Mubeenat harma nayi jorting cikin shafi akai.
Har suka iso inda zasu Farhan maiba san an iso ba saida ta taimaka mishi gurin dakatawa da baitikanta tace "Haba Habibinah munfa wuce gidan"
"Nasan baza kiga laifina ba sabida kece kika mantar dani a cikin zuciyarki ko kuwa ince kika makantar dani."
"Hhh tona gode,zuwa bayan azahar seka dawo mu koma"
"Yes Mah" ya fad'a yana tsosar lips nashi.
Idonta takai baya taga Shureim kam har yayi bacci abinshi dama baccin yakeji tun a gida amma dayake yana son yawo sai daya biyo su.
Murmushi sukayi a tare sannan Farhan ya fito sukaje suka gaisa sannan ta sake rakoshi gun mota inda ya d'ago shureim ya dawo dashi gaba duk yana bacci.
Kallonta yake cike da so da k'auna "Habibty sena dawo"
"To Allah ya kare min kai"
"Ameen nagode" sannan ya tafi yana hangota daga mirro inda take tsaye tana binsa da byeee.Farhan yana cikin tafiya amma se kewar Mubeenat yakeyi kamar wanda suka dad'e basu had'u ba.
Nan ya tuna da kalamanta inda take ce mishi _"Habibi aduk lokacin dakaji kana kewata sosai toka bud'e wannan choculate d'in kasha,acikin d'and'anonsa zakaji tana had'e da soyayyata zuwa gareka"_
Murmushi Farhan yayi tare da ambaton sunanta kamar tana jinsa "Habibty" sannan ya b'are wannan choculate d'in yana gutsuransa a hankali kamar bazai sha ba.
Wata babbar mota ce ta nufo kansu,hon Farhan yake musu dan yaga sunata nufowa kansa,amma duk da haka baisa sun kauce ba gashi dama titin ba wani motoci sosai su biyunne kawai akan hanyan.
Cikin rud'ewa Farhan ya fara fad'in _"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"_ wanda hakan yasa Shureim farkawa daga bacci, take yasa ihu mai k'arfin gaske a lokacin da yaga Farhan ya kaucewa k'atuwar motar sun nufi gun wani k'aton dutse mai girma sosai har a lokacin Farhan salati yakeyi yayin da shi kuwa Shureim ya tsume dan tsorata dayayi.
Cikin rud'ewa Farhan ya kira sunan Shureim ganin ya suma,kan ya sake kaucewa dutsen tuni suka bugi wannan dutsen da karfi wanda seda motar tayita juyi kusan sau biyu kafin ta fad'o a k'asa ji kake chaaas.
Cikin sauri mutanen da Abokan Atif suka basu wannan aikin suka k'araso gurin nan sukaga jini yana zuba daga gefen kan Farhan jikinsa babu kyan gani Shureim kuwa ya fad'a can gefe.
Da wuri suka fito da Farhan tare da d'auko Shureim suka ajiyesu a gefe,shi kuwa mai tuk'a babbar motar seya wuce kamar ma baisan anyi hatsariba.
Nan suka kama ihu suna cewa "Jama'a ku taimaka mana dan Allah" kan ace kwabo mutane sun taru agun bila adadin kowa cewa yake "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" mutane dewa daga cikinsu sun gane Farhan dayake akwai wanda suke aiki a Company nashi dan haka aka d'aukesu cikin gaggawa se Hospital yayinda wani daga cikinsu yace yana da No Abban Mubeenat nan aka kira wayarsa yanata ringing...😥Votr and comment frirnds
Team FARBEEN
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...