1

4.3K 147 7
                                    

🍉🍇🍇🍉🍇🍇🍉🍇🍇
*KOMAI NISAN JIFA*
🍉🍇🍇🍉🍇🍇🍉🍇🍇                 
                        
        *by maman shureim*
               🌺sad-nas🌺

*©pure moment of life writters*

*ASSALAMU ALAIKUM.*
*'Yan'uwana ina muku barka da sallah tare da fatan Allah ya nuna mana nagaba Allah yasa muna cikin 'yantattun bayin watan ramada Allah kuma ya karb'i ibadunmu ya kuma gafarta mana zunubammu ameeen...*

_Masoyana ina mik'a muku sak'on gaisuwata mai d'auke da tarin k'auna,Allah yabar zumunci ameen._
  _Sannan ina muku albishir da cewa nadawo kamar dai yadda namuku alk'awari,Allah yasa yadda na fara wannan littafi nawa lfy in gamata lfy,Allah ya bani ikon ilmartarwa da fad'in daidai ameen._

*wanan shafin farko nayishine dan Aneesa abubakar rimi, billylosh,da kuma FIDDY G,ina muku fatan alkhairi agidajenku na aure Allah yabada zaman lfy,Allah ya dauwamar daku agidajenku har abada ya kareku daga dukkan sharrin shaid'an ameen*❤❤❤

Page 1
Kuka sosai takeyi kamar wacce akayiwa rasuwa ta zamto abin tausayi gaduk wanda yaganta.
Amal ce zaune agefenta itama kukan takeyi tana rarrashinta,dukda tasan cewa sam *mubinat* bata sauraronta amma taci gaba da rarrashi tana cewa "Dan Allah mubinat kidena kukan kanki zaiyi ciwo kibarwa Allah komai kinji?"
"Dago da kanta tayi fiskanta cike da kwalla da majina tace "amal kibarni inyi kuka kozanji sanyi araina,amal ina son Ya atif sosai amma son yaya da k'anwa bawai so na masoyi da masoyiyaba bazan taba iya mallakamishi kainaba dan haka nibanga anfanin aurenmuba wlh zaku nemini ku sara muddin aka d'aura wannan auren wlh bana k'aunarsa a matsayin uban 'ya'yana kije ki fahimtar dasu ABBA kozasu fasa auren pls amal...
  "Kuka sosai amal takeyi tare da k'ara rungume aminiyarta tana cewa bakin alk'alami ya riga daya bushe an gama raba katin aurenku nan da 2hrs za'a d'aura muku aure dole kid'au wannan kaddaran mubinat kibarwa Allah. Shuru amal tayi saboda ta kasa karashe maganan sakamakon kuka dayaci karfinta tana goge kwalla.
  Mubinata ta tsaya da kukanta dan ganin yadda amal tashiga damuwa,kamota tayi tana goge kwallan tace shikenan amal nahakura kidena kuka,da sauri amal ta d'ago kai tana kallon mubinat amma daga ganin fiskanta tasan akwai wani abu aran mubinat bawai ta hakuran bane.
"Yauwa mubinat pls karki sakeyin kuka bari inje gida in d'ibo kayana dan mushirya akan lokaci kinji?" To tace da ita sannan amal ta tafi.
Mubinat ta fito tsakar gida ko d'ankwali babu akanta gun abba ta wuce,amma bayanan umma kawai ta samu da mutane anata hidima. Kusa da umma taje ta rik'ota tace umma kina sona kuwa kamar yadda mahaifiyata take sona? Umma ta kamota zuwa jikinta tace haba mubinat ina k'aunarki fiye da hakama meyasa kike fad'in haka,kidena kinji?
Janye jikinta tayi daga gun umman tana komawa da baya tare da kwalla tace sam banga alama umma,da kina sona dakin dakatar da wannan auren tunda kowa shaidane cewa banzab'i ya atif a matsayin mijiba wlh Allah bana kaunarsa idan kuma akayi auren wlh bazaku sake ganinaba wannan alk'awari na d'aukawa kaina. Tana kaiwa nan ta fice aguje taa kuka mai karfi,kowa a palon jikinsa yayi sanyi, umma kuwa hawayene yaketa zuba daga idanunta tanajin irin k'unar da mubinat 'yarta keji,amma babu abinda zata iyayi akai domin lokaci ya k'ure.

  Atif ango kuwa yana can shida friends nashi sunata shirye shirye,amma sam hankalinsa nakan *sis mubinat*,shikanshi tausayinta yakeji amma kuma bazai iya hak'uraba dan yana matuk'ar k'aunarta fiye da tunanin masu karatu.
"Guys zanje gida idan kun gama zamu had'u,ok sukace dashi sannan ya d'auki motarsa se hanyan gida. Wayar amal ya kira ,bugu d'aya ta d'aga tare da sallama,amal kuna tare da sis mubee ne? A'a yanzu na barta a gida amma zan koma yanzu. Ok amma ya take? Well gaskya babu wani canji akan yadda ka sani,tana nan akan bakanta. Hankalinsa atashe yace "oh my God" pls amal kishawomin kan sis mubee,amal i luv her nd i promise to take care of her pls amal do mosething bazan iya rayuwa ba sis mubee ba plss. Dukda cewa itama amal bata son mubinat da ya atif amma yana bata tausayi sosai har cikin zuciyarta,kuma tasan cewa ya atif zai rik'eta rik'o na hak'ik'a zai kula da ita sosai amma kuma kash sam mubinat bata k'aunarshi. Atif yaji shuru daga b'angaren amal dan haka ya sake cewa amal ar u there? "Tace yes bakomai ya atif amma pls ina neman wata alfarma agare dukda dai nasan baishafeniba pls karkayi k'ok'arin tarayya da mubee harse ta fara sonka pls?"
"Shuru atif yayi,azuciyarsa kuwa cewa yake damuwar sis mubee kenan,tabbas yasan sis mubee ne ta gayamata hakan. Murmushi yayi tare da cewa indai wannane matsalar takwantar da hankalinta,amal zan zauna da sis mubee koda babu komai tsaanina da ita i promiss. Shikenan ya atif bari inje gurinta dan ita kad'ai na bari.

  Muryan shureim takeji tundaga waje yana dariya. Wuf ta tashi kamar ba itaba ta fito tsakar gida da gudu ta k'arasa gun motarsu. Da sauri shureim yazo ya rungumeta yana kwalla,kwallan data gani a fiskar shureim ne yatabbatar mata da cewa yauma babu wani nasara da'akayi.
Mik'ewa tayi ta nufi hanyan zuwa shashinsu tana zubar da kwalla masu zafin gaske,shikuwa baida niyan tsayawa sam,dan haka tasha gabansa ta tsaya suna kallon juna cikin ido.
"Meyasa kake son ka haukatanine,meyake faruwane nakasa fahimtar komai *ya farhan* dan Allah ka fahimtar dani,nan da 1hr za'a d'aura min aure fa da ya atif shikenan bani bakai fa ya faran mun rasa junanmu fa kenan baka ganewane wai? Dan Allah ka dawo hayyacinka ya farhan dakai kad'ai zan iya rayuwa pls ya farhan ka farka daga baccin da kakeyi plsss idan na rasaka rayuwata batada amfani habibina pls...
Motar atif ne ya shigo haraban gidan,tun daga nesa yake hango sis mubee durkushe agan farhan tana kuka sosai. Farhan yace sister mubinat pls kidena kuka ki tashi kinji? Shureim yace dole tayi kuka ya farhan yaza'ayi ace ka kasa ganeta aurentafa za'ayi yah farhan ina tausaya maka idan har kazo ka gane wacece sis mubee agurinka dan wlh nasan halinda zaka shiga seyafi wanda ita take ciki ayanzu dan nikad'ai nasan irin k'aunar da kakeyiwa sis mubee dan Allah kadowo hayyacinka yah farhan.
"Sam farhan bayason ganin shureim cikin damuwa dan haka ya rik'o shureim yana share mishi hawaye yace "shureim naganeta mana sis mubee ce kacemin koh aiban manceba kacemata tadena kuka. Kamance mana, kaizaka rarrasheta baniba domin rarrashinka take bukata a yanzu.
  Kallonta yayi cike da murmushi afiskarsa yace "tashi sis mubee nd pls stop craying okay?" Koba komai taji sanyi a ranta,atare suka d'ago zuwa sama yana mata murmushi itama haka.
  "Atif ya dad'e atsaye yana kallonsu,matsowa yayi kusa da farhan suka gaisa,ai kuwa seyace toga sis mubee kasake rarrashinta koza dena kuka,atif yayi murmushi yace ai duk gidannan kai kad'aine zaka rarrasheta tayi shuru kainedai ka kasa gane hakan. Mubinat ta maida kallonta gun ya atif,hannunsa ta janyo da sauri shikuwa yana biye da ita kamar k'aramin yaro har palo,sannan ta durk'usa agabansa tana cewa "tunda kasan da hakan pls ya atif kadakatar da aurenmu kace baka sona dan Allah ya atif kataimakeni?"
  Shima duk'usawa yayi cikin fiskan tausayi da damuwa gabad'aya ya canja kamar ba atif d'an gaye da aka saniba yana kallonta har cikin ido yace dazan iya danayi tuntuni sis mubee amma wlh bazan iyaba kiyi hak'uri sis mubee.
Kuka tafarayi tana dukansa ak'irjinsa tanacewa wlh zaka iya furtawa fa kawai zakayi dan Allah kaje ka gayawa abba cewa kapasa dan Allah ya atif? Sis mubee kekike ganinsa kawai amma bakina bazai iya furtawaba,ki amince dani zan rik'eki fiye da farhan zan k'aunaceki da nuna kulawa fiye dashi pls kibani dama my luv? Hannunta ya rik'o wanda take dukansa dasu d'in yana kissing nasu.
  Janye hannun tayi ta mik'e dagudu zuwa d'aki tana kuka,da sauri yabi bayanta amma tasa key sautin kukanta kawai akeji,koda ya duba agogon hannunsa saura 30minits d'aurin aurensu dan haka yafito yabarta...

KOMAI NISAN JIFADove le storie prendono vita. Scoprilo ora