🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺*©Pure Momment Of Life Writers*
We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.comWannan shafin nakine Aunty Sis💞nagode sosai da irin gudummawar da kika bani a wannan littafin nawa #KNJ, ALLAH ya saka miki da gidan Aljannar fiddausi ya albarkaci rayuwar sulti ya kuma saukeki lafiya ameen.
🌹🌷🌹🌷🌹🌷Page 53
Anyi awo na ukku bayan wata ukku inda suke zaune ana jiran jin saka mako
Daga Atif d'in har Mubeenat duk a tsorace suke dan sunsan wannan shine gwaji na k'arshe,musamman shi Atif da yake tunanin lokacin rabuwarsu da Mubeenat yazo kenan inhar bata dashi.
Doctor ya shigo fuskarsa d'auke da murmushi ya zauna tare da cewa "Alhamdulillah yanzu ma dai negative ya sake nuna mana,dan haka Mubeenat ta tsira."
Nanne hankalin Atif ya kwanta tare da cewa "Alhamdulillah! Doctor dama ana iya samun haka? Mutum na d'auke da k'wayar cutar k'anjamau yayi amfani da mace kuma ace ita bata d'auka ba?"
"Yes! Hakan yana faruwa amma in rare cases, shima idan dai amfani da macen bai wuce sau d'aya ba kamar dai irin case d'inku."
Doctor yaci gaba da cewa "Kasan wasu nada body immunity ( garkuwan jikin dake yak'i da hana k'wayoyin cututtuka shiga jikin D'an Adam) idan suna da tasiri da k'arfi suna hana k'wayoyin cututtuka shiga jikin D'an Adam musamman idan ana samun kyakkyawan abinci mai balance diet
Idan cuta tayi cuta ne tana shiga jikin D'an Adam shine har take iya karya garkuwan jiki saboda tun suna iya yak'i da cutar har tazo tafi k'arfinsu ta kashesu murus ta samu wajen zama."
"Haka kuma white blood cells (leukocyte) suma wani b'angare ne na immune system da ke taimakawa wajen yak'i da bak'in cututtuka da duk wani abu bak'o da zai shiga jikin D'an Adam, idan Allah yasa mutum nada body immune mai kyau da kuma wadataccen white blood cells da suke functioning sosai,cuta ko wacce iri ce tana da wahalar shiga jikin D'an Adam sai dai idan cutar ta dade ba'ayi maganinta ba shine har take cinyesu ta lalatasu sai ta samu gurbin zama."
"A case irin na Mubeenat Allah ya taimaketa sosai saboda body immune system d'inta is verry responsive and white blood cells d'inta lokacin da muka mata full blood count munga yana da yawa da lfy gashi kuma yana functioning yadda ya kamata"
"Amma kam da ka cigaba da amfani da ita da babu ablnda zai hanata d'auka, yanzu dai zamu ce Allah ya so Mubeenat da rahamarsa ya tsareta da tsarewarshi sai kasan matakin d'auka kafin ka kashe 'yar mutane."
Shuru Atif yayi ya kasa cewa komai sai kallon Mubeenat da yakeyi kamar zaiyi kuka saboda tausayawa kansa da yayi.
Ita ma hawayene cike a idanunta har yana zuba inda yayi saurin kai hannunsa ya share mata tare da mik'ewa yabar office d'in.
Cikin tausayawa ta kalli Doctor "Yanzu miye abinyi Doctor?"
"Mubeenat dah akwai wata hanya dana gaya muku,amma gaskiya babu"
"Mun gode Doctor" sannan ta goge k'wallanta ta wuce gurin Atif dake zaune a cikin mota yanata kuka kamar k'aramin yaro.
"Dan Allah Ya Atif ka dena please?"
"Nasan yadda kakeji a yanzu,nima kuma hakan nakeji har cikin raina dan Allah muje gida."
"Bazan iya driving ba a halin da nake ciki yanzu Sis Mubee,sai dai ki jamu yau"
Ganin gaskiyane maganarsa yasa ta zauna tare dajan motar batare data sake cewa komaiba ta maida hankalinta akan tuk'in dayake ba sabawa tayi ba.
Sun dad'e da isowa gida amma dukkansu zaune suke kamar wa'inda akayiwa rasuwa.
"Ya Atif kazo mu shiga ciki ka huta zuwa anjuma saika fito"
Shuru yayi baka jin komai sai sautin kukansa. "Dan Allah ka dena kukan nan Ya Atif,ya kake so inyi ne? Bari naje na kira Umma tunda bazaka dena ba"
Ko d'aga kansa baiyiba gaba d'aya ya zama abin tausayi alokaci guda.
Cikin muryan kuka take yiwa Umma magana "Umma dan Allah kizo kiyiwa Ya Atif magana tun a asibiti yaketa kuka har muka iso nan ko magana baya iya yi"
"Tome ya sameshi haka?"
"Umma gwaji ya tabbatar da cewa bana d'auke da irin cutarsa,duk damuwansa a yanzu shine bazai iya rabuwa dani ba,wlh Umma ina tausayawa Ya Atif har cikin zuciyata, tsoro nake kar k'aunar da yake min ya jefa shi cikin wani hali Umma" ta k'arashe maganar tana mai tsananta yin kukan ta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Umma ta furta tare da wucewa gun Atif "Atif dan Allah kayi hak'uri,ai ba akanka aka fara hakanba,sannan har a yanzu Mubeenat matar kace ku wuce ciki kuci abinci"
Idanunsa jawur yake kallon Umma tare da cewa "Umma dan Allah karku rabani da Sis Mubee wlh ita ce rayuwa ta bazan iya rayuwa babu ita ba dan Allah Umma"
Tausayin shine ya kama Umma "Atif Auren Mubeenat a hannunka yake ba'a hannunmu ba,kai kake da iko akanta fiye damu,dan haka ku shiga ciki har sai Abban ku ya dawo muji ta bakinsu."
Mubeenat ce taje kusa dashi ta rik'o hannunsa tana janshi da dukkan k'arfinta yana biye da ita, ita kuwa Umma k'wallan idanunta take gogewa yayin da motar Farhan ta shigo cikin gidan ya d'auko Shureim daga skul.
Tun daga nesa yake hango Umma tana share k'walla yayin da Mubeenat kuwa take jan hannun Atif tana hawaye shi kuwa yana biye da ita."Umma lafiya,me yake faruwa ne?"
"Su Atif ne yau sunje sun karb'o sakamakon gwajin da akayiwa Mubeenat, an tabbatar da bata d'auke da cutar ita"
"Hakan shiya d'aga musu hankali ita da Atif d'in,abun akwai tausayi wlh" tana kaiwa nan ta wuce Shureim yana biye da ita shi kuwa Farhan yana tsaye yama rasa me zaice...Voye and comment
Team #KNJ
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...