13

847 62 3
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

©Pure Momment Of Life Writers


Page 13
Assalamu alaikum 'yan'uwana mata,nice wadda kukafi sani da Hajiyan juyi. Nazo gidan radio ne badan komaiba sedan innemi gafararku daku da mazajenku akan zalincinku danayi.
Kamar yadda kowa yasan wacece ni ya kuma san sana'ata,tun bayan da wani d'an iska yayi tarayya dani na kamu da ciwo mai zafin gaske,kodanaje gun doctor se aka tabbatar min da cewa ina d'auke da cuta mai karya garkuwan jiki.
Hakan yasa na dakata da wannan sana'ar tawa,amma masu cuta irin tawa sukanzo muyi abinda muka saba.
Bayan nan nayi tafiya domin inje sayo kayayyakin da nake had'a maganin mata dashi,na kashe kud'i sama da dubu d'ari biyu da hamsin akan magungunan. Bayan na dawone daga tafiyan sena zauna domin had'a tsimina mai suna "yankan wuk'a".
Na gama had'a komai da komai acikinta,sena manta ban yanka d'aya daga cikin had'inba. Na d'auko wuk'a ina yankawa,sakamakon kaifin wuk'anne sena yanke tafin hannuna yanka sosai. Kan in mik'e daga inda nake jini yayi ta zuba acikin wannan had'in tsimin dake gabana,niwuma gaskiya bana jin zan iya zubar da wannan stimin dan kud'i mai yawa na zuba akansh,i gashi kuma gabad'aya na had'ashi babu ragowa. Sam banyi tunanin wannan d'an jinin nawa daya zuba a cikin tsimin zai haifar da matsalaba,sedana je na tsaftace hannuna dana yanken kafin nazo na k'arasa had'a tsumin. Shikanshi tsimin dama bak'i-bak'i yake kuma jaja-jaja,dan haka na zuba acikin robobi na ajiye akazo aka sayesu tas harma ana neman wasu saboda tsabar k'warewata awannan harkan.
Bayan na koma ganin doctor ne nake masa tambaya cikin dabara akan abinda ya faru da tsimina,doctor ya tabbatarmin dacewa lallai mutane zasu iya kamuwa da cutar danake d'auke da ita.
Tun daga wannan lokacin se hankalina ya tashi sosai nashiga damuwa fiye da tunanin mai sauraro,saboda mutane sama da dubu d'aya suke sayan kayan mata agurina,idan akace duk sun kamu da wannan cuta aina shiga uku,musammanma masu kishiyoyi. Kullum cikin kuka da damuwa nake, na zauna zaman jiran abinda zaije yadawo,wata uku na farajin k'ishin-k'ishin,kan in ankara naji anata zance mace ta kamu da cuta kuma batabin namiji,lokacin danaji aminaina suna wannan hiran,shikenan nasan lallai maganar doctor ya tabbata hakan yasa nazo gidan radio domin neman gafararku dan Allah kuyafemin ni Hajiyan juyi yau duniya ta juyoni gareku...
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" mutanen dake tsaye suna sauraran bayanin wannan yarinyar suketa maimaitawa.
Tacigaba da cewa "wannan shine abinda nama mijina,na halakashi na halaka kaina harma da sauran abokan zamana. Tir da mai hali irin nawa...
"Tabd'i" cewa Mubinat,amma gaskya baiwar Allah na tausaya miki,domin kind'auki alhakin 'yan'uwanki da mijinki. Ta dubi tarin matan dake tsaye agun duk jikinsu yayi sanyi dajin labarin.
Su kuwa mazajen cewa suke "Allah dai yasa matata bata d'aya daga cikinsu" sukaiwa mutumin jaje sannan suka wuce gida cikin sauri dansuje su d'ibi matansu zuwa asibiti. Atif ya dubi Mubinat wanda taketa bayani mamakine ya kamashi sosai,ganin ita dai yarinyace 'yar kimani shekara ashirin aduniya amma gata gaban manyan mata wasuma iyayentane tana musu bayani kamar wata malamarsu tana cewa...

"Haba 'yan'uwana dan Allah mudena yaudarar kanmu."
"Ina da wata k'awata mai suna Aisha Kabir,wata k'ila wasu daga cikinku sun santa,dan mahaifinta babban mutum ne agarinnan."
"Tare muke koda yaushe dani da ita da kuma Amal,Aisha ta aminta da maganin mata sosai tun muna 'yanmata komai aka bata sha takeyi. Munyi-munyi da Aisha tadena sha amma tak'i, ana aurenta saura wata uku Aisha tazo mana da wasu magunguna wai ance yana had'a mace ta matse sosai,mudai munk'i amincewa dashi kuma mun hanata amma tak'iji seda tayi amfani dashi. Dana matsi dana sha da kuma na tsarki duk tayi amfani dasu.
Kuma saya takeyi sosai sedai idan bataji ance ga sabon fitowaba.
Bayan bikin Aisha da wata biyu ta fara rashin lafiya,kowa tunaninsa ciki Aisha take d'auke dashi, amma da'akaje gun doctor seyace ba ciki bane kawai dai zazzab'ine,akayita jinya zazzab'i yak'i tafiya se'aka koma gun doctor. Bayan an gama dukkan bincikene se'aka gano cewa kansa ne da ita,kuma kansan agabanta yake. Ita kanta tayi mamakin abinda doctor yace,wlh tun daga lokacin Aisha tasa damuwa aranta ciwo yak'i warkewa,kuma tasanar da doctor cewa maganin matane take amfani dashi tun tana budurwa wanda muma shaidane akan hakan.
Intak'aice muku watan Aisha hud'u ad'akin mijinta Allah yayi mata rasuwa."
Mubinat ta tsaya da labarinta anan tana share k'walla tare da fad'in "Allah yajik'anki Aisha" mutanen dake gurin suka amsa da "Ameen"
Mubinat tacigaba dacewa "Meyasa muke yaudaran kanmune mata? Inba yaudaran kaiba kina budurwa meya kaiki amfani da maganin mata wai kina matsi dashi? Kuna tunanin akwai wani maganin mata da budurwa zatasha harya sake had'eta fiye da yadda Allah yayi mata halittanta? Haba 'ya'uwana! Wlh duk wanda yagaya miki wannan to babban mak'aryacine kuma mayaudari,dan duk mai ilimi da tunani wlh baza'a yaudaresa da ire-iren wad'annan abubuwaba. Gabad'ayan mata yanzu akan maganin mata suke cinye duk arzikinsu,basa iya yiwa kansu komai bare suma 'ya'yansu ko iyayensu dasuka haifesu. Kuma wlh maganin mata yanzu zanbane,watama kuka zata daka tasa citta da kanumfari indai yana kamshi shikenan a baki k'ullinsa naira d'ari ace kisha da madara zakiga aiki. Watama batasan me dame aka had'aba,amma duk se'ayita saya daga baya yazama miki illa arasa gane meyake damunki.
Dan Allah 'yan'uwana mata mufarka,mudena yadda ana cutar damu bayan muma muna da daman gyara kanmu da kanmu base munje gun wata ko wani ya mana k'arya ya cucemuba. Duk duniya babu abinda yake kawowa mace ni'ima irin kwanciyan hankali,kai ba mace kad'aiba hatta namiji,duk wacce bata yaddaba to dan Allah kizaunar da mijinki kitambayeshi natabbata zaki yarda da maganata. Duk macen ko namijin da bashi da kwanciyan hankali todole kisamesu da k'arancin ni'ima wlh.
Bawai nace ku dena amfani da maganin matabane,ina nufin ki had'ashi da hannunki wanda kekinsan abinda kika harhad'a acikinsa bawai kije ki sayi fitina da kud'inkiba kizo kina ciza yatsa daga baya. Inda zakuci gaba da biyoni,to  zakuji irin abubuwan dake k'arawa mace ni'ima da kuma d'and'ano...
Atif ne yayi saurin shigowa gefen matan,dan gabad'aya an zagaye Mubinat ana jin bayaninta mai d'auke da darusa iri-iri ya kamo hannunta tare da cewa"Kuyi hak'uri,lokacin tafiyanmu yayi"
Muryan mata kake jiyowa ana cewa "Dan Allah kad'an k'ara mana minti goma bawan Allah"
Amma ina,baima tsaya sauraransuba,janta yake daga k'arshema d'aukanta yayi cak har cikin mota. Mutane se binsu da ido akeyi yayinda wasu suke cewa "Ai dole ya d'agata,irin wannan bayani nata aima yaci ace ya goyata wlh,k'aramar yarinya da basira haka."
Suna tayi dai wasu samarai kuwa cewa suke ai itace matar Atif Muhammad Bakari d'an wasan k'wallonnan ai d'an uwantane, dabashi zata auraba ai wani balarabene mai suna Farhan,sakamakon accident dayayine yayi losing memory d'inshi shine aka had'ata da Atif d'in.
Wani daga gefe yace "short up duk bakusan komaiba,accident d'in Farhan d'in ai abune shiryayye,kuma se Allah ya kaddara hakan zai faru dashi,mubar wannan zancen tunda bai shafemuba danni wlh Atif d'in burgeni yakeyi Allah,akwai iya short d'in ball."
Eh wlh gaskiya nima gayen yana kaimin,infa ball ya shiga hannunsa toseya cinyesu kamar maye wlh. Hakadai sukaita hiransu sannan suka wuce...

"Meyasa ka janyoni bangama maganaba Ya Atif?"
"Saboda maza sunyi yawa kuma duksun tsaya sauraran bayanankine kuma suna kalle min ke wanda hakan yasa naji kishi sosai acikin raina."
"Hhhh kai Ya Atif har wani kishi kakeyi akaina?"
"Hmm bazaki tab'a ganewa bane Sis Mubi,i love you more than you'r thinking" ya fad'a tare da maida kansa kan driving kamar mai yin tunanin wani abu.
Kallonshi taketayi tare da shafar sajen fiskarsa da hannunta tace "Are you thinking of something?"
"Yes" yace da ita
"Tell me,menene?"
"Matso da kunnenki kiji"
Bamusu ta matso dashi tana sauraronsa.
"Ina tunanin irin kukan dazakiyi yaune" ya rad'a mata tare da cizan kunnen nata ahankali yana mata dariya mai had'e da zolaya...

Vote and comment k'awayena,hakan yana sani jin dad'i da farinciki...

                                   Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAWhere stories live. Discover now