KOMAI NISAN JIFA
by maman shureim
sad-nasPage 17
A hankali Farhan ya tuna da kalmar daya furta daga bakinsa,wanda yasan hakan shiyasa kowa dake gun kallonsa.
Cikin sauri da farin ciki Mubinat ta tashi daga jikin Atif tana kallon Farhan ko k'yafta ido batayi,shi kuwa Atif ita da Farhan yake bi da kallo cikin tashi hankali.
"Farhan,Alhamdulillahi memory naka ya dawo" Abba ya fad'a cikin farin ciki.
A hankali Farhan ya rufe idanun sa tare da rik'e kansa yana motsi da leb'en bakinsa,ko ba'a fad'aba kowa yasan addu'a yakeyi.
Dan kar Abba ya zargi wani abune se Ahmad yace "Farhan,kai masha Allah,Alhamdulillah, abokina yanzu ka samu lafiya completely" yana dariya tare da dafa kafad'ar Farhan d'in.
Shureim da aka barsu a cikin mota se faman buga glass d'in mota yakeyi. Hakan yasa Farhan ya maida hankalin sa gun motan,cikin sauri ya kalli Mubinat dake tsaye a gabansa tana murmushin farin ciki. "Akwai key acikin aljihun jikinki kozan samu?" Cewar Farhan.
Hannu tasa ta d'auko sannan ta mik'a mishi,cikin hanzari yaje ya bud'e su.
"Ya Farhan meya sameka naga bayanka da jini?"
"Karka damu Shureim,d'an rauni na samu ba wani ciwo bane sosai"
Da sauri suka fito shida Musa suka k'araso gun, Shureim ya rungume Mubinat yana cewa "Sis Mubee babu abinda ya sameki ko? Ya naga kayan Ya Farhan a jikinki sannan shi na ganshi haka, ina kayanki?"
Farhan ne ya shafi kansa,tare da muntsinin kunnen sa alamun yayi shuri.
Abba yace "Yanzu dai dukku dakata,muje gida gaba d'ayanmu."
Ba musu Farhan ya kamo hannun Shureim da Musa suka koma motarsu,shi kuma Ahmad yace wa wanda suke tare kaje kawai,nizan kai Abba gida zamuyi waya.
Bayan shima ya tafine,Ahmad yaja motar Abba sukayi gaba. Mubinat tana tsaye tana binsu Farhan da kallo yayin da duk wani b'ak'in cikinta ya sauya zuwa farin ciki. Jin motsin Atif da tayi ne a kusa da ita yasa ta juya suka kalli juna, gaba d'aya jikinsa a mace wucewa tayi zuwa motarsa sannan ya bita a baya.
Shureim se dariya yakeyi wai "Ya Farhan kalli inda Sis Mubee take yawo a cikin kayan ka"
Farhan baisan lokacin dayayi dariya ba hakama Musa almajiri. Seda yaga tafiyar su sannan yabi bayansu zuciyarsa cike da tunani iri daban-daban.Bayan isarsu gidane Farhan ya kira Ahmad a waya,ba jimawa yazo gun motan,Farhan ya sanar dashi cewa yaje ya kawo mishi shrit da wando a d'aki. Bayan ya kawo mishi ne seya sa a cikin motan, dan bazai iya fita a haka ba ganin taron mutanen dake tsaye a harabar gidan.
Farhan yayi magana da Ahmad a sirrance, kan cewa karya sanar dasu Abba cewan an kama wani, koda Ahmad yaso jin dalilin hakan amma bai samu amsa daga gun Farhan ba.
Umma da Mum d'in Atif da Amal da Aisha, kai kusan duk dangin su Mubinat sun samu labarin abinda ya faru, dan haka suna tsaye a tsakar gida corko-corko.
Suna isa Mubinat taje aguje ta rungume Ummanta tana kuka. Ita kanta Umma seda tayi kwalla. Mum d'in Atif ne tazo kusa da ita tace "Allah sarki Mubinat d'ita Allah ya kiyaye na gaba,Allah ya toni asirinsu,kai Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu,wlh tashin hankali baiyiba."
Umma tace "Wlh ki bari kawai Allah ya kiyaye kawai su kuma masu irin wannan halin Allah ya shirye su." Aka amsa sa ameen. Cikin jin kunya Mubinat ta kalli su Amal tare dayi musu magana da ido akan su tafi ciki.
Amal ce tace "Sannu Mubee muje ki sauya kayan jikinki" a silale ta wuce suna biye da ita.
Su Abba kuwa parlour suka wuce dukkan ninsu,inda Mahaifin Atif ma ya iso suka wuce a tare.Dad d'in su Atif ne yace "Aise a tsaura bincike domin baza'abar maganan haka nan ba,dole abi diddigi musan wanda ya turosu. Ahmad yayi magana "Eh dama muma muna kan binciken kenan insha Allahu za'ayi nasara. Atif kuwa yana zaune rai a b'ace zuciyarsa se tafasa takeyi.
Abba yace "To Bayan wannan kuma akwai wani albishir dazan sanar daku a yanzu."
Dad d'in Atif ne yace "To muna sauraro"
Abba yace "Alokacin da Mamana take gudu akan titi wanda saura kad'an mota ya bugeta anan Farhan ya samu lafiya,ma'ana wannan had'arin da aka kusa yine ya dawo masa da momory nashi,yanzu lafiyan sa k'alau sedai muyiwa Allah godiya." Nan parlour ya hargitse da murna anata addu'oi sosai kowa yana nuna farin cikin sa. Abba yaci gaba da cewa "Farhan nasan kana sane da cewa Mamana tayi aure kuma Atif take aure?" Cikin sanyin murya Farhan yace "Eh Abba"
Abba yaci gaba da cewa "To inaso kayi hak'uri kad'au k'addara dama can Mamana ba matarka bace,sannan dan Allah ku cire komai aranku dukkanku biyun musam man kai Atif, gaskiya banji dad'in abinda kukayiba wlh, duk ku d'in d'ayane aguna dan haka ku kula dan Allah."
"Kayi hak'uri Abba,sharrin zuciya ce insha Allah hakan bazai sake faruwa ba." Cewar Atif sannan ya kalli Farhan yace "Farhan kayi hak'uri,nayi kuskure."
"Bakomai wlh ya wuce sannan ya kalli Abba, Abba kayi hak'uri munyi kuskure." Cewar Farhan
Abba yace "To Alhamdulillahi Allah ya muku albarka" Suka amsa da ameen. Nanma Dad d'in Atif ya sake musu nasiha tare da sake baiwa Farhan hak'uri akan rasa Mubinat dayayi.
"Ka shirya semu je gun Doctor ya dubaka" cewar Abba.
"To" Farhan yace, sannan suka mik'e dukkansu ukun zuwa shashin su.Mubinat ce zaune suna hira dasu Amal bayan tayi wanka ta canja kaya. Dama da kayanta a gida sunkai kala takwas. Sunci abinci sun k'oshine take basu labarin yadda mutanen nan suka mata. Mamaki sosai sukayi,sannan sukayi musu addu'an shiriya dan bai kamata ayi musu bakiba sedai a nema musu shiriya a gurin Allah.
Mubinat taci gaba da cewa "Ya Farhan ya dawo hayyacinsa yanzu yana sane da komai,inama da ace Abi d'insa yana k'asar, nasan zaifi kowa farin ciki dajin wannan labarin amma fa bazai kainiba."
Amal da Aisha se binta suke da kallo suna tayata murna. Acikin ransu kuwa cewa suke akwai aiki. Hira sukai sosai, mak'ota se shigo musu sukeyi ana tayasu barkan dawowan Mubinat.Bayan sallan la'asar Shureim yazo inda suke zaune yace "Sis Mubee wai kifito ku tafi"
Badan taso ba haka ta mik'e suka fito duk kansu, taso ace sunyi magana ita da Farhan amma hakan baiyu ba. Tayi ta dube-dube ko zata ganshi amma sam babu alaman sa agun, kallon Shureim tayi tare da kiransa da hannunta "Ina Ya Farhan,kodai sun fita ne?" Ta tambaye shi.
"A'a Ya Ahmad ne kawai ya tafi, Ya Farhan yana bacci bayan ya gama k'wallan rasaki dayayi."
Hankali Mubinat yayi matuk'ar tashi sosai,ji take kamar taje d'akin nashi danta ganshi,amma seta shige cikin mota kamar wanda ruwa ya dake ta. Su Aisha dai basu ce komaiba se ido da suke binta dashi.
Seda Atif ya shigo motar ne su Amal sukace "Zamu zo jibi ki hada mana beta"
"To sekun zo" ta fad'a cikin sanyin murya sannan Atif yaja motarsa suka tafi.Tun a hanya ya lura da yanayin ta. Tunani yakeyi cikin zuciyarsa "Sis Mubee zata canja min kenan tunda har tasan Farhan ya samu lafiya yanzu, dole inyi saurin yin tarayya da Mubee inaga yin hakan shi zaisa ta saki jiki dani harma ta mance da Farhan muddin d'ana ya shiga jikinta."
A hankali ya rik'o hannunta tare dayin magana cikin sanyin murya "Sis Mubee, are you alright?"
Shuru tayi bata ce komai ba,ya sake cewa "I'm sorry for what happen,dan Allah ki mance dashi a zuciyarki shaid'an ne da kuma kishin yadda nazo na ganki babu sutura a jikinki."
Hannunta ta janye daga nashi tace "Ya wuce bakomai."
Bai sake ce mata komaiba har suka isa gida.Lokacin baccin su kuwa tana kwance shuru bai shigo ba. Se taji sallamarsa da ledoji cike a hannunsa wanda yasha sayayya iri-iri.
Kayan jikinsa ya cire ya wuce toilet. Babu jimawa ya fito yasa jallabiya yace "Taso muyi sallah"
"Nayi" tace dashi
"Ina nufin muyi nafila"
Mik'ewa tayi tasa himar dama doguwar riga ce a jikin ta.
Bayan sun idar ne yace"Sis Mubee ina fatan yau zan samu had'in kanki a matsayina na mijin ki?"
Mik'ewa tayi ta wuce zuwa d'ayan d'akin da gudu tana kuka.
Tashi yayi ya cire rigan jikinsa ya fesa turare sannan ya bita, k'ofar a bud'e ya jita dan haka ya shige kai tsaye tana kwance akan gadonsa tana kuka.
"Dan Allah karka tab'ani Ya Atif" ta fad'a cikin muryan kuka.
"Me yasa zakice haka Sis Mubee,kin manta yaune alk'awarin mu,me yasa zaki karya min alk'awari bayan na gama sa raina,kinaga kinmin adalci kenan idan kika min hakan?"
Kuka sosai takeyi tana girgiza kanta "Dan Allah kayi hak'uri"
Kanshi ya shafa da hannunsa yayi magana cikin b'acin rai "Bazai yuba Sis Mubee,yau zaki bani hakkina indai ni Mijinki ne...!Vote and comment mana
Team #KNJ
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...