🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺*©Pure Momment Of Life Writers*
We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤Page 39
"Mubeenat"
"Na'am Uncle"
"Zoki zuba mana abincin ko?"
"To Uncle" sannan ta zuba mishi shida Ummi da Kakansu,Farhan suna binta da kallo daga nan suka wuce ciki.
Hira sosai Mubeenat sukeyi da Iyayen Farhan,ta saki jiki dasu sosai ganin yadda suke sonta.
Farhan ne ya fito da waya a hannunsa "Abbi"
"Yes Son"
"Kasa a kawo maka motan ne?"
"Na'aam suna kawowa,zakuje wani guri ne?"
"Abbi ina son mota ne dan zamu fita da Atif anjima domin muga guraren"
"Ok Son bari idan an kawo min motan seku fita kaima ka sayi naka ko?"
"Ok"
"Ya Farhan mota zaka saya?"
"Yeah,ko kina saida motan ne?" Ya tambayeta cikin zolaya.
Dariya tayi "A'a akwai dai wanda Abba yake saya agunsu ne zanso ka saya agunsu suna da kirki sosai"
"Ok kinsan gurin?"
"A'a but Ya Atif ya sani,nidai ban tab'a zuwa ba sedai su sukan kawowa Abba mota har gida indan zai saya"
"Ok zanyiwa Atif magana se muje"
"Ok thanks"
"You'r wlcum" sannan ya kalli Ummin shi tare da kashe mata ido d'aya yana murmushi.
"Habibi ta'ali"
Dawowa yayi yace "Im here Ummi"
"Zauna anan" ta nuna mishi kujeran dake kusa da Mubeenat.
Bayan ya zauna ne seya ajiye wayarsa,idon Mubeenat yakai kan screen nashi inda taga hoton sane yana sanye da shert yellow mai dogon hannu tare da wata yarinya tana sanye da pink d'in top da kuma bak'in suwaita akai sunyi kyau sosai musamman shi Farhan d'in.
"Ya Farhan zan iya yin tambaya?"
"Sure!"
"Kaida waye a hoton nan?"
Wayarsa ya kalla sannan yayi murmushi "She's my Sister k'anwar Abdullahi ce"
"Tamin kyau sosai"
Murmushi yayi tare da cewa "Thanks" yana mai kallon fuskarta se kallon hoton takeyi.
"Zan had'aku k'awance kina so?"
"Da ni?"
"Yeah indai kina so"
"To nagode" tana murmushi baisan yana binta da kallo har haka ba seda Ummin shi tace "Habibi"
Sannan ya cire idanunsa akan Mubeenat wanda ita kamma bata san yanayi ba.
"Na'aam Ummi"
"You are my Habibi,and she's my Habibty" cewar Ummi
Kallon Ummin nashi yayi cikin mamaki,ita kanta Mubeenat wani irin kunya taji dan tasan Habibty dai masoyiya ne.
Farhan ya kalli Mubeenat yace "Habibty?"
Itama kallonsa takeyi tare da saurin sauke idanunta zuwa k'asa.
"Yes Habibi,i love her so much"
Abbi ne yayi gyaran murya "Kunfa takura min Yarinya,kun sata jin kunya,Mubeenat tashi ki shiga ciki kinji?"
Kamar tana jira dama ta mik'e cikin sauri ta wuce d'akin Ummi dan anan Ummi ta ajiye mata kayanta.Bayan maganganu da sukayi da d'ansu Farhan ne sannan ya wuce gun Abdullahi a d'aki suna hira.
Bayan la'asar aka kawowa Abbi motar. Take Farhan yayiwa Atif waya yazo suka wuce dukkansu ba tare da Mubeenat tasan da zuwan Atif ba dan tana bacci a d'akin Ummi.
A hanya Farhan yake gayawa Atif maganar mota da Mubeenat ta mishi.
"Yeah muje gurin to"
Suna isa Farhan ya zab'i mota Camry 2015 ash colour had'ad'd'iya.
Ahmad ne yau ke zaune agidan motocin dan Yayansa baya nan ya wuce Umrah shiyasa yabar komai a hannu Ahmad d'in.
"Amma dai kai bak'o ne ko?" Cewar Atif
Ahmad yayi murmushi yace "Eh dayake bamu tab'a had'uwa ba,ni k'anin Lukman ne baya gari shiyasa na zauna anan d'in"
"Ok,toga d'an uwana sunan shi Farhan daga Madina suka zo kuma zaici gaba da zama anan ne baisan kowa ba dai a yanzu da fatan zaku zama friends?"
"Allah sarki,why note? Nice to meet you Farahan" cewar Ahmad tare da sake mik'a mishi hannu.
"Thankyou Ahmad" sannan sukayi exchenging number yayi mishi mobile transfer na kud'in motar sannan aka rubuta komai na motar aka basu suka tafi suna godiya.
Abdullahi ne ya hau sabuwar motar Atif da Farhan kuwa suna mota d'aya Abdullahi yana binsu a baya.
Yawo sosai sukayi yana nuna musu gurare har kusan magrib kafin suka dawo gida.
Lokacin Mubeenat ta gama musu abincin dare har tayi wanka sannan suka dawo.
Gaba d'ayansu suka fito domin ganin motar Farhan,nan sukaita mishi addu'a sannan suka koma ciki seda Atif yaci abinci suka tab'a d'an hira da Mubeenat kafin ya wuce gida.
8:45 Mubeenat ta shige d'akin Ummi ta kwanta akan gadonta suna chartn da Amal da Aisha tanata murmushi.
"Slm" taji sallamar Farhan
"Waslm" ta amsa tare da mik'ewa taje ta bud'e mishi k'ofar "Ya Farhan?"
"Na'am bacci zakiyi?"
"Eh" ta bashi amsa
"Ok then ma'assalam"
"Murmushi tayi tace Bissalam" sannan ya tafi.
"Ummi bacci fa zatayi"
"To shikenan dama naga ita kad'ai ce shiyasa nace ka dubo ta"
Haka sukaita hiransu cikin harcen larabci tana jiyosu har bacci yayi gaba da ita.
Washe gari da safe bayan anyi sallah ta shige kishi ta had'a musu d'anwake dake Abbi ya sanar da ita cewa suna son duk wani abu daya shafi flour.Gidan su Amal kuwa tunda Ummanta ta tashi bata ganewa jikin taba sakamakon mugayen aljanu da suka shiga jikinta nan take ta kira Amal.
"Gani Umma"
"Kije ki kiramin Umman Mubeenat"
"To" sannan ta fita tare da tunanin meya faru Umma zata aikeni da sassafe haka?"
Fitar Amal kenan itama Umman nata tasa k'afa ta fito,Mai gadi yayi mamakin ganinta ta fita da safe haka amma seya gaishe ta "Ina kwana hajiya?"
"Lafiya" kawai tace dashi sannan ta wuce ta kama hanya ba tare data san inda take dosa ba.
Wannan shine silar barin Umman Amal daga wannan gidan wanda har yanzu ba'asan inda takeba tsawon shekara biyu kenan yanzu.
Ita kanta Umman Mubeenat hankalinta a tashe ganin safiya ce kuma Amal tace Ummanta na kiranta,bayan ta sanar da Abban Mubeenat ne se suka wuce ita da Amal d'in.
Koda Amal ta shiga se bata ga Ummanta ba,ta kirata taji shuru,ta duba ko ina shuru saita wuce d'akin Babanta nanma yace da ita bata shigo ba.
Abu kamar wasa su Samira da Umman Mubeenat anata nemanta can mai gadi yace aita fita.
"Ta fita kuma? Amma aini bata gayamin zata fita ba" cewar Abban Amal.
Nanne hankalin kowa ya tashi amma banda Samira da Sagir da suka san abinda suka aikata wanda se murna suke acikin zuciyar su.
_ALLAH KA SHIGA TSAKANIN NA GARI DA MUGU,MASU HALI IRIN NA SAMIRA DA SAGIR ALLAH KA SHIRYAR DASU KASA MUFI K'ARFIN ZUCIYOYINNU AMEEN._
Abu kamar wasa aka kira wayanta se akaji yana ringing a cikin d'akinta,duk inda ake tunanin zataje duk an tambaya amma babu alamunta.
Take Amal ta fashe da kuka Samira tazo kusa da ita zata rarrasheta cikin sauri da kallon banza ta wuce gun Umman Mubeenat tana kuka sosai mai k'arfi.
Abban Mubeenat ne yace Umma ta shiga da ita gida bari su shiga cikin gari,nan suka fita shida Aban Amal d'in Atif ma yabi bayansu da motar shi se nemanta ake abu kamar a film mutum da girmansa anemeshi a rasa...Voye and comment
Team #KNJ
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...