🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺©Pure Momment Of Life Writers
Page 7
Bayan Atif ya dawone yake gayawa Mubinat cewa ta shirya dan gobe zasu wuce abuja. Marairaicewa tayi tace "gobe kuma,mezamuje muyi acan d'in?"
"Hutawa mana sis mubinat,kinsan fa ni angone ina so muje yawone kinji?"
Kallonsa tayi cikin shagwab'a "pls mubari se wani sati kagafa ko gurinsu mum bamujeba kuma ina so ind'an k'ara samun lfy kafin muyi tfy pls Ya atif."
Ganin yadda take mishi shagwab'ane yasa ya amince da cewa "Ok naji,but wani satin bazan sake k'arb'an wani escuse nakiba agree?"
"Yes no"
"Hhhh" yayi dariya tare da rungumeta yace you don't stard ba?"
"Hahah nop I'm just kidding you" tare da rungumesa tana tuna farhan...Haka dai rayuwarsu taci gaba da kasancewa babu wani damuwa. Alk'awarinsu yananan kamar dai yadda suka amincewa junansu.
Ta hakanne mubinat take moransa sosai,ga wani sabon k'aunarta dayake shigansa fiye dana da.
Aduk lokacin data buk'aci yin magana da Ya farhan Sam baya Janata,hakan yasa tasake dashi sosai dama kuma can akwai k'auna atsakaninsu.
Duk cikin yayyunta tafi son Ya atif kodon gida d'aya suke zama oho.
Yanzu kam da kanta take musu girki kala kala masu dad'i,daga ita harshi sun fara kyan gani dan hankalinsu akwance yake.Ta b'angaren farhan kuwa sauk'in shine mahaifiyarsa,yana matuk'ar son mahaifiyar saboda k'auna da take nuna masa. Cikin ikon Allah ya fara samun sauk'i,amma k'aunar da yakeyiwa Sis mubinat yananan acikin zuciyarsa wanda shikam se'a hankali zai fita.
Ganin kamar ya fara mancewa da itane yasa wan mahaifiyarsa yayi masa magana akan wata yarinya acan d'in kozai aureta.
"Farhan baya iya b'oye abu kokuma wani nuk'u-nuk'u,dan haka ya gayawa uncle nasa cewa gaskya hakan bazaiyuba amishi hak'uri."
Tun daga wannan rana babu wanda yasake mishi magana akan aure...Can gida Nigeria kuwa su Atif yau suke hangar tafiya abuja.
Dake flight sukabi basu sha wahalan hanyaba. Abokansa dake canne d'aya daga cikinsu wato Nazir,shiyaje ya d'aukosu yakaisu d'aya daga cikin gidajensa da babu kowa aciki yakaisu.
Shidai Nazir sana'an gidaje yakeyi da kuma bada haya,dan shinema ya hana Atif sauka a hotel.
Gidane flat hud'u acikinsa,ukun da mutane aciki,d'ayan kuma babu kowa dama sabbin gidajene. Atif yace tofa guy ka kama k'asafa,murmushi yayi tare da cewa "aiban kaikaba ango suna dariya tare da shigewa ciki.
Komai dai Sabone aciki, kuma awadace 2bedroom ne se parlour da raining dakuma kichine.
Nazir bai zaunaba yace"barinaje gida zamu taho da sweetheart dan girki na musamman tayi muku wlh."
Bayan tafiyarsane Atif ya shiga musu da kayansu sannan ya rik'o hannunta tare da fiskantarta yace "gurin ya miki,kodai mutafi hotel?"
Murmushi cike da fiskanta tace "yayi,kuma kaga ga mutane agidan zan samu k'awayen hira."
"Are you sure'bana so kitakura jus tell me the truth" yana shafar firkarta
"I'm serious wlh nan d'in yayi thankyou, ta rungumesa"
Dad'in hakan yaji ya d'agata sama zuwa d'akinsu tana dariya. Akan gado ya direta sannan tace bari nayi wanka,murmushi yayi yace to idan kin fito Nima sena shiga.
Nazir ne da matarsa da kuma 'yarsu d'aya mai suna Kismat. Idan ka gansu atare dole su burgeka,ga kyakkyawar babynsu kismat 'yar kimanin shekaru biyar.
Hira sosai sukayi cikin hara dajin dad'i har 3:00pm kafin sukai sallama suka tafi.
Bayan isha Nazir da abokinsa sukazo da Mota biyu,d'ayan sun kawowa Atif ne dan zaga gari shida Mubinat sannan suka koma a d'ayan.Haka sukaci gabada zama a abuja har tsawon sati d'aya,sunyi yawo sosai ga kuma matan abokan Atif Sunada kirki sosai. Hakan yasa suka shak'u kamar sunyi shekaru tare.
Suma matan da suke zaune a gida d'aya da mubinat d'in suna da kirki sosai ba laifi,Soyayya sosai sukeyi da mazajensu Dan dukkansu amarene.
Hakan yasa wani lokaci Atif yake sa damuwa aransa. Dan wani soyayyanma agabansu akeyi akan idanunsu wanda hakan baisa ya karya alk'awarin dayayiwa mubinat ba,sedai wani lokaci yana tsintar kanshi cikin tunani ko kuma ince damuwa.Wata rana mubinat tayi wanka cikin english wears riga da wando,rigar hannu d'ayane kawai gata ja. Kyau sosai tayi yayinda tayi parking gashinta a tsakiyar kai.
Tunda Atif yadawo idanunsa na kanta ya kasa d'auke kai,ahankali yabita kichine inda take yanka musu fruit tana wak'an *Umar m sharif* abakinta.
West nata ya rik'o yayinda ta razana sosai dan batasan yashigo kichine d'inba. Bayan ya juyo da itane suna kallon junansu wanda hakan yasa taji tsoronsa dan duk kamanninsa ya sauya idanunsa sun k'ank'ance
Magana yake cikin murya mai kashe jiki yanacewa
"You look beautiful in this dress"
Cikin rawan murya tace "thanks"
"What's is going on sis mubinat,I won't do anything I promise okay"
"Silent"
"Why are you quite, say something"
"Please stop it Ya atif" ta furta dai-dai lokacin da yake neman wuce gona da iri.
Mubinat bataga alaman zai bariba dan haka ta tureshi gefe da k'arfi tana hawaye "pls stop it"
Ajiyar zuciya ya sauk'e amma sam baiji dad'in hakanba acikin ranshi, baice da ita komaiba yabar kichine d'in. Da Sauri ta biyo bayanshi danta lura da yanayinsa na rashin jin dad'in abinda tayi mishi. Yana zaune a parlour rufe da idanunsa ta k'arasa gurin ta zauna kusa dashi tare da sunkuyar da kanta k'asa tace "i'm sorry"
"Silent"
Kanta ta d'ago tana kallonsa cikin nadama ta sake cewa "Ya atif i'm sorry please"tare da rik'o yatsun hannunsa tana wasa dasu.
Hannunsa ya janye tare da mik'ewa ya wuce d'aki batare dayace mata komaiba. Jiki sanyaye tabi bayanshi tana zubar da kwalla.
Kayan jikinsa yake cirewa,gabansa taje ta tsaya tana share kwalla sannan ta sake cewa "Ya atif i'm sorry tsorone ya kamani shiyasa nayi haka..."Tsoro fa kikace,wani irin tsoro kenan sis mubunat,i am your husband yakama kisa hakan aranki kidena guduna pls it's really hurt can't you understand!"
"And ki duba irin shigar da kikayi yanzu,kuma kina expecting inyi ignoring d'inki?"
"Kina ganin kinmin adalci kenan sis mubinat?"
"Nifa mutum ne d'an adam mai lafiya ajikinshi kika kafa min dokanki nakuma amince miki amma kuma shine zaki tayarmin da hankali kuma kice zan iya jurewa kinaga bakiso kanki sosaiba sis mubinat?"
Tunda ya fara magana take kuka dan yadda taga ranshi ya b'aci yana magana cikin fushi harse daya gama sannan tace "kayi hak'uri dan Allah bazan sakeba" kota kanta baibiba ya wuce d'ayan d'akin ya kwanta abinsa rai ab'ace.
Koda mubinat tabi bayansa amma setaji k'ofar arufe. Bugawa take tana cewa "pls open the door Ya atif I don't mean to hurt you wlh bazan sakeba pls karkayi fushi dani."
"Ya atif please open the door"
"Just leave me along sis mubi"
"Please stop saying that, hakan yana nufin kayi fushi danine kenan?"
"Banyi fushiba kawai ina son kasancewa ni kad'aine"
"Dan Allah karkamin haka Ya atif kazo muje mu kwanta,kasan kariga daka sabar min yin bacci tare dakai i'm sorry please...Vote and comment please
Team #KNJ#
BINABASA MO ANG
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...