🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺*©Pure Momment Of Life Writers*
We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤NOTE
Assalamu Alaikum masoyan littafina,ina mai baku hak'uri akan ra'ayoyinku da nakeji na mukoma zuwa cigaban labarin. To zanyi iya bakin k'ok'arina dan inga na tsinto muku abubuwan da suka dace ta yadda idan mun cigaba da labarin zaku faminci komai insha Allah.
Daga k'arshe na gode da soyayyarku agareni Allah ya barmu tare ameen...❤❤❤Page 44
Tun daga wannan ranan Mubeenat take jin kunyar Ya Farhan,musamman ma dataga alamunsa akanta.
Yaune Abba da Farhan sukaje ismaliyya aka gama komai an d'auki Farhan Malami a wannan islamiyya dan wani sati za'a koma,Shureim se murna yakeyi zai dinga bin Farhan a mota.
Atif kuwa satinsu biyu sannan suka dawo,daga shi har Mubeenat sunyi kewar junansu sosai dukda dai kusan kullum suna manne a waya kamar saurayi da budurwa,shiyasama daya dawo har Farhan ya fara tunanin kodai akwai soyayya a tsakaninsu ne amma se daga baya ya fahimci cewa shak'uwace kawai wanda hakan ya burgeshi sosai.
Tunda Atif ya dawo mubeenat bata samun baiwa Farhan lokacinta kamar daba,dan kusan kullum suna fita yawo koma gidan friends nata lokacin da Atif baya nan Farhan shine mai kaita ko ina amma banda yanzu da Atif ya dawo komai ya sauya.
Haka dai rayuwarsu taci gaba har tsawon shekara d'aya.*~~~~~~*
Alokacin Farhan ya zama cikakken d'an k'asa dan kusan ko ina ya sani gashi shak'uwarsu da Mubeenat ya k'aru sosai wanda shi sam baya so tayi nesa dashi.
Ko a office ne minti d'aya biyu zai kirata dayake ita da Amal acan suke aiki tare dashi,duk wata suna da albashinsu 30k ta hakanne suke hidimarsu sosai basu rasa komaiba dama kuma Abban Mubeenat komai zaiyiwa Mubeenat to ita da Amal yake had'awa duk dan ta kwantar da hankalinta na rashin Mahaifiyarta da har yanzu ba'a san inda take ba.Shureim yana zaune yana tuna tambayoyin da Farhan yayi mishi akan Mubeenat na tana da saurayin da take so ne?
"Meyasa Ya Farhan yamin wannan tambayar kodai son Sis Mubee yakeyi ne kuma yana kunyar sanar da ita? Indai hakane nasan abinda zanyi dan wlh bazan bari Ya Farhan ya saurari wannan 'yan matan islamiyyan namuba wanda suke had'oni da wasik'a gurin Ya Farhan."
Parlour'n Umma ya nufa yaga Sis Mubee kwance tana bacci dan haka ya koma d'akin Ya Farhan ya d'auko hotonsa guda d'aya yazo ya d'aga hannun Mubeenat a hankali yasa hoton akan cikinta sannan ya mayar da hannun nata ya koma d'akin Farhan da sauri ya kwanta yana game a laptop nashi.
Bayan minti talatin sega Farhan ya dawo gida,kai tsaye parlour'n Umma ya nufa da niyan ya gaisheta da gida sannan ya wuce.
Mubeenat ya gani kwance tana bacci tare da farin abu akan cikinta,haka kawai yaji yana son ganin menene wannan abun. Na baku labarin gurinnan a baya dan haka zanci gaba daga inda ya koma d'aki rik'e da hoton a hannunsa yana tambayar Shureim ya akayi Sis Mubeenat ta samu hotona?
"Ya Farhan kasan tana zuwa gyara maka d'aki watak'ila anan tagani ta d'auka."
Murmushi Farhan yayi tare da rage kayan jikinsa ya wuce toilet yana tunanin "Kodai itama Sis Mubeenat ta kamu da soyayyata ne?"Dama Farhan ya gayawa Abbi da Umminsa cewa yana son Habibty kamar yadda suke sonshi da ita tun a baya,amma ya sanar da Abbi nashi cewar karya gayawa Abba shi da kanshi zai nemi izini agun Abba kafinma ya sanar da ita Mubeenat d'in.
Murna sosai sukayi da har Farhan ya aminta da Mubeenat dan kanshi,dan haka sukaci gaba dayi musu addu'an alkhairi.
Bayan sallan isha Farhan yaje gun Abba a parlour sund'an tab'a hirane sannan yace "Abba dama nazo ne da wata buk'ata nawa"
"To Farhan ina jinka"
Cikin girmamawa ya sunkuyar da kansa ya fara magana cikin jin kunya "Abba dama ina so in nemi izini agunka ne akan Sis Mubeenat,indai ba'a riga da an amsawa waniba ina so inje mata da buk'atata inhar ka amince min?"
"Alhamdulillah" Abba ya fad'a acikin zuciyarsa,a fili kuma yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace "Toba komai Farhan na maka izini idan kun dai-daita shikenan, fatanmu shine Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Ameen Abba nagode,sannan inaso asani acikin addu'a."
"Insha Allah Farhan,Allah ya had'a kawunanku"
Ameen Abba nagode sosai" sannan ya fice duk kunya ya kama shi.
Fitar Farhan ne Abba yaketa addu'oi acikin ransa,dan Farhan mutum ne wanda ko wani uba zaiso ace 'yarsa ta samu miji kamarsa,ga Addini ga nutsuwa da sanin darajan mutane.
Nan take ya kira Umman Mubeenat ya sanar da ita wannan abin farin ciki daya samesu yau,itama murna sosai tayi tare da yin addu'a "Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Abba ya amsa da "Ameen"Washe gari da safe bayan sun gama shirin zuwa gurin aiki,Farhan ne ya fita dasu ita da Amal. Mubeenat ce a gaba se ita Amal d'in a baya.
"Ya Farhan amma dai yau bazamu dad'e sosaiba nida Amal don yau za'a fara program na auren Aisha Kabir"
"Ok Habibty,bakomai"
Murmushi tayi tare da juyowa ta kalli Amal sukayiwa junansu murmushi.
Isarsu k'awayensu ko kuma ince abokan aikinsu suka taho ana gaida Farhan "Good morning Sir"
"Morning dukkanku kuzo nan"
Duk aka taru har dasu Amal ana sauraron abinda zaice.
Fuskarsa cike da fara'a ya fara magana cikin nutsuwa "Bakomai ne yasa na tara kuba sedan wata alfarma da nake nema agurinku"
Kowa yayi shuru yana son jin menene kuma yau Sir zai nema agurinmu,harda su Mubeenat a wannan tunanin.
Yaci gaba da cewa "Ina buk'atar addu'oinku akan wani abu da nake nema Allah ya tabbatar min da alkhairi akan sa"
Nan aka amsa da "Ameen"
Sannan wani yace Sir akan company namu ne?"
"No! Neman aure nakeyi,dan haka ku tayani da addu'a please?"
"Masha Allah Sir Allah ya tabbatar da alkhairi Allah yasa rabon kace"
Cikin jin mamaki Mubeenat da Amal suka kalli junansu "Neman aure kuma? A ina kenan Ya Farhan yake neman aure?" Suke tambayar zuciyarsu wanda duk hankalinsa agunsu yake.
"Ameen" ya furta tare da cewa "Nagode zaku iya tafiya"
Nan guri ya watse kowa ya koma gun aikinsa suna mamakin wace mai rabo ce haka Sir Farhan yake nema?Mubeenat da Amal dai abun ya damesu sosai,dan har Amal tana cewa Mubeenat nifa gani nake kamar Ya Farhan yana sonki? Hmm kema dai to idan ma yana sona ai bai tab'a gaya minba dukda dai nima nakanyi wannan tunani wani lokacin.
Bayan Mubeenat ta gama tunaninne ta kalli Amal tace "Amma kuma fa banji zancen Ya Farhan yana neman aureba,kinga aiko Ya Atif ma zai gaya min ko kuma su Umma ko?"
"To nima dai mamakin da nake tayi kenan tun d'azu wlh,gaba d'aya jikina yayi sanyi Mubeenat."
"To koma dai wacece Alah ya tabbatar mishi da alkhairi."
Cikin sanyin jiki Amal ta amsa da "Ameen."Bayan awa biyu Farhan ya kira Mubeenat a waya,batare da b'ata lokaciba ta d'auka tare da cewa "Hello Sir"
Cikin murya mai dad'i yace "Bana gaya miki indai nida ke bane ki dena kirana da Sir?"
Murmushi tayi "I'm sorry Ya Farhan"
"It's okay,zan iya samun coffee?"
"Sure" sannan ta katse wayar taje ta had'o kamar yadda ta saba tayi sallama sannan ta shiga yana zaune yana shan sanyi AC.
Ahankali ta ajiye akan table dake gabansa tace "Bisimillah Ya Farhan" fuskarta d'auke da murushi.
Kallonta yayi tare da cewa "Thanks" sannan ta juya zata koma yayi saurin kiran sunanta "Habibty?"
Cak ta tsaya tare da juyowa "Na'am"
"Baza kimin murna bane kodai bakiji abinda na fad'a bane d'azu?"
Murmushi tayi tare da k'aik'aya kanta a hankali "I'm sorry,na tayaka murna Ya Farhan Allah ya tabbatar da alkhairi."
"Ameen,amma har cikin zuciyarki kika fad'i hakan?"
Kallonsa tayi cike da mamaki "Eh mana ai abun farin cikine sosai dukda dai baka sanar daniba tun a gida seda muka zo nan"
Coffee d'in ya ajiye tare da mik'ewa yazo har inda take tsaya yana kallon kyakkyawar fuskarta tare dayin k'asa da muryarsa "Kina nufin bakya kishi?"
Kallon juna suka tsayayi tace "Kishi kuma? Akan me zanyi kishi ya Farhan,ai sedai intayaka murna"
Lips nashi ya tsotsa tare da sake kallonta "Are you sure Habibty?" Yana mai kallon cikin idanunta.
Wani irin nauyinsa taji dan kallon dataga yana mata,dan haka tayi saurin sunkuyar da kanta tace "Yes,zan iya tafiya?"
"Yeah,k'arfe nawa zaku tashi yau?"
"12:00 dai ko kuma idan munyi sallan azahar"
"Ok wazai maidaku?"
"Ya Atif zaizo ya d'aukemu"
"Badamuwa idan kun shirya ki gaya min"
"Ok" sannan ta wuce yana binta da murmushi...Vote and comment please
Team #FARBEEN
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...