6

1K 64 5
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

©Pure Momment Of Life Writers

Wannan page d'in nakine faty axland😘naji dad'in samunki akusa dani matuk'a,Allah yabar zumunci ameen🌺🌺🌺


Page 6
Murmushi atif ya tsayayi yayinda mubinat taketa faman juyi akan gado.
"Barkanki da farkawa gimbiyan mata"
Kunya sosai taji,dan gabad'aya tamance cewa ba'agidansu takeba yanzu. D'an murmushi tayi batare datace komaiba ta mik'e zuwa toilet. Byan fitowartane shima ya shiga yayi alwala yazo sukai sallah.
Abincin da umma takai musu hospital shiya d'auko musu yakawo sukaci tare sannan ya bata magungunanta tasha.
"Sis mubinat" yakira sunanta. "Na'am" ta furta tana kallonsa.
"Kizo ki zauna muyi magana" babu musa taje kusa dashi ta zauna tare da zuba mishi ido.
Fiskarsa cike da fara'a yace "inaso kigayamin abinda kike so da kuma wanda bakya so domin in kiyayesu musami  zaman lfy atsakaninmu"
Ajiyar zuciya tayi sannan tace "indai kamin alk'awarin cewa bazaka nemi wani abu daga gareniba bayan wanda ka nema d'azu toshikenan babu wata matsala"
"Kina nufin babu tarayyan aure tsakanina dake kenan"?
Shuru tayi ta kasa amsamishi. "Sis mubi,idan dai kinaga hakan daidaine toba komai,nayi alk'awari bazan kusancekiba harse randa kika fara ganina amatsayin mijinki"
Manyan idanunta ta d'ago tana kallonsa cikin tausayi dajin kunya tace " dan Allah kayi hak'uri ya atif,kad'anmin hak'uri har zuwa... shiii kidena damuwa sis mubi nafahimceki,kuma zan jira harse lokacin da kika fara sona amatsayin miji ba yaya ba. Janyota yayi zuwa jikinshi ya rungumeta yana shafar bayanta tare da rad'a mata cewa "ina so wannan maganar yazama sirri atsakanina dake,sannan inaso kisaki jikinki dani kidena kunyana sannan bazaki hanani huging nakiba hakama kuma kiss,kin amince da wannan"? Kai ta d'aga masa alaman eh ta amince tare da murmushi a fiskanta.
Shima murmushin ya mayar mata tare da tsunbatan goshinta yana jin dad'in ganin yadda ta sake dashi ayanzu. Cikin zuciyarsa kuwa cewa yake "ya Allah ka karkato da zuciyar mubinat zuwa gareni,Allah ka bani ikon cikamata wannan alk'awari dana d'auka mata ameen"

Bayan sallan isha atif ya tafi gidansu domin karb'a musu abinci,bai jimaba dan dama ya sanar da mum nashi cewa tayi musu abinci.
  Mubinat ta gama shirin bacci dan rigar bacci ne ajikinta amma bamai fitar da siffan jikintaba.
Jin k'aran motar atif ne yatabbatar mata da cewa ya dawo. Sallamarsa taji tare da shigowa ya bud'e mata hannayensa,cikin jin kunya ta mik'e taje ta shige jikinsa,shikuwa d'agata yayi sama tanata faman dariya tana cewa "pls ka saukeni ya atif nifa ba shureim bace" hhhh to ai da kad'an kika fishi,bazan saukekiba harse na kaiki kan daining. Dariya takeyi harya direta akan kujera,ita ta zuba musu abincin sukaci sannan tasha maganinta suka wuce d'akinta. Dama sunyi wanka dan haka brush kawai sukayi sannan suka kwanta cikin bargo d'aya kowa da tunanin da yakeyi cikin ransa.
Babu wani abu daya faru atsakaninsu illa kissing nata dayayi tare da mannata ajikinshi da haka sukai bacci.

Atif yana son kissing arayuwarsa,amma kuwa wannan alk'awari yada d'auka zai iya cikawa kenan?... hmmmm muje dai
Gari ya waye sukai sallah sannan suka koma bacci,cikin ikon Allah jikin mubinat yayi sauk'i sosai sedai muce Alhamdulillah...

Farhan kuwa yana can sararin samaniya inda jirginsu ta d'auki hanyarzuwa madina. Tafiya akeyi amma gabad'aya seyaji dama baiyi tfyanba,ya gwammaci yana nigeria koda lbrntane yadinga ji.
Koda suka isa bro nashi mai suna Abdullahi da kuma sauran 'yan'uwansa maza biyu sukaje tararsa a airpot. Sunyi farincikin ganisa matuk'a tare da murnan memorinsa ya dawo normal yanzu babu wata matsala atattare dashi.
Cikin harshen larabci suketa magana sun rugumesa,murmushi yakeyi dan shima yayi kewarsu sosai. Haka suka d'au hanyar gida yayinda abdullahi yake jan motar.
Wata balarabiya ce kyakkyawar gaske ta fito sanye da doguwar riga irin tasu,ga wani murmushi na farin ciki da takeyi. Farhan naji ya furta "ummi" tare da wani kalamai dayayi cikin harshe larabci suka rungume junansu tana kwalla tare da cewa "Alhamdulillah habibi" sauran kalaman nata dai cikin yarensune wato larabci,amma zaka iya fahimtar abinda take cewa dan yadda take kuka tare da furta sunan mubinat abakinta.
Hannunsa ta rik'o yana kwalla suka shige cikin gida wanda base na gayamuku irin tsarinsaba.
D'akinsa ya nufa ya watsa ruwa sannan ya fito aka zauna jera masa abinci kala kala amma kad'an yaci sannan aka shiga hira.
Dukdai hirar tasu akan mubinat ce,dan mahaifiyar tasa se hawaye takeyi tana rarrashinsa kamar sabon jariri. Koda yake dama larabawa akwai iya nunawa yaransu k'auna fiye da mazajensuma.
Fararen matane biyu suka shigo tare da rungume farhan suna magana cikin harcensu na larabci. Shi kuwa farhan murmushi yad'anyi ba laifi sannan suka zauna kusa dashi anata faman hira...

Mubinat ne zaune da amal da aisha se kuma shureim a palo suna hira. Amal tace "seku tashi mutafi ai tunda naga jikin nata da sauk'i"
"Nidai ba yanzu zan komaba" cewar shureim.
Amal tace "to aisha tashi mutafi dan wlh banso ya atif yadawo ya samemu" mik'ewa aisha tayi tace "to mubinat Allah ya sauwak'a se kuma kin sake ganinmu"
"Dan Allah kudinga zuwa kullum muna hira pls"
Amal tace "to shikenan semunzo gobe amarya mai magarnar sugar". Tafawa sukayi ita da aisha suna mata dariya sannan aisha tace "yanzu shikenan mukuma semuyita yawon zuwa gidanki dan bamu da gurin zuwa,ai wlh kafin ki sake ganin k'afarmu agidannan zai dad'e"
Kallonsu mubinat ta tsayayi tare da harara "hakama zakucemin ko"?
"Mayar da wuk'an aminiyata,kinsan koda aisha zatak'i zuwa tofa nikam zaki ganni wlh" murmushi mubinat tayi tace tona gode kugaidasu umma. "Tashi mutafi shureim" cewar aisha.
"A'a wlh kubarshi idan ya atif yazo zaimaidashi" inji mubinat. To ai shikenan suka had'a baki,tare da zuwa gun motarsu inda driver'n su aisha yake jiransu.

Bayan tfyarsune shureim yakeyiwa sis mubinat hira yana cewa "sis mubi ya farhan ma bayida lfy d'azu abbansa yakegayawa abba wai ciwon kai yakeyi sosai"Kuma dama yace min in kawo masa hotunanki,guda biyar ya d'auka acikin kits nashi yacemin idan kina kuka indinga share miki hawaye sannan ince miki ki zauna da ya atif da zuciya d'aya kuma kiyi masa biyayya dan bayaso kizama d'aya daga cikin wanda ake azabtarwa ranan gobe."
Tunda shureim ya fara magana mubinat take zubar da kwalla harya gama. Hannunsa ta kamo tace "yaushe ya gaya maka wad'annan maganganun?"
"Jiya da dare daya kira wayar umma shine yace abani mugaisa"
Ajiyar zuciya tayi tace "nagode shureim,kace mishi naji sak'onshi" hon d'in motar atif suka jiyo,da sauri ta goge kwallanta dan bata so yasan tayi kuka. Shureim ya fita da sauri yace "dama kainake jira kamaidani gida"
"Amma ai zaka bari inshiga in sanar da sis mubinat tunda bataga shigowanaba"
"To barina tayaka shigar da kayan kafin ka fito"
Kansa atif ya shafa yace "yawwa tona gode" sannan ya wuce da ledan hannunsa ciki.
Sayayyan drinks ne sosai atif yayi dakuma abinda basu dashi. Tas shureim ya shigar zuwa store sannan ya dawo palo ya zauna yana jiran atif.
Rungume yake da ita yace"bari in maida shureim kar dare yayi kina son wani abune"?
"A'a seka dawo"
"Are you sure"?
"Uhm"
"Ok tose na dawo" tare da manna mata kiss a lips nata sunayiwa juna murmushi yafita.
Bayan ta tabbatar da sun tafine ta bud'e wayanta da suka taho mata dashi tana kallon hotunan ya farhan habibinta. Musaman wanda yake bata hak'uri lokacin da shureim ya goge mata komai na wayanta tace seta dakeshi,hakan yasan farhan had'a hannayensa guri d'aya yana bata hak'uri akan karta dasheshi sanye da bak'in shets ajikinsa. Ganin yayi mata kyaune alokacin yasa tayi mishi wannan hoton.
Koda ta dawo daga duniyar tunani seta sake fashewa da kuka tana cewa "Allah yabaka lfy ya farhan..."

Vote and comment pls

                                    Team #KNJ#

KOMAI NISAN JIFAWhere stories live. Discover now