🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸by maman shureim
🌺sad-nas🌺*©Pure Momment Of Life Writers*
We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers❤Page 35
Amal ce zaune da mahaifiyarta waisam se an mata tsifa.
"Yanzu k'atuwar budurwa dake amma kice senayi miki tsifa Amal?"
"Nidai wlh ke zakimin danni bana sauri"
"To amma ai ni yanzu ina da abinyi sedai ki bari zuwa anjuma sena miki"
"Nidai yanzu zaki min,anjuma zanje gun Mubeenat ne ai zamuyi bak'i"
"Idan kika nace wa abu kaman d'an da yake cikin mamanshi zai fito duniya"
"Hhhh Ummata ni kad'ai idan baki minba wa zai min,nice 'yar fari kuma auta fa"
Baban Amal dake zaune daga gefe se dariya yake yi "Ba dole ta sakalce ba,kince ita kad'ai ta isheki ai duk laifinkine kece kika shagwab'ata haka"
"Haba Abban Amal lokacine bai yiba"
"Haka dai kike cewa kullum"
Sunata hiransu gwanin sha'awa se suka jiyo sallama,wata mata ce tare da wani na miji.
Da sauri Umman Amal ta mik'e tana murna tare da cewa "Wa nake gani kamar Samira yau?"
"Nice dai wlh"
Nan taje ta rungumeta tare da isar da ita parlour'n ta,shi kuwa na mijin tace ya shiga parlour'n Abban Amal.
Bayan Amal takai musu abinci da abin shane suka gaisa sannan ta fita tayiyo gidansu Mubeenat.
"Samira ashe kina duniya,ya bayan rabuwa?"
"Alhamdulillah ashe dai gidan ba b'oyayye bane kwatancenki da kuma sunanki kawai na tambayi mutane shine aka kawomu har bakin gate naku."
"Allah sarki samira kardai ince tun bayan rasuwan mijinki bakiyi aure ba?"
"Wlh kuwa banyi ba duk wanda nace mishi zan zauna da k'aninane to bazai sake dawowa ba."
"To kema samira in banda naki a zamaninnan wazai yarda kikai masa k'aton saurayi haka,ko k'anana agolama ya aka k'are dasu bare kuma Sagir k'aton saurayi ai kema kinsan bazai yuba."
"Hakane to amma ya zanyi,mu biyun kenan muka rage kuma gaskiya bana son mu rabu dashi"
"Hakane,amma ai koda wani aikinne seya fara yi kinga ko'a wani gidane seki kama mishi haya,wai har yanzu haka Sagir yake baya aikin komai se'an mishi?"
"Wlh haka yake,yadda dai kika sanshi adah toh har yanzu babu abinda ya canja"
"Tabd'i lallai akwai aiki,ai wlh kinsan nidai bazan yadda da wannan shiriritan ba dolene ya nemi abinyi kema ya barki kiyi aure ina amfanin yawo haka kana da shekara 29 zuwa 30 ace komai se'an maka kamar k'aramin yaro?"
"Ai dama nasanki da zafi shiyasa ma nace yadai kamata muzo ko zai samu aiki ta gunki nima in samu inyi aure in dena galanfiri akan titi wlh ni kaina auren nake so Sagir ne yake b'atamin komai wlh"
"To ai shikenan,kici abinci muje ku gaisa da Abban Amal"
"To" sannan taci abinci tana k'arewa gidan kallo da kuma yadda taga abincin nasu had'ad'd'e ga nama zok'o-zok'o ga kuma yadda taga tsarin gidan nasu ya burgeta suma kansu suna da kyan gani a ido ba kamar muba.Mubeenat ne zaune da Amal inda Amal take bata labarin sunyi bak'i.
Haka dai suketa hiransu har Mubeenat ta gama mata tsifan tas ta tace mata kan ta d'aure sannan taje ta wanke hannunta ta dawo sukaci gaba da hiransu.
Hon suka jiyo da k'arfi nan suka fito waje dan ganin wazai shigo.
Honda accord ce one door 2010 ta shigo kai tsaye.
Mubeenat ta kalli Amal itama Mubeenat d'in take kallo sukayi magana a tare "Ya Atif?"
Da murna suka k'arasa gurin motar Amal taje daga d'ayan gefen,ita kuwa Mubeenat ta koma ta gefensa tare da bud'ewa tace "Ya Atif dama kaine bak'on?"
Murmushi yayi tare da fitowa daga motar yace "Wani bak'o kenan?"
"Wanda zai dawo gidannan da zama a matsayin yayana"
"Nop bani bane nidai nazo ne mu gaisa kuma in koma zuwa anjuma"
Nan jikin mubee yayi sanyi ta karb'i Ipad na hannunshi tace "To waye ne bak'on kenan?"
"Sis Mubee bakya murnan ganina ne yau?"
"Inayi mana sosai ma,amma dai naso ace kaine zaka zauna anan shiyasa duk naji ba dad'i"
Ganin yadda tayine yasa Atif rik'o hannunta "Ooh come on Sis Mubee fushi baya miki kyau dan haka ki dena"
Dariya sukayi ita da Amal sannan suka wuce ciki inda ta jero mishi abinci tare da cewa bismillah Ya Atif ninayi girkinnan dan haka kaci ka k'oshi sannan ka gayamin yayi dad'i ko baiyi ba."
"Ok" sannan ya fara ci yana kad'a kai,ita da Amal se dariya suke binshi dashi.
Bayan ya gamane tace "Ehen tell me"
"Sis Mubee i don't believed cewa kece kikayi girkin nan"
"Haba Ya Atif meka mai dani ne? Wacce bata iya komaiba kenan?"
"Not like that Sis Mubee,ban tab'a sanin cewa kina yin girki bane ai that's why"
"To dai nice nayi"
"Woow! so sweet of you my luvlyn Sis,gaskiya a ajiyemin kafin in tafi anjuma zan sake ci kinji?"
"Hhhhh alright" sannan suka zauna suna ta hira.Gidan su Amal kuwa bayan sun gaisa da Baban Amal ne seta nunawa Sagir wani d'aki can kusa dana mai gadi "Ga d'aki can Sagir ka dinga kwana aciki babu kowa"
"To Aunty nagode" sannan ya wuce da kayansa.
Ita kuwa Samira a ciki ta gurin d'akin Amal aka bata wani d'aki da toilet nashi a ciki,nan ta dinga godiya kamar zata had'iyeta.
6:00pm Amal tace "To nidai nayi gida,Ya Atif idan ka tafi ka gaida Aisha"
"Zataji ki gaida Umma"
"Ok" sannan Mubeenat ta rakata har gida domin taga bak'in.
Tun daga gate suka ga Sagir inda ya bud'e idanunsa yana k'are musu kallo "Ina wuni" cewar Mubeenat
"Lafiya 'yan mata ya kuke?"
Bata sake cewa komaiba suka wuce yanata binsu da kallo.
"Nisam baiminba tunda na ganshi wlh,ji yadda yake binmu da kallo kamar wani soko" cewar Amal
"Hhhh amma fa ke baki da kirki bak'onka Annabinka,daga zuwansa harkin mishi mummunan fassara?"
"Haba Mubee kema dai kya fad'i gaskiya kinga yadda yake binmu da kallo kuwa?"
"To ke kuwa aidai kya mishi uzuri na yau kawai"
Samira ce ta fito daga ciki,nan Amal tayi magana wa Mubeenat a hankali "Ga yar tashi nan"
Ita Samiran tace Amal kin dawo?"
Ciki-ciki Amal tace "Eh" sannan Mubeenat tace "Ina wuni?"
Cikin fara'a tace "Lafiya 'yan mata ya sunanki?"
"Sunana Mubeenat"
"Suna mai dad'i gaki kyakkyawa dake sannunku"
Amal ta janyo hannun Mubee suka wuce d'aki tace "Ni wlh gaba d'ayansu basu min ba"
"Kai Amal,dama ke can kin tsani kika bak'i sunzo gidanku musamman ma in kwana zasuyi,to nidai na tafi nabar Ya Atif shi kad'ai se gobe zan shigo miki"
"To nagode" sannan Mubeenat ta wuce har wajen gate se Sagir yace " 'Yan mata ya sunanki?"
Ba tare data tsaya ba tace "Mubeenat"
"Lallai sunan ya dace dake"
Bata ma tsaya jin me zai ceba ta shige gida abinta.
Shi kuwa Sagir yace "Aiho dama nanne gidanku,ashe bamu da nisa ma" yana shafa gemunsa yana dariya kaman bunsuru.
Mubeenat tana shiga sega Abbanta ya dawo,nan ta tsaya ta mishi sannu da dawowa tare da karb'an abinda ya taho dashi ta wuce ciki.
Atif ne ya fito ya k'arasa gun Abba "Sannu da dawowa Abba"
"Atif ka iso kenan,lallai Mamana tana cikin murna yau"
"Eh amma ban gaya mata ba har yanzu ce mata nayi idan nayi sallah zan tafi"
Dariya Abba yayi sannan suka wuce tare.
Har bayan isha ana neman 8:12pm Mubeenat taga Atif baice zai tafi ba,hakan yasa tace "Ya Atif kodai zaka kwana mana ne yau?"
Cikin sauri Shureim yace "Sis Mubee dama fa shine Yayanmu dazai dawo gidanmu da zama"
Cikin rashin yadda tace "Wai hakane Ya Atif?"
Murmushi yayi wanda ya k'ara mishi kyau tare da kashe mata ido d'aya.
Matsowa tayi kusa dasu "Pls Ya Atif da gaske ne wai?"
"Yes" ya fad'a yana mata murmushi.
Nan kunya ya kamata ganin Abba da Umma duk dariya suke mata a parlour'n,da sauri ta mik'e ta fice zuwa parlour'n Umma cike da murna sosai...Vote and comment guys
_Team #KNJ_
YOU ARE READING
KOMAI NISAN JIFA
Fantasywannan lbr ne daya kunshi abubuwa da dama dake faruwa a wannan zamanin namu,ko kuma ince ya zamanto kamar sana'a gawasu mutane. Cin amana,yaudara,makirci da kuma son zuciya. kudai biyoni don warware muku manufata...