'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
3
A yammacin wata asabar ne tana zaune a sitting room tana kallon movie a tashar mbc2. Farida da Ummie ne suka shigo suka zauna. Remote Farida ta dauka tare da canja channel zuwa musicplus. Dagowa tayi ta kalletaganin yadda sukazo suka iske ta tana kallo suka canja mata salon tayi magana suyi mata rashin kunya. "Fadi karta kasheki" shine abinda Farida tace mata. Dauke kai tayi tamkar bata san cewa da ita takeyi ba.
A guje Ruqaiya da Zainab suka shigo suna rige-rigen hawa kanta suka ce "Aunty Aisha mun dawo" da fara'arta ta dagosu tare da cewa "to sannunku da dawowa, sai aje a cire uniform ayi haramar yin sallah magriba ko". A tare suka ce to suna masu wucewa don su canja kayan islamiyyarsu zuwa na gida. "Kai kuzo nan" Farida tace musu "ban hanaku kula wannan matar ba amma shine dayake kunnuwanku na kashi ne ku bakwa ji kullum sai kunje inda take ko, kuna kallonmu amma ko sannu baku ce mana ba kun tafi wurin kanwar uwarku, to wallahi bari kuji na gaya muku daga yauidan na kara gani ko kallonta kunyi sai nayi muku shegen duka, ku wuce ku bani wuri".
Sum-sum suka wuce zuwa dakinsu. Su kam har kullum suna mamakin yadda yayyensu ke yiwa Aunty Aisha tamkar dai ba 'yaruwarsu bace. Ita kam Aisha suna fara yiwa yaran fada ta haya sama ta bar musu parlour. Dakinta ta nufa don yin sallar magriba don kuwa har an fara kiran sallah.
Koda ta idar da sallah bata tashi a wurin ba sai taci gaba da wuridi har aka kira sallar isha ta tashi tayi sannan ta sauka kasa don tayi serving dinner. Akan table ta iskesu sun fara cin abincin kasancewar Daddy baya nan yasa suka fara cin abincin ba tare da sun jirata ba. Tana bude warmers din taga wayam babu komai a ciki, takaici ne ya kamata ganin yadda suka cinye abincin ba tare da sun rage mata ba. Juyawa kawai tayi ta koma daki don bakin ciki bazai barta ta shiga kitchen don neman abinda zata ci ba.
Khalifa ne ya kalli kannenshi dake haramar barin table din yace "ina kuke tunanin tashi kuje ba tare da kun cinye abincinku ba, wannan din wa kuka barwa shi". Turo baki Farida tayi tace "to Yaya Khalifa mun fa koshi ne". Harara ya doka mata sannan yace "come on dawo ku zauna ku cinye, kunsan bazaku ciba kuka kwashe abincin gaba daya ita mai daguwar baku rage mata ba. Idan ma kunyi ne don kuyi mata mugunta to kanku kuka yiwa don kuwa sai kun cinye abincinnan tas ina kallonku".
Haka suka zauna suka tuttura abincin da kyar yana kallonsu har sai da suka cinye tukunna ya tashi ya bar wurin. Tuntsirewa Mu'azzam yayi da dariya har yana rike ciki ganin yadda suke ymutsa fuska kamar masu shirin yin amai. Tsaki Ummie tayi tace "to miye abin dariyar kuma". Wata dariyar ya karayi sannan yace "ai kune kuka sakani dariyar, ai idan kuna son yiwa matarnan tsiya bari zakuyisai Daddy na nan yanda duk abinda zakuyi ba maice muku uffan, amma Yaya Khalifa kam ai kinsan he always has a soft spot for her. Aurenta da Daddy ne ma yasa yaja baya da ita". "Wannan kuma shi ya jiyo, amma mudai ba'a isa a hanamu takurawa yarinya ba tunda dai ta yarda ta auri ubanmu" cewar Farida. Mu'azzam yace "lallai ma Farida bakida kunya, Aishan kike cewa yarinya agemate dina cefa don nasha jin Mami na cewa watanni 2 na bata".
Taking tayi tare da cewa "to shine me don sa'arka ce ko sa'ar Yaya Khalifa ce ai na kirata yarinya tunda kuwa dai a haife Daddy ya haifeta sannan kuma girman da tayi mana bai wuce na shekaru uku zuwa hudu ba. Ni ai tunda ta yarda ta auri Daddy naji na tsaneta ni inaga dama can tana sonshi ta rasa yadda zatayi ne sai kuma ta samu Hajiya ta bullo da maganar aure a tsakaninsu, bakuga ko musu batayi ba ta amince ita a dole ga mai biyayya".TUSHEN LABARIN.
UMMASGHAR.
VOCÊ ESTÁ LENDO
'YA'YAN MIJI
Ficção GeralAisha yarinya ce da rikonta ya dawo hannunta Goggonta bayan rasuwar mahaifiyarta inda ita kuma ta mika ta ga matar danta. Rayuwa ta juyawa Aisha baya ne a lokacin da marikiyarta ta rasu aka aura mata mijin marikiyarta.