'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
24
Ranshi a bace ya shigo gidan. Tun daga kasa yake kwalawa Farida kira. Gaba daya jikinta ne ya dauki rawa jin yanayin da Daddy yake kiranta. Allah yasa dai ba wani laifin tayi ba don tun jiya dama a tsorace take da Daddy ganin bai wani bata goyin baya ba akan rikinsu da maigidanta.
A kasalance ta fito daga dakin don zuwa amsa kiran Daddy. Bata taba zaton akwai wata rana da zata ji tsoron haduwarta da Daddy ba irin yau don yanayin kiran da yake mata sosai ya kidimata. A bakin kofar dakin sukayi kacibis da Aisha da tazo kiranta. Ce mata kawai taje Daddy na kiranta ta wuce zuwa dakinta.
Da kyar Farida ta iya jan kafafunta ta wuce zuwa parlour Daddy. A hankali tamkar bata so tayi sallama, sai bayan daya amsa sallamar ne ta shiga cikin parlour. Durkusawa tayi tace "Daddy ina yini, gani ance kana kirana". Shiru ne ya ziyarci parlour tamkar babu kowa. Shi dai Daddy kallon Farida kawai yakeyi yana mamakin irin halayen yarinyar da abubuwan da mijinta yace tana yi mishi. Sai dai kuma yasan shine babban mai laifi a duk wani hali da Faridan ta kasance a ciki.
Tun tasowarta ya kasancevmai nuna bambanci tsakaninta da 'yanuwanta baya son laifinta ko kadan komai tayi a wurinshi daidai ne. Wani irin so yake yi mata da baya yiwa 'ya'yan daya haifa. Sosai yake tausayinta da maraicinta yana ganin duk duniya bata da sai shi tunda bata san ubanta ba. Kullum cikin nuna bambanci yake tsakaninta da 'yanuwanta don ko abu ne ya hadasu to baya taba bata laifi koda kuwa itace bata da gaskiya sai yace au aukw tsokanarta.
Akan haka sun sha samun sabani da Zainab don tana yawan gwada mishi cewa ba daidai bane abinda yakeyi. Bazai yiwu tayi tsokana ba sannan a bawa wanda t tsokana laifi ba wannan ba adalci bane amma sai ya rufe ido ya hau fada yana cewa don ba 'yarta bace yasa take ganin abin da yakeyi a kanta a matsayin rashin kyautawa amma da 'yarya ce yasan ko daga kai baza tayi ta kallesu ba.
A duk sanda irin haka ta faru sai tace mishi "wannan sangartawar fa da kake yiwa Farida ba gata ne kake yi mata ba domin kuwa ita din 'ya mace ce kuma wata rana gidan aure zata je, babu kuma mijin da zai dauki rashin da'a da rashin tarbiyyarta. Wannan wacce irin rayuwace ace yaro duk abinda yayi daidai ne baza'a mishi fada ba idan nayi magana kace na takura mata saboda ba 'yata bace nana tausayin maraicinta".
A yau ga wata rana din da Zainab ke yawan gaya mishi tazo gashi miji ya koro mishi Faridanshi akan halayenta marasa kyau. Allah ya jikan Zainab yayi mata Rahama, har kullum yana jin kewarta tana damunshi ya sani a zamansu bai kyuata mata ba don kuwa bai bata dama tayiwa yaranta irin tarbiyyar da take so ba. Dagowa yayi ya kalli Farida da jar lokacin take a durkushe tana sharar hawaye. A lokacin daya shigo daga ganawarsu da mijinta ranshi a matukar bace yake shine ma dalilim da yasa ya shigo yana kwala mata kira abinda ya fito da Aisha daga kitchen tana tambayarshi lafiya. Zaunar dashi tayi ta kawo mishi ruwa yasha sannan tace mishi bawai zai samu Farida da fada bane, nasiha zaiyi mata ya nuna mata cewa baya son munanan halayenta baiji dadin yadda take tafiyar da al'amuran gidanta ba a cikin nutsuwa ba wai da fada ba.
"Yanzu maigidanki ya bar nan mun kuma tattauna akan yanayin zamanki dashi da kuma iyalinshi. Banji dadi ba yanda yace wai bakya girmamashi bakya girmama matarshi sannan kuma bakya son 'ya'yansgi ba kyaso kiga yana kyakkyawar mu'amala dasu. Wanne irin sonkai ne dake Farida, yaya zakije gidan mata da 'ya'yanta kice wai mijinta bazai yi hulda da ita ba, to a ina aka taba irin haka.
Ai kema kinsan bakiso a zauna lafiya ba. Kin kuma dauki hanyar nesanta kanki ne da mijinki don ko ni nan bazan taba son matar da bata son iyalina ba. Don haka ina horonki da idan kin koma gidanki ki sake tsarin mu'amalarki da maigidanki da kuma iyalinshi.
YOU ARE READING
'YA'YAN MIJI
General FictionAisha yarinya ce da rikonta ya dawo hannunta Goggonta bayan rasuwar mahaifiyarta inda ita kuma ta mika ta ga matar danta. Rayuwa ta juyawa Aisha baya ne a lokacin da marikiyarta ta rasu aka aura mata mijin marikiyarta.