BABI NA ASHIRIN DA DAYA

478 45 0
                                    


          'YA'YAN MIJI

Na Umm Asghar

             21

A yanzu da akayi wa su Farida aure Aisha bata da wata matsala a cikin gidanta don sosai Ruqaiya da Zainab ke yi mata biyayya kuma dama dai a yadda yaran suka taso tare da ita bata da matsala dasu.


An gama biki da sati biyu Daddy ya kwashi Aisha da yaranta masu watanni biyar suka tafi umrah sai Zainab da Ruqaiya kasancewar Yaran na hutu.

Mu'azzam kawai aka bari a gida don har lokacin Daddy ba wai ya huce daga fuahin da yakeyi dashi bane. A lokacin da Daddy yayiwa Aisha maganar tafiyarsu Umrah sosai tayi murna sai ta tuna lokacin da Farida tayi ta mata kafafa akan zasuyi tafiya su barta to itama yanzu gashi nata lokacin yayi don dama komai yana da lokacin.


Sosai Ruqaiya da Zainab ke taimaka mata wajen rainon twins, duk da Daddy na fadan yawan bawa yaran twins da take yi wai kar su kada su. Idan yana fadanshi kawai sai dai tayi dariya tana mamakin son 'ya'ya irin na Daddy shi komai a harkar yaranshi idonshi yana kai.

Sai dai ta sakawa ranta cewa ita kam bazata yadda ya bata mata yara ba irin yadda yayiwa su Ummie shine kuma dalilin da yasaka suke taka kowa ba tare da fargaba ba don sun san komai sukayi a wurin ubansu ba laifi bane.


Sai da sukayi sati uku sannan suka dawo gida nigeria, gaba daya a wannan lokacin Aisha ta canja ta kara yin kyau saboda kwanciyar hankali data samu ga uwa uba  soyayya da kulawar mijinta data samu.

Bayan sati daya da dawowarsu ne Daddy yace ta shirya ta rakashi gidajensu Ummie yaje yaga dakunansu don tun da akayi auren bawai yaje bane.

Tayi shirinta cikin atamfar super exclusive kalar navy blue da ratsin fari da light yellow a jiki sai tayi amfani da farin mayafi da takalmi. Bata dauki jaka ba sai wayarta data rike a hannunta.

A gida ta bar twins qurin masu rainonsu kuma ganin su Ruqaiya na gidan yasa bata damu sai ta fita dasu ba.

Gidan Farida suka fara zuwa, Daddy yace ta shiga ta sanar musu da zuwan shi. Ta shiga cikin gidan da sallama, a main parlour su ta tarar da uwargidan Faridan tare da yaranta da maigidan.

Cikin girmamawa sosai matar ta karbeta duk da cewa zata iya girmewa Aisha. Bayan sun gaisa ne Aishan ke tambayar Farida tace mata tana dakinta ta saka yarinyarta ta raka Aisha.

Kafin su wuce ne Aisha ke sanar musu cewa tare da Daddy suke ai kuwa maigidan naji yayi hamzarin tashi yana cewa bari yaje ya shigo dashi.

Ta shiga dakin Farida tana ta kwala sallama amma ba'a amsa ba don haka ta zauna a parlour tacewa yarinyar ta shiga dakin ta yi mata magana. Ta shiga babu dadewa ta fito ta ce mata wai gata nan zuwa.

Tayi zaman fiye da mintuna goma kafin Farida ta fito tana yatsina fuska ta zauna. A dakile tace mata ina yini, lafiya kawai Aisha tace mata tace "tare muke da Daddynku yace na rakoshi yaga gidanku so yana kasa idan kinga dama kina iya zuwa ki gaisheshi".

Jin cewa yare suke da Daddy ya sa tayi saurin tashi ta fita. Ta dan jima kafin ta dawo, kamar bazata yiwa Aisha magana ba sai kuma tace mata "Daddy yace kije ku tafi" mikewa tayi ta ajiye mata ledar tsarabarta tace mata "to Allah ya bamu alkhairi" bata jira amsawarta ba ta fice.

Daga gidan Farida gidan Ummie suka nufa. Anan ma Daddy bai shiga ba. Ita kam Ummie ta karbeta da mutunci da murnarta har tana tambayarta twins tana cewa me yasa ba'a zo dasu ba.

Bayan sun gaisa ne take sanar mata cewa tare suke da Daddy. Sosai tayi murnar jin Daddy yazo gidanta. Tashi tayi ta shiga part din maigidan ta sanar mishi, babu wani dadewa kuwa ya fito.

Har kasa ya tsugunna ya gaida Aisha sannan ya fita don ya shigo da Daddy. A parlourshi ya saukeshi don haka can Ummie ta bishi ta gaidashi. Sun danfi dadewa a gidan Ummie  sannan Daddy yace ta fito su tafi.

Itama ajiye mata tsarabarta tayi sannan sukayi sallama ta fita. Har wurin mota suka raka su sunata godiya. Ummie na rokon Daddy don Allah ya bari su Ruqaiya suzo mata don tunda akayi auren ya hanasu zuwa.

A hanyarsu ta komawa gida ne ya biya da ita  grand square sai dai be yadda ta shiga ba, bayan ya fito ne ya miko mata leda mai dauke da turaruka designers guda uku. Sai kuma chocolates da biscuits na yara.

UMMASGHAR.

'YA'YAN MIJIOnde histórias criam vida. Descubra agora