Babi na Hudu

514 40 0
                                    

'YA'YAN MIJI

Na Umm Asghar

4

TUSHEN LABARIN

Ja'afar Bello Danmaliki haifaffen garin kano ne a cikin unguwar gadon kaya sai dai iyayensu asalinsu mutanen karamar hukumar gaya ne. Su biyu iyayensu suka haifa shi da kaninshi Ismail. Daga Ismail mahaifiyarsu da suke kira da Hajiya bata kara haihuwa ba hakanan kuma mahaifinsu bai yi sha'awar kara aure ba ko don ganin ya samu wasu 'ya'yan.
Ja'afar yayi karatu tun daga primary anan kano har ya gama secondary, daga nan ya wuce Nigerian defence academy wato nda a kaduna inda ya karanci engineering a bangaren army ya fito da mukamin 2nd lieutenant. A shekarar daya fito daga nda ne ya auri dadaddiyar budurwarshi tun ta yarinta wato Zainab wacce ta kasance 'yar makotansu.
Watannin aurensu goma Zainab ta haifi danta na farko Muhammad Bello mai sunan mahaifin Ja'afar suna ce mishi Khalifa. Khalifa nada shekaru uku ta haifi Ibrahim Mu'azzam. Bayan Mu'azzam ne ta haifi Khadija (Ummie) mai sunan mahaifiyarta. Tsakanin Mu'azzam da Ummie ma shekaru uku ne. A shekarar da Zainab ta haifi Ummie ne Ismail kanin Ja'afar yayi aure a cikin kuma shekarar ne dai Allah yayi mishi rasuwa a dalilin hatsarin mota, ya rasu ya bar matar shi da cikin wata shida.
Mutuwar Ismail ta kada Ja'afar sosai don kuwa akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Bayan watanni uku da rasuwar Ismail matarshi ta haifi diya mace akasa mata suna Farida. A lokacin da Farida ta isa shiga makaranta nevya karbota ya kawowa Zainab sannan ya sakata a makaranta tare da Ummie. Farida da Ummie sun taso tamkar 'yan biyu kasancewar duk sunyi kama da iyayensu maza ne don sau tari mutanebna dauka 'yan biyu ne.
Tun bayan Ummie Zainab bata kara haihuwa ba sai da aka shekara goma don har ta fara cire rai da haihuwa sai kuma Allah ya kawo. A ranar wata litinin ne da safe tana zaune tana shayar da jaririyar data haifa Ruqaiya Hajiya wato surukarta tayi sallama a tare da wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha uku ba.
Mikewa tayi tsaye tana cewa "Hajiya sannu da zuwa" "yauwa sannu Zainabu sai ke kadai ko yaran duk sun tafi makaranta" tace bayan ta zauna akan kujera. Zaman itama Zainab din tayi tana cewa "wallahi kuwa Hajiya kinji yanda gidan yayi shiru sai sun dawo kuma, barka da asuba Hajiya an tashi lafiya" tace tana mai rusunawa. "Lafiya lau ya kwanan yaran" "lafiyarsu lau Alhamdulillah". "To Masha Allah dama yarinyace na kawo miki, ina take ne ma kame Aisha" tace tana waigawa. Tasowa yarinyar tayi daga inda take a bayan kujera tazo ta tsugunna tacr "Hajiya gani". Gyara zamanta tayi sannan tace "kinaji ba Zainabu yarinya ce 'yar kanwata a kauye uwar ta rasu shine na dauko ta ganin ita kadai uwar ta bari to shine naga gara na kawota nan wurinku tunda dai akwai yara sai ki hadasu ki rike ko 'yan aikace-aikace ta taya ki, amma don Allah Zainab ki rike mini ita amana tamkar 'yarki tunda dai da na kowa ne ladanki na wurin Allah bare ma rikon maraya Allah ne kadai zai biyaki".
Dagowa tayi ta kalli yarinyar. Ba laifi kam yarinyar tsaf take babu wani alamu na kazanta ko kauyanci a tare da ita. Tace "to Hajiya nagode Allah ya kara girma, Allah kuma ya tayani riko yaya sunanta". "Aisha sunanta, abokan wasa muke da uwar ta jima bata haihu ba saida girma ya fara kamata sannan Allah ya bata Aisha daga ita kuma bata kara haihuwa ba". Ta juya ta kalli Aisha tace "kina jina Aisha ga Zainabu nan a wurinta zaki zauna ki dauketa tamkar mahaifiyarki kiyi mata biyayya, da nan gidan da can wurina duk daya ne don haka kar ki sanu wata damuwa kinji, Allah yayi miki albarka"
"Bari na tafi Zainabu idan yaran sun dawo ace ina gaishesu" tace tana mikewa. Har wurin mita suka rakata sannan suka dawo ciki. "Zo nan kusa dani ki zauna" Zainab tace mata. Tasowa tayi ta zauna a darare akan kujera inda ta nuna mata. Dafata tayi tare da cewa "ki saki jikinki dani kinji Aisha, ki daukeni tamkar mahaifiyarki duka abinda kikeso ki gaya mini In Sha Allahu zanyi miki shi idan har baifi karfina ba, kuma daga yau Mami zaki na ce mini kamar yadda 'yanuwanki suke kirana, basanan suna makaranta yanzu amma idan sun dawo zaki gansu".
A hankali ta gyada kai tace "nagida Mami In Sha Allahu zaki sameni mai bin abin da kika ce". Mami tace "to haka ake so yanzu tashi muje na nuna miki dakinku". Tashi tayi ta dauki ledar kayanta tabi bayan Mami suka hau sama zuwa dakinsu Ummie. Daki ne babba yana dauke da gado 6by6 sai wardrobe din jikin bango da madubi. A wardrobe din Mami tace ta ajiye kayanta sannan ta nuna mata bandaki ko tana da bukatar shiga ta juya ta fita.

UMMASGHAR.

'YA'YAN MIJIWhere stories live. Discover now