Babi na farko

1K 88 2
                                    

Sadaukarwa gareki 'yaruwa rabin jiki Fatima (Uwani) Eshak, Allah ya jikanki ya kyautata kwanciyarki

               1
Zaune take akan kujerar gaban madubi tana shafa man body shop. Bayan ta gama ta dauko haɗaɗɗiyar humrar ta tabi dukkanin gaɓoɓin jikinta ta shafa sannan ta ɗauki doguwar rigar baccinta mai santsi kalar purple ta saka.

Hair spray din argan oil(ors) ta fesa a gashinta sannan ta ɗaureshi a cikin ribbon ta kawo hula kalar light purple ta rufe kanta da ita.

Turaren sandra (al rehab collection) ta feshe jikinta dashi haɗe da sassanyar turaren cool water. Zani ta ɗauka ta ɗaura akan kayan baccin ta saka hijabi, wayarta dake ajiye akan durowar gefen gado ta ɗauka ta fita daga ɗakin tana mai janyo ƙofar ta rufe da makulli don tasan kaɗan da aikin yaran gidan su shiga suyi mata ɓarna duk kuwa da ba wai ƙananun yara bane su tsabar neman magana ne da rashin son a zauna lafiya.

A daidai corridor da zai sadata da dakin maigidan suka yi karo da Ummi wacce ta fito daga parlourn mahaifinsu. Kallon sama da ƙasa tayi mata sannan ta doka tsaki tare da cewa "maciyiya amana har an fito za'a tafi turaka? Ke yanzu ko kunyar idanunmu ba kya ji sai ki fito ki shige ɗakin ubanmu da sunan kin tafi ɗakin miji kina kallon idonmu muna kallon naki. Wai ace duk irin hallacin da muka yi miki a cikin gidan nan ki rasa da abinda zaki saka mana dashi sai auren Daddy, mijin Mami nefa? Matar data soki ta ɗaukake ki ta riƙe ki amana tamkar ita ta haifeki, tayi miki duk wani gata da iyayen da suka kawo ki duniya suka kasa yi miki irin shi amma ki rasa mijin aure sai nata, saboda tsabar cin amana da yaudara bayan mun ɗauki dukkanin yarda mun baki ki rasa da abinda zaki saka mana sai auren ubanmu". 

Bangazarta tayi sannan ta wuce ta bar ta a tsaye a wurin tamkar wacce aka dasa. Tafi minti biyar a tsaye tana jujjuya maganar Ummie a ranta, bata san me yasa suke ganin laifinta cikin abinda bata da laifi ba. Suna manta cewar ita ma ba'a son ranta ta auri Daddy ba sai don anfi ƙarfinta kuma dolenta tayi biyayya.

Hannu ta saka ta goge ƙwallar da taji ta ciko a idanunta don haka nan taji tana son yin kuka sai dai kuma dolenta ta haɗiye kukan don bata san me zata cewa Daddy ba idan ya tuhumeta dalilin kukanta. "Hmm... Like he'd care" tace a cikin ranta, wasu lokutan takan manta cewa bata gaban Daddy shi yasa duk cin kashin da ƴaƴanshi suke yi mata bai taɓa tsawatar musu ba.

Da ƙyar dai ta janye ƙafafun data ji sun yi mata nauyi ta wuce zuwa ɗakin Daddy. A hankali ta tura ƙofar tare da yin Sallama. A can ciki ya amsa mata sallamar don idan banda taga alamar motsawar bakinshi yayin amsa sallamar da sai tace bai ji ta ba don ko ɗagowa bai yi ya kalleta ba.

Yana zaune a kan gado ya jingina da allon gadon sai ya ɗora ƙafafunshi akan gadon ya miƙar dasu. Takardu ne yake dubawa.

"Sannu da aiki Daddy" tace mishi bayan ta ninke hijab da zanin data ɗora akan kayan baccinta, don kuwa dokarshi ce idan har ta shiga ɗakinshi to dole ne ta cire duk wasu kaya data ɗora a kan kayan baccinta don baya son ayi mishi zaune a cikin hijabi tamkar matar mamaci a cewar shi fa amma.

"Akwai abinda kake buƙata kafin na kwanta?" ta tambayeshi cikin kaskantar da murya cike da ladabi duk kuwa da bai amsa sannun data yi mishi ba.

Kamar ba zai amsata ba kuma can sai ya ce mata "black tea nake so".
Zaninta ta mayar sannan ta saka hijabin ta fita. Kitchen ta nufa ta dora ruwan tea data saka lipton guda biyu da kayan ƙamshi wajen dahuwar sai teaspoon ɗaya na strawberry flavour data zuba.

Bayan ya tafasa ta juye a cikin flask ta ɗora akan tray hade da kofi da cokali da zuma don Daddy baya shan sugar sai dai yayi amfani da zuma ta ɗauka ta nufi ɗaki.

A zaune a inda ta bar shi anan ta dawo ta sameshi bai ko motsa ba, akan bedsida drawer ta ajiye tray ɗin sannan ta wuce banɗaki ta haɗa mishi ruwan wanka. Tana fitowa ta sanar mishi cewa ta haɗa mishi ruwan wanka.

Tashi yayi ya shiga banɗakin ita kuma ta tattare mishi takardun ta zuba a cikin wata brown envelope da ta gani haɗe da takardun ta buɗe drawer ta saka mishi a ciki.

Ƙara karkaɗe gadon tayi sannan ta ɗan ɗofana a bakin gadon ta zauna tana jiran fitowarshi. Yana fitowa ta tashi don karɓar towel ɗin hannunshi yayi maza ya ďaga mata hannu alamar ta bari.

Komawa tayi ta zauna a bakin gadon ta jira har ya gama shiryawa ya hau kan gadon yana shirin kwanciya don kamar ma ya manta da kayan shayin da yasa ta haɗo mishi.

Tashi tayi ta ɗauki kofi ta zuba mishi tea ɗin sannan tace "Daddy ga tea ďin". Tashi yayi ya karɓi kofin ya kai bakinshi ya kurɓi ruwan shayin.

Tana kallon yadda ya lumshe ido ga alama shayin yayi mishi daɗi. Yana gamawa ta haɗa kan kayan ta mayar kitchen, ko da ta dawo ɗakin har ya kwanta don haka ta kashe fitila ta hau kan gadon ta kwanta don sosai take cikin gajiya, bacci kawai take so ta samu.

Tana kwanciya ya saka hannu ya janyota cikin jikinshi tare da kashe mata jiki da kalolin wasannin shi. Dole ta wartsake ta kula dashi har sai da ya samu gamsuwa bayan wani dogon lokaci sannan ya sarara mata. Har kullum tana mamakin yadda Daddy baya iya ɗaga mata ƙafa ta wannan fannin, yadda yake rikice mata idan sun zo kwanciya na bata mamaki sam kamar ba shine wannan Daddyn da bai damu da ita da al'amuranta ba, kamar ba shine wanda aka yiwa dole yake zaune da ita ba.

Your votes and comments will really be appreciated, thank you.

'YA'YAN MIJIWhere stories live. Discover now