BABI NA SHA TARA

597 48 0
                                        


        'YA'YAN MIJI

Na Umm Asghar

             19

Yau kwanankin Aisha uku a asibiti kuma yau dinne ake saka ran za'a bata sallama. A cikin kwanakin nan gaba daya su Farida sai wasan buya suke yi da Daddy ko da wasa basu bari sun hadu dashi ba.

Shima kuma baibi takansu ba don a yanzu ba abinda ke gabanshi ba kenan. A yanzu ta lafiyar Aisha yakeyi, ya bari ne sai sun koma gida sannan ya zauna dasu dukkansu don yaji miye musabbabin hatsarin daya faru.

Baya so ya zurfafa zarginshi akan yaran sai dai kuma yanayinsu  a lokacin ya nuna tabbas basu da gaskiya. Gashi kuma tun ranar bai kara sakasu a idanunshi ba abinda ya kara assasa zargin da yakeyi na cewar sune ke da alhakin kada Aisha har ta kusa tayi loosing yaranta.

Mutanen gaya ma sun samu labarin haihuwar Aisha don haka sukayita tururuwar zuwa dubata, Yakumbo Dije kuma ta zauna don ta kula da lafiyarta data jariran.

Koda aka sallameta gidanta aka wuce da ita duk da dai Hajiya taso ta tafi da ita gidanta amma Daddt yace a'a tunda dai ga Yakumbo Dije babu bukatar sai ta koma wurin Hajiya.

Koda suka dawo daga asibitin su Ummie basu je sun mata sannu ba bare suga babies, Khalifa ne kadai ya shiga ya dubata a daren ranar sai kuma su Ruqaiya da suka tare a dakinta basa motsawa ko nan da can.

Bayan kwana biyu da dawowarsu daga asibiti ne Daddy ya tara su a parlourshi na sama, tun daga kan Khalifa da ba ma ya nan abin ya faru har zuwa kan Farida. Ruqaiya da Zainab ne kawai babu.

Hatta da Hajia a ranar sai da tazo don tun suna asibiti ya gaya mata cewa yana so za suyi magana amma bai gaya mata akan miye ba sai kuma a yau yayi mata waya yace ya tura Khalifa ya daukota.

Gaba dayansu sun taru a parlourshi har Aisha. Ga Mu'azzam da Farida kuwa gaba daya sun rude don sun tabbatar da wannan zaman akansu akayi shi, hatta da Ummie a tsorace take.

Kallon wurin da suke Daddy yayi yaga yanda sukayi tsuru-tsuru kwata-kwata basa cikin nutsuwarsu.

Bayan wasu 'yan mintuna ne Daddy yayi gyaran murya yace "abinda yasa na taraku duka anan shine dan na sanar daku abinda ya faru kwanaki biyar da suka wuce na samun Aisha da nayi kwance a cikin jini bata cikin hayyacinta sai kuma wadannan da na samu a tsaye akanta wanda bana raba daya biyu sune sukayi sanadin dana sameta a halin dana tarar da ita" ya fada yana mai nuna su Mu'azzam.

Yaci gana da cewa "shine yasa na taraku anan don ina son sanin asalin abinda ya faru, Aisha ko zaki gaya mini yanda akayi kika fadi akan cikinki har yayi sanadin da sai da aka miki aiki aka ciro babies?"


Sunkuyar da kanta tayi ta kasa magana don sai yanzu da yayi maganar ne ma taji ciwon abin sosai. Bata taba sanin kin da suke yi mata har yakai yanda zasu yi mata lahani ba sai yanzu.

Tasan da gayya Mu'azzam ya cilla mata ball dinnan a cikinta abinda bata taba zaton zasu iya yi mata ba. Jin shirun nata yayi yawa ne yasa Daddy yace mata "Aisha kiyi magana mana, nace ko zaki iya fada mini abinda ya faru a ranar na tarar dake a kwance cikin jini".

Girgiza kanta tayi sannan tace "a gaskiya bazan iya tunawa ba na manta". Hajiya ce ta ce "wanne irin kin manta kina nufin baki san yadda akayi kika fadi akan cikinki ba da har yay sanadin da akayi miki aiki aka ciro yaran dake cikinki, kenan kin samu shafewar tunani da bazaki iya tuna rayuwarki ta baya ba".

Nanma Aisha cewa tayi "a'a Hajiya ban samu shafewar tunani ba kawai dai na manta abinda ya faru ne a ranar". Hajiya zata sake magana Daddy yayi hanzarin cewa "kyaleta Hajiya tunda tace ta manta shikenan saukinta ai ba ita kadai bace a wurin da abin ya faru don haka kai Mu'azzam kaine babba ko zan iya sanin abin d yaru da har nazo na iske Aisha a kwance yayinda kuke tsaye akanta kai da kannenka".

Mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Mu'azzam don har ga Allah yana tsoron Daddy yasan cewa shine ya cilla mata ball a ciki duk da dai yana tunanin Daddyn yasan cewa sune shine ma dalilin da yasa ya tara su duka anan wurin.

Ganin yayi shiru ya kasa magana ne yasa Daddy ya juya akalar tambayarshi wurin Ummie, itama shiru tayi ta kasa bashi amsa haka ma Farida.

Ranshi yayi mummunan baci, shirunsu ya kara tabbatar mishida zarginshi na cewa sune sukayi sanadin da Aisha ta kwanta a asibiti.

Cikin masifaffiyar murya yace "kunsan me shirun ku yake nufi, yana nufin zargin da nake yi akanku ya tabbata don ko rantsuwa zan iyayi akan cewa kune kuka yi sanadin da Aisha ta fadi. Yanzun its either ku fada mini gaskiyar abinda ya faru ko kuma  nayi bincike na gano yanda abin ya kasance don kada ku manta ba wai ku kadai bane a wurin a ranar da abin ya faru kun kuma san Zainab bazata gaya mini karya ba. So its better you start talking right now".


Mu'azzama ne yayi karfin halin cewa "Daddy don Allah kayi hakuri wallahi tsautsayi ne",cikin tsawa yace "comeon ka fada mini abinda ya faru don bawai na tara ku anan don kuyi mini yawo da hankali bane".

A haka dai Mu'azzam ya daure ya fadi abinda ya faru sai dai yayi kokarin ya nuna cewa laifin na Farida ne don ita ta kauce bata bari Aisha ta dafa ta ba abinda yayi sanadin data kifa akan cikinta.

Gaba daya Farida rikicewa tayi jin Mu'azzam na neman ya juya laifin kanta ita kadai bayan kuma da ace bai fara jefa mata ball dinba da duk haka bata faru ba.

Sosai ran Hajiya ya baci da jin abinda ya faru. Fada sosai ta hau yi tana cewa "wannan ai rashi imani ne ku jefi mace da tsohon ciki, me kuke so ku zama ne yarannan".

Khalifa ma ranshi ya baci dajin abinda sukayi, ya rasa me ke damun yarannan wai har Mu'azzam da yake babba kuma namiji ace yana abu irin na jahilai yana biyewa su Farida.

Daddy kam takaici ne ma ya hana shi magana sai zuwa can ya ce"yanzu magana guda daya ce zanyi bazan yi tolerating iskancinku ba acikin gidana dole ne kuyi respecting matata don disresoecting dinta yana nufin disrespecting dina. Aisha da kuke gani matata ce and its a must for you to accept her as a mother, babu ruwana da wani grudges da kuke holding against her wannan damuwarku ce.

Abinda na sani shine cewa nine mai gida kuma dukkanku a karkashina kuke so dole kuyi accepting ko waye na kawo na ajjiye a cikin gidannan, don haka this should be the first and the last time da wani abu makamancin wannan zai kuma faruwa.

Abu na gaba kuma shine ke Ummie da Farida ku fito da miji auren zan yi muku tunda na lura har da kyaleku da nayi kun zaune mini a cikin gida babu aure yasaka kuke mini iskancin da kuka ga dama, don haka sai ku shirya auren Khalifa da za'ayi tare da naku za'a hada".

Kai kuwa Mu'azzam babu abinda zan ce maka don kuwa a shekarunka idan har baka tsawatarwa da na kasa dakai ba bazaka biye musu kuyi abinda kukayi ba amma kuma unfortunately kai ne kake nuna musu ko miye ma sukeyi, abu daya zan gaya maka shine bazan dauki rashin da'a a cikin gidana ba. Bazan yadda da ganganci irin wannan ba ayi terming dinshi as tsautsayi".

"sannan kuma inaso dukkanku ku bawa Aisha hakuri tare da alkawarin makamancin irin wannan bazai kuma faruwa ba". Ummie ce ta dago kai tana sharar hawaye ta ce "Aunty Aisha don Allah kiyi hakuri In Sha Allahu wani abu makamancin wannan ba zai kuma faruwa ba" ita dai Ummie har cikin ranta tayi danasanin abinda ya faru duk da dai babu ita a cikin abin da ya faru amma kuma tasan cewa ita ma tanayi wa Aisha  abubuwa.

Duk sai da suka bata hakuri sannan Daddy ya sallamesu, itama Aisha ta tashi ta koma dakinta.

UMMASGHAR.

'YA'YAN MIJIHistórias para pegar e não largar. Descubra agora