'YA'YAN MIJINa Umm Asghar
7
A haka dai rayuwa taci gaba da tafiya. Ga Aisha dai ta dada kame kanta daga shiga harkar Farida da Mu'azzam don ta lura akansu zaman gidan zai iya gagararta. Ita kuwa a yanda takejin dadin zama da Mami ga kuma ingantaccen ilimi duka biyu wato na addini da boko da take samu baza taso tayi abinda zai rabata da zaman gaidannan ba.
Ga kuma baby Ruqaiya da sukayi wata irin shakuwa da ita don mafi yawan lokuta idan tana wurin Aisha ko Mami bata yarda ta dauketa sai da kyar. To shima Daddy a nashi bangaren bai kara maganar mayar da ita gidan Hajiya ba, kodayake a yanzu duk fitinar Farida da neman rigimarta ta kyale Aisha ganin bata shiga harkarta.
A yanzu haka Aisha tana ss1 ne yayin dasu Ummie suke jss3. Tun zuwan Aisha gidan sau daya taje garinsu tayi hutu na sati uku. A wannan lokacin ma hutun take son zuwa sai dai kuma kasancewar ciki ne da Mami tsohi yasa dole ta hakura. Ko babu komai tana taimakawa Mami da hidimar gidan don zuwa wannan lokacin babu wani abu da bata iya ba a kitchen.
Mafi yawan lokuta zaka sameta ne a kitchen tare da Mami da sauran ma'aikatan gidan, abinda bazaki taba ganin Ummie ko Farida sunyi ba. Yanzu ma aikin abincin dare sukeyi ita da Mami a kitchen. Yaya Khalifa ne ya shigo kitchen din yace "sannu Mami, mezan samu wallahi na gaji da yawa ga yunwa na kwaso, yau tunda muka fara lectures tun 12 sai six muka gama without any interval".
"Sannu Yay Khalifa ai kana kokari wallahi Allah dai ya bada sa'a". "Amin Aisha nagode, me kukayi ne da rana? Yace bayan ya zauna akan kujerar kitchen din. "Favourite dinka ne wato faten doya bari na zuba maka" tace bayan ta dauki plate ta zuba mishi abincin sannan tace mishi "anan zakaci ne ko na kai maka parlour". "Bari kawai na wuce dashi Aisha nagode" yace yana mai tashi daga kan kujerar. Karbar abincin yayi ya fita a kitchen din. Bayan sun gama hada abincin ne Mami ta fita ta barta a kitchen din ta karasa gyarawa. Sosai take tausayawa Mami ganin duk da tsufan cikinta hakan bai hanata yin hidimar gidanta ba.
A daren ranar suna kwance suna bacci Mami ta shigo dakinsu ta tashi Aisha. "Lafiya Mami?" tace bayan ta tashi zaune. "Saka hijabinki ki taso asibiti zamuje" tace mata a yayin da take barin dakin. A hanzarce ta tashi ta daura zani akan kayan baccinta ta dora hijabi ta fita zuwa dakina Mami. Akwatin da Mami ta hada don zuwa asibiti ta dauka suka fita. Koda suka fita harabar gidan tuni Daddy ya juyo da mota, gidan gaba ta budewa Mami ta shiga sannan ta koma baya ta zauna.
A lokacin da suka isa asibitin karfe daya da rabi ne na dare. Suna zuwa direct labour room aka wuce da Mami, su kuma suka samu wuri anan rwception din suka zauna. Nesa sosai da Daddy Aisha ta zauna, duk sai tana jinta a takure don ita dai hakanan take jin tsoron Daddy bata taba sakewa dashi ba shima kuma bai taba sakar mata fuska ba tsakaninta dashi gaisuwa ce kawai.
Basuyi zaman awa daya ba a wurin nurse ta fito ta fada musu Mami ta haihu diya mace. Gaba daya annurin farinciki ne ya sauka a fuskar Daddy, mamaki ne ya kama Aisha don kuwa bata taba ganin fara'arshi haka ba. Ba'a wani jima sosai ba aka fito da Mami da babynta zuwa wani dakin. Bin bayansu sukayi zuwa dakin da aka kwantar da ita. Daddy na rike da baby sai faman fara'a yakeyi yana ce mata "sannu Zainab", ya dade a asibitin kafin yayi sallama da Mami ya tafi gida don a lokacin kausan karfe uku da rabi ne na dare. Daga Mami har Aisha basu wani samu yin barci ba saboda baby bata barsu ba. Sauki daya suka samu ma shine da safe da likita yazo ya dubasu ya basu sallama. Anyi sallamar babu dadewa Daddy ya shigo dakin hannunshi rike da kwandon kayan abinci. Da sauri Aisha ta tashi ta karbi kwandon a hannunshi sannanta gaisheshi. Yana amsawa ya karasa kan gadon ya zauna yana yiwa Mami sannu tare da amsar baby a hannunta. Breakfast kawai sukayi suka koma gida kasancewar anyi discharging dinsu tun kafin zuwan Daddy. Da isarsu gida yaran gaba daya suka fito suna ihun Murna. Rige-rigen karbar baby sukeyi, Mu'azzam ne ya karbi babyn a hannun Aisha ita kuma ta fito da kayansu suka shiga cikin gidan. Cikin kankanin lokaci gidan ya cika da baki 'yan barka don haka nema hutun da Aisha take bukata bata sameshi ba saboda hidima da tayi mata yawa.UMMASGHAR.
KAMU SEDANG MEMBACA
'YA'YAN MIJI
Fiksi UmumAisha yarinya ce da rikonta ya dawo hannunta Goggonta bayan rasuwar mahaifiyarta inda ita kuma ta mika ta ga matar danta. Rayuwa ta juyawa Aisha baya ne a lokacin da marikiyarta ta rasu aka aura mata mijin marikiyarta.