'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
12
A kwana a tashi babu wuya wurin Allah. Gashi har Aisha ta gama dalilin da yasa ta cewa Mami tana son zuwa gida don kuwa ta dade bata jeba. Sati biyu taso yi amma sai Mami tace tayi sati daya don bata son tana yin nesa da ita. Ba don taso ba ta amince sai don bazata iya musawa Mami ba.
Bayan kwana biyu ne ta shirya ta tafi gaya. Sosai mutanen gidan sukayi murnar ganinta. Goggo ta sauketa da fura da nono da danwaken wake da rogo mai dan karen dadi.
Sosai taci danwaken don ta dade rabon da taci. A kano basayin danwake don yaran gidan duk basa so shi yasa Daddy yace a daina yi tunda babu maiso.
Tana gama cin abincin ta haye gadon Goggo ta kwanta barci inda ba ita ta farka ba sai da la'asar. Bayan tayi sallar ne ta fita zuwa gidan yayarta Huwaila wacce ta kasance babba a gidansu haka kuma 'ya a wurin Goggo.
Da murnarta ta tareta, bayan sun gaisa ne ta kawo mata kunun aya mai dadi tasha kasancewar sana'arta ce saida kunun aya. Suna cikin hira ne ta sako mata maganar aure tace "amma dai zuwa yanzun kin tsaida miji ko don tun dadewa ya kamata ace an aurar dake".
Yake Aisha tayi tace "Yaya Huwaila kenan". Hade rai Yaya Huwaila tayi tace "ban gane da ni kenan ba, kina nufin har yanzu baki tsaida miji ba Aisha kin kuwa san yadda Baba ya damu da batun aurenki? Shiru fa kawai yayi don yana jin nauyin Hajiya bayaso ya nuna musu ikonshi akanki amma banda haka ai da tuni yayi magana akan zamanki a haka don ba so yakeyi ba ko karatun da kikayi don babu yadda zaiyi ne amma da don tashi ne da kina gama secondary school za'a aurar dake".
Gaba daya jikinta taji yayi sanyi jin cewar Baba ya damu da zamanta haka babu aure. Banda abin Baba ma dai miye abin damuwa don takai yanzu ba tayi aure ba tunda dai ba wai ta wuce lokacin auren bane bare ace ta rasa miji. Shine fa dalilin da yasa wasu lokutan bata cika son zuwa gida ba don kuwa idan tazo an dunga yi mata surutu akan rashin aure kenan.
Bata bar gidan Yaya Huwaila ba sai bayan da tayi sallar magriba taci abinci tukunna. Koda ta koma gida ta tarar Baba bai dawo daga masallaci ba kasancewar idan ya fita sallar magriba baya dawowa gida sai yayi isha. Tana shigowa gida ana yin kiran sallar isha don haka ko zama ba tayi ba dauki buta tayi alwala sanna ta gabatar da sallah.
Tana zaune akan sallaya taji shigiwar Baba. Bayan kamar mintuna biyar da shigarshi dakinshi ne ta tashi ta bishi. Da sallama ta shiga dakin sannan ta zauna akan tabarma. "Sannu Baba ina yini" tace tana mai russunawa. "Lafiya lau Aisha, kinzo lafiya" "lafiya lau Baba". "Madalla, ya wajensu Alhaji Jafarun dasu Hajiya duk suna lafiya dai ko?" tace "duk lafiyarsu lau sunce a gaisheku" yace "Masha Allahu, to ya karatunnanki babu dai wata matsala ko".
Tace "Alhamdulillahi, ai Baba harna gama ma" yace "to Masha Allahu, Allah ya bada sa'a. Sai batun aure kenan ko tunda Allah yasa kin gama karatu". Shiru tayi tare da sunkuyar da kai. "Ya kika yi shiru Aisha, ko har yanzu mijin bai samu ba" cikin sanyin murya tace "kayi hakuri Baba".
Shiru ne ya ratsa na wasu 'yan mintuna zuwa can Baba yace "kina jina ko Aishatu, ni da kike ganina bazan yi miki dole ba hakanan kuma bazan zuba miki idanu kiyi ta zama babu aure ba don haka idan har kinsan akwai wanda kika tsayar kiyi gaggawar turoshi idan kuma babu to ki tabbatar da kin samu zaki gabatar dashi dimin kuwa har ga Allah zamannan naki a haka ba sonshi nakeyi ba".
Tace "In Sha Allahu Baba bazan baka kunya ba". Daga haka suka shiga hirar duniya. Bata bar dakin Baba ba sai kusan karfe sha daya. Dakin Goggo ta shiga tayi shirin kwanciya sannan ta kwanta.
Tunda ta fita da safe yawon gaishe-gaishe bata dawo gida ba sai gaf da sallar magriba. Sosai take cikin gajiya. Ko don ta dade ba tayi yawo irin haka ba gaba daya sai taji jikinta yana mata ciwo.
A ranar da ta kwana biyu da zuwa gida wurin karfe sha biyu na rana suna zaune da Goggi, gyaran zogalen da Goggo zatayi dambu takeyi. Yarone ya shigo yace wai ana sallama da ita. Mamaki ne ya kamata, waye kuwa zaiyi sallama da ita da safennan. Ita wa ma ta sani da har za'azo wurinta.
Ganin bata da niyyar amsawa ne yasa Goggo tacewa yaron kace tana zuwa sanna ta cewa Aisha "tashi kije ki ga waye, ai ba'a san inda za'a dace ba". Kasancewar tayi wanka tun tashinta, sanye take cikin atamfar Holland dinkin riga da zani. Hijabi kawai ta saka ta fita don ganin mai sallama da ita.
Mallam Adamu ta gani zaune cikin mota. Cikin sassarfa ta karasa wajenshi, tana zuwa ki gaishe shi batayi ba ta tambayeshi lafiya. Murmushi yayi sannan yace "lafiya lau Mami ce tace nazo na daukeki" "Mami fa kace kuma lafiya Mallam Adamu ka tabbata" ta tambayeshi fuskarta dauke da mamakin jin cewar Mami tace a zo a dauketa ganin sun rabu ne akan zatayi sati daya kafin ta koma. Yace "lafiya lau kawai dai tace ne nazo na daukeki". To ina zuwa tace mishi sannan ta juya zuwa cikin gidan.
Sanarwa da Goggo tayi batun tafiyarta. Itama Goggo tarrarrabi takeyi cewa anya kuwa lafiya. Daki Aisha ta shiga ta hada kayanta sannan ta fito tayi sallam da Goggo tana cewa ta fadawa Babanta batun tafiyarta idan ya dawo. A sosron gidan sukayi kacibis da Baba, kafin tayi Mayans ya rigata da cewa "naga Mallam Adamu yazo daukarki ko, Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutanen gidan. Tace "amin Baba fatana dai Allah yasa lafiya" yace "lafiya lau kawai dai bata ji dadi bane Mamun taku amma yace jikin da sauki".
Sallam Ragusa Baba sannan ta wuce mota suka dauki hanyar kano. Hakanan taji gabanta na faduwa don haka ta fiddo da AlQur'ani daga jakarta tana karantawa. Sai da suka isa kano sannan ta rufe AlQur'anin ta mayar cikin jaka.
Suna shiga layin gidansu taga cincirondon motoci a kofar gidansu. Mummunar faduwar gaba ce ta sameta, cikin rawar murya tace "Mallam Adamu me je faruwa ne, don Allah ka gaya mini". Cikin dakewa Mallam Adamu yace mata "sai dai muyi hakuri Aisha Hajiya Mami Allah yayi mata rasuwa jiya da darea sanadiyar ciwon ciki".
Sandarewa kawai Aisha tayi a zaunen da take ta rasa gane ne kunnuwanta suka jiye mata. Wani irin kuka ne yazo mata, kifa kanta kawai tayi akan cinyoyinta tana kuka. Mami wai Maminta ce ta rasu. Mamin data tafi ta bari cikin koshin lafiya ashe bazata dawo ta tarar da ita ba. Wannan rayuwar abar tsoro ce, wato tsakanin rayuwa da mutuwa dan takin kalilan ne ( Allah yasa muyi kyakkyawan karshe, Amin).
Ta dade a zaune cikin motar kafin tayi karfin halin fitowa, gidan a cike yake da mutane 'yan karbar gaisuwa. Ta kofar kitchen tabi ta shiga cikin gidan. A parlour ta tarar dasu Hajiya da Hajiyarsu Mami da wasu daga cikin 'yanuwanta. Durkushewa tayi kawai a wurin tana wani irin kuka, mutanen wurin gaba daya suka hau bata hakuri.
Da kyar ta iya tsaida kukan tayiwa su Hajiya gaisuwa sannan ta tashi ta haya sama zuwa dakinsu. Su Ummie ne a dakin tare da kawayensu. Tana shiga Ummie ta taso ta rungumeta tare da fashewa da kuka, itama Aisha kukan takeyi.
UMMASGHAR.
YOU ARE READING
'YA'YAN MIJI
General FictionAisha yarinya ce da rikonta ya dawo hannunta Goggonta bayan rasuwar mahaifiyarta inda ita kuma ta mika ta ga matar danta. Rayuwa ta juyawa Aisha baya ne a lokacin da marikiyarta ta rasu aka aura mata mijin marikiyarta.
