'YA'YAN MIJI
Na Umm Asghar
11
Sosai takejin dadin zamanta da Hajiya. Ko babu komai tana karuwa da ita sosai ta fannin ilimi don kuwa mawuyacin abu ne kaji Hajiya ta zauna tana sakin zance barkatai. Duk wata magana da zata fito daga bakinta mai ma'ana ce ko da kuwa a cikin hira ne.Suna zaune a parlour suna kallon tashar Sunna TV wayar Hajiya dake ajiye akan tv stand ta dauki kara. Tashi Aisha tayi don ta dauko wayar. Intetnational number ta gani akan screen din.
Mikawa Hajiya wayar tayi sannan ta shige daki don ta bawa Hajiya wuri ta amsa wayarta ga alama mutanen saudia ne suka kirata.
Tayi kusan mintuna goma da shiga dakin sai ga Hajiya ta shigo ta mika mata wayar tace mata "karba Maminku ce akan layi". Da sallama ta amsa wayar sannan tace "Mami ina yini, ina Zainab da Rukieta?" "Lafiya lau Aisha, ya gida" Mami ta amsa mata. "Gida lafiya lau Mami, yasu Ummie da Farida dasu Ya khalifa. Wai yaushe zaku dawo ne Mami wallahi sosai nake cikin kewarku". "Muma muna kewarki Aisha, ga yaranki nan sun hanani sakat ni kaina na matsu mu dawo ko na huta kullum cikin rabon fada nake".
Dariya Aisha tayi tace "ayya Mami kice idan kuka dawo sai na basu purnishement tunda suka wahalar mini da Mamita".
Sun dade suna hira da Mami kafin sukayi sallama. Tashi tayi ta kaiwa Hajiya wayarta sannan ta zauna suka cigaba da kallon da sukeyi. Ji tayi Hajiya na magana don haka ta dawo da hankalinta gaba daya wurin Hajiya. "Na'am Hajiya me kikace" tsaki Hajiya tayi sannan tace "fadan Maminku nakeyi wai gaya mini takeyi ta gaji hidimar yara tayi mata yawa. Dama ni tunda suka yi maganar tafiya Ummara da yara banji sun saka dake ba shiru na musu ban yi magana ba tunda sun riga sun gama tsarinsu amma ko don ki tayata da hidimar yara ai da sun tafi dake. To shi Jafaru wani irin baudadden hali gareshi abinda yasa kanshi shi yakeyi ni kuwa ban cika son shiga sha'anin gidanshi ba. Ita kuma Zainab tsoronshi takeyi duk abinda yace ko baiyi mata ba bata iya musa mish. Yo dama wadannan malalatan yaran nata me suka iya bare har su tayata da rainon yara, su da basa iya tsinanawa kansu komai bare suyi wa wani".
Aisha dai shiru tayi tana sauraren Hajiya ba tare da ta tanka mata ba.sai dai cikin ranta mamaki ne takeyi wao kenan har Hajiya ma tasn halin Daddy na rashin son mutane su rabeshi, sai dai kuma ba abin mamaki bane tunda itan mahaifiyarshi ce. Ita kam ta sani ko ita karfin zamanta a gidannan Mami ce da don tashi ne da tuni ta dade ba barin mishi gida.
A ranar da tayi sati biyu a gidan Hajiya ya kama washegari su Mami zasu dawo ta shirya ta tafi gidan don ta gyara duk da dai akwai masu aiki a gidan to amma gyaran sama gaba daya aikinta ne 'yan aiki basa gyara musu dakunan barcinsu.
Aikin da tayi ya dauketa tsawon lokaci kafin ta gama. Gidan Hajiya ta koma ta kwana gari na wayewa ta koma gidan din ta shirya musu abinci. Fried rice tayi da coleslaw hade da peppered chicken sai tuwon alkama miyar kubewa busashiya da tayi saboda Daddy yafi son abincin gargajiya fiye da komai.
Karfe biyar da kwata na yamma su Mami suka shigo harabar gidan tare da Mallam Adamu da yayi kanin yini a airport yana jiran saukarsu. Aisha najin tsayuwar motarsu ta fito da sauri tana murna.
A guje Ruqaiya da Zainab suka taho suka rungumeta. Ita ma farincikin ganinsu duk ya cikata. Rike hannuwansu tayi ta karasa wurinsu Mami tana yi musu sannu da zuwa. Gaba dayansu suka dunguma zuwa cikin gida. Dukansu a parlour suka zauna sai Mami da Daddy ne kawai suka haya sama.
Ruwa da lemuna Aisha ta kawo musu tana yi musu sannu. Tana zama Zainab da Ruqaiya suka sakata a gaba da labari. Farida da Ummie kam kujera kowaccensu ta hau ta kwanta yayinda Yaya Khalifa da Mu'azzam suka wuce dining area don cin abinci.
Sai bayan kusan minti talatin sannan Mami ta sauko. Ga alama wanka tayi don ta canja kayan jikinta zuwa doguwar rigar atamfa. Table din ta nufa tana bude kwanuka.
Tashi Aisha tayi ta nufi table din. Durkusawa tayi ta gaida Mami tare da yi mata barka da dawowa. Bayan sun gaisa ne Mami kece mata "sannu a kokari Aisha Allah ya biyaki, duk ke kadai kikayi wannan aikin?" Dariya kawai tayi tace "amin Mami". Hada abincin Daddy Mami tayi sannan ta dauka ta koma sama ga alama dai yau a saman zaici abincin.
Da dare ne bayan anyi sallar isha'i Aisha taja Zainab don ta rakata ta gaida Daddy. A parlournshi na sama ta same shi yana kishingide akan doguwar kujera. Ganinta baisa ya tashi zaune ba. Durkusawa tayi ta gaisheshi tare da yi mishi barka da dawowa.
A dakile ya amsa mata gaisuwar da lafiya. Tashi tayi ta fita ta bar Zainab da tun shigarsu parlourn ta nufi wurin Babanta ta zauna.
Washegari da safe ne Mami ta bata tsarabarta. Dogayen riguna ne masu kyau guda biyu daga Mami sai wani agogon hannu inji Daddy. Sosai Aisha tayi murna da tsarabar da aka bata.
Ruqaiya da Zainab ma matetial suka bata sai Ummie da ta bata kayan bacci riga da wando. Yaya Khalifa kuma ya bata takalmi sai Mu'azzam da ya bata agogo, ta tashi da agogi biyi kenan.
Farida kam ko kallonta batayi ba bare kuma tasaka rai da tsarabarta. To ita dinma bata saka rai tunda dai tasan tsakaninsu da Farida, amma kuma duk ma'aikatan gidan babu wanda batayi wa tsaraba ba har masu gadi.
UMMASGHAR.
ESTÁS LEYENDO
'YA'YAN MIJI
Ficción GeneralAisha yarinya ce da rikonta ya dawo hannunta Goggonta bayan rasuwar mahaifiyarta inda ita kuma ta mika ta ga matar danta. Rayuwa ta juyawa Aisha baya ne a lokacin da marikiyarta ta rasu aka aura mata mijin marikiyarta.