BABI N A TAKWAS

438 46 0
                                    


           'YA'YAN MIJI

Na Umm Asghar

             8
Tun bayan da Mami ta haihu gidansu bai rabu da jama'a ba. Don Aisha ma ko makaranta bata samun zuwa saboda hidima da tayi mata yawa. Ga aikin jego ga kuma hidimar Ruqaiya da kacokam ta dawo hannunta.
A ranar da akayi kwana biyar ne da haihuwar da safe Aisha na zaune a dakin Mami tana shirya kayan baby data wanke Mami ta shigo cikin dakin dauke da baby. Kwantar da ita tayi akan gado sannan tace da Aisha "idan kin gama shirya kayan kawo mini kunu sai kizo ki janyo mini wancan akwatin". Bayan ta gama shirya kayan ne taje kitchen ta damowa Mami kunun gyada sannan ta kawo mata. Akwatin data ce ta janyo mata tare da budewa ta fito da kayan ciki. Laces ne guda uku sai atamfar super holland guda hudu da voiles guda uku. Mami tace "miko mini na gani" tashi tayi ta mika mata kayan. Dagawa Mami tayi ta kalla sannan tace "wai nan kayan fitar suna ne Daddy ya mini sai kace wata yarinya, nikam ai na gaya mishi babu wani taron suna da zanyi".
Aisha ta kara daga kayan ta kalla sannan tace "ai kuwa dai Mami kayan sunyi kyau, Allah ya sakawa Daddy da alkhairi, amma Mami meyasa bazakiyi taron suna ba". Dariya Mami tayi tace "kayya Aisha taron suna ai na yara ne, haihuwa ta biyar ni kuwa wani suna zanyi, don wani abu irin na Daddy ma wai baby sunana ya saka mata nayi-nayi dashi ya saka sunan Hajiya yace a'a".
Cikin fara'a sosai Aisha tace "Allah ya rayata, kuma Mami me za'ace mata?" "Zainab dinta zaku kirata don banason boye sunannan" a cewar Mami. "Ina Ruqaiya ne duk yau ban ganta ba" Mami ta tambayeta. "Tana wurin Lami tun bayan dana mata wanka ta dauketa ta goyata to inaga bacci takeyi tunda kikaga shiru bata kawo taba". Aisha ta amsa mata.
A ranar suna ne baby taci sunan Mami wato Zainab. Kasancewar Mami ba taro takeyi yasa gidan bai cika da mutane ba amma duk da haka 'yanuwa na jiki duk sunzo don haka aiki yayi wa Aisha da sauran ma'aikatan yawa don sai faman dora abinci sukeyi suna saukewa. Ita dai Aisha har ta matsu dare yayi ko ta samu ta kwanta ta huta.
Bayan suna ne da kwana biyu suna zaune a parlour gaba gayansu yaran gidan suna hira Mami kece mata idan anyi hutu sai ta shirya taje garinsu ta kwana biyu. Sosai taji dadi sai dai kuma tana tunanin udan har ta tafi yadda hidima zatayiwa Mami yawa, bata dai yi magana ba don kuwa tana kewar Babanta zataso taje ta ganshi.
Murmushi tayi sannan tace "to Mami nagode Allah ya kara girma". Kallonta Ummie tayi sannan tace "umh Aunty Aisha sai murna kikeyi zaki tafi ki barmu ko tausayinmu bakya ji bayan kinsan zamuyi missing dinki sosai". Tsaki Farida tayi hade da tabe baki tace "kedai zakiyi missing dinta nikam da zamanta da rashinshi duk daya ne a wurina don rayuwata nakeyi tamkar babu ita a cikin gidannan".
Murmushi kawai Aisha tayi ta dauke kai. Ita dai ta rasa abinda ta tsarewa Farida a cikin gidannan don ko magana idan har ba ita tayi mata ba batayi mata shima kuma ba lallai ne ta amsa ba. Wannan kuma baisa ta daina yi mata magana ba koda kuwa kullum ta mata bazata amsa ba.
Tun bayan da Mami tayi mata maganar zuwa gida ta fara shiri don ta fitar dakayanta da yawa da zata bayar a garinsu wa 'yanuwanta haka ma kuma Mami ta hada mata kayan bayarwa nabyara da yawa da zata rabar acan. A daren da zata tafi ne tana zaune a tsakar dakinsu tana shirya kayanta a cikin akwati Mami ta shigo hannunta rike da bakar kedar viva. Zama tayi a bakin gadon sannan ta mika mata ledar , jarba tayi tana kallon Mami da alamar tambaya a fuskarta. " Na Babanki ne da kuma goggonki wato matar Babanki ga kuma wannan ki kaiwa babanki inji Daddy sai kije kiyi mishi godiya" ta mika mata envelope.
Russunawa tayi hadi da karbar envelope din tace "nagode  Mami Allah ya saka da alkhairi ya kara budi". Bayan data gama hada kayan ne ta nufi parlour Daddy don tayi mishi godiyar alkhairin daya yiwa mahaifinta. Daga bakin kofa ta tsaya tayi sallama, sai bayan an amsa ne tare da bata izinin shiga sannan ta shiga. Durkusawa tayi ta gaisheshi sannan ta mishi godiya ta tashi ta fita. Ruqaiya dake wasa a parlour ta taso ta biyota tana rigimar sai ta goyata. A daren ranar dai baccin Aisha rabi da rabi ne don dokin zataje taga Babanta.

UMMASGHAR.

'YA'YAN MIJIWhere stories live. Discover now