page 1

2.3K 120 3
                                    

0⃣1⃣

~*YAR AIKIN GIDA NA*~
(ta zama matar miji na)

*NANA AICHA* ce

Sadaukarwa gareki, my beautiful dear, my little sister *official marcy*

Bissimillahir rahamanin rahim da sunan Allah me rahama me jin kay.... Ina rokon Allah da Ya bani ikon fara littafin nan lfy in gama lfy.....
Labari na kir'kirarrane ni na tsara shi da kay na, banyi shi ba dan cin zarafin wani ba...
kuma ayi hakuri dani sabida shine littafina na farko.....
Jaruman littafin
*Habib*
*Hafsat*
*Samira*

Inna suwaiba ce ke kallon 'yar ta tana cewa

"Samira tun d'azu ina cewa me kike jira baza ki tashi kije gidan aiki ba, kinsan aikin nan naki da shi ne muke samun abincin da zamu ci"

Samira ta zumb'ura baki tace "Wlh Inna ni gaskiya gidan aiki zan sauya saboda kullum Alhajin gidan baya da aiki sai kallona, ni kuma ina tsoron wanan masifaffiyar matar ta shi"

Inna tace "Kiyi hakuri d'iyata wlh da ina da yadda zanyi da nayi kin bar zuwa aikin nan sai dai babu yadda na iya ki cigaba da hakuri wata rana sai labari kinji d'iyata"

Samira ta tashi tayi wanka ta tsaftace jikinta ta wanke kwanon abincin da take tahowa da shi tace "toh Inna ni na tafi"
Inna suwaiba tace "Allah ya kiyaye hanya Samira ki gaida su"

Samira ta amsa da "Ameen" tana yin gaba.

Tafe take bisa hanya a nutse tana kallon dun yara yan makaranta da suke wucewa, tana sha'awar school sosai sai dai ba hali tin bayan rasuwar Mahaifinta kulawarta ta koma ga mahaifiyar ta shiyasa tabar zuwa school saboda ita ke zuwa aiki da yake Inna ba tada isashen lfy shiyasa tabar zuwa, amma Allah yayi ta me kokari saboda tana *5e*( js2 kenan) tabar school, Tana tafya tana tunani har ta kai gidan aikinta gidan Alhaji Habib dan canji da uwar gidan shi hajiya Hafsat.

Tana zuwa ta fara aikin ta kamar yadda ta saba a koda yaushe tanayi tana mita, "mace har mace amma bata san ta gyara gidan ta ba said dai kullum yar aiki tayi mata komi, ni wlh matar nan ta far isata se son jikin tsiya ga masifa.

Kuma yanzu ta iya zuwa tayi mani jaraba tace ban yi dai-dai ba , Allah dai ya rabani da gidan nan lfy" (😍 ameen samira )

Nan dan nan ta share palour ta goge ta feshe shi da turare me dadin kamshi, sai gidan ya fito tsaf gwanin kyau. tana gamawa ta aza abincin rana shinkafa da miyar yakuwa zata yi, da yake ta kware wajen iya girki yarinya ce karama amma girki ta iyata sosai sai dai abinda bata taba gani ba.

Tana gamawa ta kwashe abincin ta jera shi saman dinning ta wanke tukunya tayi gaba saboda bata so matar gidan ta tadda ta ta sanya ta aiki kasancewar ita kuma tana sauri ta je gida taga innar ta. Nan da nan tayi ta gama ni kuma na lab'e bayan kofar ta rufe da ni sabida ina son ganin wanan matar gida😅

______________

Zaune nake ina jiran isowar mutanen gidan. Ina nan labe se naga mai gadi ya bude get wata mota yar madaidaciya ta kunno kai cikin gidan, tana gama parking sai naga wasu yara kanana sun fito daga cikin mota su biyu mace da namiji ina nan zaune se naga wata mata black beauty ta fito daga cikin mota rataye da jaka kalar kayan dake jikin ta , hatta takalmi kala guda ne, nace yayi dai matar dan canji dole👌🏻

Wash typing wahala😔😔😔😔😔

Ina jiran comment in ku

YAR AIKIN GIDANA ( ta zama matar mijina)Where stories live. Discover now