"Ayyiriri!!! An daura !!! Najma ta zama matar Jamilu Allah ya kawo kazantar daki." Cewar wata yamushashshiyar tsohuwa bayan ta rangada guda.
Hawaye ne ya kuma silmiyowa Amaryar a karo na ba adadi yayinda wata mata ta rungumeta tana me share mata cikin tausayinta.
"Najma ba za ki daina kukan nan ba ne wai ?kowa da kike gani hakuri yake da lamarin duniyar nan,Aure fa ibada ne,Aljannarki za ki nema,kika san ko a sanadiyyar Aurenki da Jamil ki shiga Aljanna?Kila Mahir ba alheri bane a gareki..."
Tun kafin ta karasa Najma ta yi saurin katseta"Haba Mami sai in ga kamar ba kya sona,duk wanda aibata Ya Mir ba masoyina bane na hakika,kuma zuciyata gaya min take ba alheri zan tarar ba a gidan Jamil."Kafin Mami ta qara yin magana, wayarta ta dau ruri, amsawa ta yi tare da yin sallama.
"Ki turo min Najma yanzu ta sameni a parking space za ta gaisa da abokaina."
"To Alhaji ka ma samu ka rarrasheta" Ta amsa masa tare da kashe wayar.
"Tashi ki dan gyara fuskarnan taki, duk kin bi kin yi ja abinka da farar mace, farar mace alkyabbar mata farar mace Lantarkin gida. "
Maimakon ta yi murmushin nan nata mai tsada da ta ke yi duk sanda aka mata irin wannan kirarin , wani kukan ta kuma fashewa da shi sakamakon tunowa da Ya Mir dinta da tayi. Shi kadai ne yake mata wannan kirarin lokacin da yayyenta suke kiranta da Mayya ko fatalwa saboda haskenta.
"Yau na ga ta kaina wai so kike nima in sa ki a gaba ne nima in fara kukan?Tun dazu na ke cewa ki yi shiru haka kin ki. " Mamin ta fada tana Saka kuka itama.
Saida suka share Kamar 20 minutes sannan suka dakata, ba wai kuma dan sun gaji ba sai dai hanzarinzu da Alhaji ya katse.
"Kin kyauta Suwaiba ko in ce kun kyauta, yanzu fisabilillah sa ta kika yi a gaba ki ka biye mata kuna kuka kamar Allah ya aiko ku? Kin barni da manyan baki suna ta jira, kema kin san na yo gayya duba ga wannan ne karo na farko da zan aurar da da shine kike nema ki kunyata ni da girmana, To ba zan lamunta ba"
"To ba ita ba ce ta ke ta kuka ba tun dazu? "
"Yasashshen zance, Suwaiba ba wancan azumin kika yi 50 ba? Sai ka ce ba ke kika haifi su Auwalu ba, Haba ki girma don Allah mana. "
"Ke Baturiya tashi ki je ku gaisa da abokaina kinji, suna ta tambayarki danma dai ba kya laifi da sun dade da yin zuciya. "Baban nata ya fada cikin zolaya sai dai ba ta ko kalleshi ba, tashi ta yi ta gyara lafayarta mai shegen tsada da ta zauna cas a jikinta, ba karya ba don rashin annurin fuskarta ba da an kirata da amarya ta bugawa a jarida.
Sun gaisa da abonkan baban nata kama daga abokan kasuwancinsa har zuwa mai masa gyaran mota don ba karya ya yi gayya.
"Abbuna ka raka ni gida don Allah ba zan iya tafiya ni kadai ba. "Najma ta rada mai cikin shagwaba da sabuwar muryarta, to sabuwace mana tunda muryarta me sanyi ce sabanin ta yanzu da take a dashe.
"Kin dai ki ki girma Baturiya yanzu fa ke matar aurece, wannan shagwabar a yi reserving wa Jamil. " Abbun ya kuma tsokanarta gami da tashi daga kan tabarmar.
Tana jiyo abokanshi na cewa ta yi shagwabarta Ta gama yau ne na karshe sai dai ita ba wannan ne damuwarta ba, abubuwa biyu ne yanzu a gabanta, matsananciyar faduwar gaban da take ji da kuma ciwon cikinta da ya dawo bayan ta samu ya lafa, ko kafin ta kara wani tunanin a bude gate din gidansu da karfi an shigo a guje.
Abubuwa uku suka daki zuciyarta a lokacin, Tausayinsa, Tsanarsa uwa uba kuma tsananin sonsa.
Ta ji Tausayinsa ne saboda daga jiya zuwa yau ya kuma zabgewa, ya rame rama ba ta wasa ba, duk da yana da duhu, ya kara duhu sosai ga alamin rashin barci a tattare da idanunshi.
Tsanarsa ko da ta ji saboda shine silar halin da suke ciki ne, yayinda sonsa ko dama wajibi akanta kamarma da shi aka halicceta.
Ko kafin ta fito daga duniyar da ta shiga ya kuma sa ta a wata duniyar.
"I LOVE YOU 'KANWATA 'YAR FARA WALLAHI KO YANZU I'M READY TO MARRY YOU" Ya fada cike da wani abu mai kama da hope.
"YAYANA 'DAN BAKI KA MAKARA NA RIGA NA ZAMA MRS JAMIL. " Najma ta fada da wani murmushi mai ciwo mai cike da tausayinsu.
"Sai da na gayama ai da kazo kafin biyu da kila labarin ya canza Ya Mir. "
"Bani da lafiya Naj Naj jiya bayan mun rabu da kyar na je gida ba ki ga ko kaya ban canza ba? "
"Na yi tunanin in na aurar da ke ga wanda ke son ki ko da ke ba kya sonshi a sannu za ki so shi, ban taba tunanin Mahir na son ki da aure ba dukda ina da yakinin zai kula da ke, na zaci ke kadai ke haukan sonshi duba ga bai taba nuna min ba balle a kai ga ya gayamin, wallahi ko da yau ya zo min da zancen,ni mai bashi ke ne,Kaico Kaico, ina ma ina ma, ina ma ina da damar gyara wannan kuskuren."Abbu ne ya yi wannan furucin cike da nadama da tausayin halinda yaran nashi ke ciki."Ina, son Najma Abbu ka taimakeni ba zan iya rasata ba. "
"Na fi ka sonta Mahir tunda har na kai ga aurenta, if you may excuse me ina son in tafi da matata. "Jamil ne ya fada cike da kishi da wani murmushi me ma'anoni da yawa ciki kuwa harda irin 'na ci ka gasa dinnan'.
"Ah Jamil ka karaso, dama yanzu na ke so in ce ta kara kintsawa ku zo ku tafi. "Daddy ya fada da dan ya'ken da ya samu ya kakalo wanda ya fi kuka ciwo.
"Eh Abbu na karaso, Kano zuwa Katsina da 'Yar tafiya kuma dole zamu biya gida ta gaisheda su Baba." Jamil ya amsa shi cike da girmamawa.
"To Allah ya yi muku albarka, don Allah Jamil ga amanarta nan na san dole ka fuskanci kalubale daga gurinta amma ina so ka kara hakuri da ita. "
"Babu komai Abbu hakuri ya zamar min dole tunda ina son ta Nagode da halaccinka mai yawa a gareni. " Jamil ya amsa masa ba tare da ya karbi amanar ba even though it didn't go unnoticed by Najma da Mahir.
Tunda Jamil ya kira Najma matarshi, Mahir bai kara sanin inda yake ba, juyawa ya yi ya kama hanyar fita ba tare da ya ma sani ba yayinda Najma ta rungume Babanta tana wani irin kuka na ban mamaki.
Tafiya yake ba tare da ya san inda ya ke sa kafarsa ba, bai lura da cewa wari da wari ya sa ba, bai lura da ababen hawan da ke kan titi ba, tunani yake, tunanin rayuwarsu ta baya mai cike da abin tausayi,haushi dariya, Kuka, sadaukarwa da dai sauransu. Yau gashi wata kaddara mai karfi ta zo ta raba su, ba zai manta ranar da suka fara Haduwa ba, ranar da aka haifeta kusan shekaru 18 baya,ranar sallah karama.
Assalamu Alaikum, ku yi comments on each line 'yan uwa, sannan votes dinku ma ina maraba da su.Ga first chapter nan what do you think, Me kuke tunanin ya raba Najma da Mahir? Kuna ganin akwai hope ko kuwa duk su hakura? Na san aikin gama ya gama but who's in support of :
#Najmil?(Najma and Jamil)
And who's in support of
#Najma?(Najma and Mahir)
Tafiyar mai nisa ce...Amma a sannu a sannu...

YOU ARE READING
Najma da Mahir
Roman d'amour"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...