"Malam ka ringa kallon gabanka in kana tafiya mana, saura 'kiris in bugeka, ina ta horn baka ji ba, ban shirya azumi sittin ba fa, tohm. " wani mutum ya fa'da bayan ya zuro kanshi ta window din motarshi.
Wannan maganar ce ta dawo da Mahir daga duniyar tunanin da ya tafi. lokacin ne ya farga da cewar babu takalmi 'daya a 'kafarshi. Ya waiwaya baya don neman takalmin, ya ci sa'a kuwa ya hangeshi.Ba laifinshi bane, laifin zuciyarshi ne da ta kai shi ta baro, ta fara son Najma ba tare da ta yi shawara da shi ba, bayan ta san ba shi zai aureta ba.
Ya dafe kanshi bayan ya zauna akan wani dandamali yana tunanin yaushe rayuwarshi za ta dawo daidai? Ya san ya rasa farin cikinshi bayan rasuwar mahaifiyarshi, sai dai kuma bai san asalin tashin hankali ba sai da Babanshi ya auri Zuwaira.
Farkon auren da ke makira ce, sai ta ringa nuna tana san shi, ta fifita soyayyarshi akan ta 'yar ta 'Anisa' da ta dawo gidansu da zama. Dukda 'karancin shekarunshi a lokacin, ya san fuska biyu ce da ita. Lokacin da ta tabbatar ta sami yardar Ahmad sai ta fara tsiro da sharri kala-kala, tun Ahmad baya yarda har ya fara yarda.
"Alhaji mai zai sa ka ware ma yaron nan wadansu kudade ne ko duk sati ne ka ringa bashi, bana so ka dauka ko zan 'kala masa sata ne, amma sau uku ina kamashi yana 'daukar min ku'di ba da sani na ba, ka ga amana ne a hannu na, in tarbiyyarshi ta 'baci ni za a zaga. "
"Alhaji anya ba zan hana yaran nan kallo ba? Ka san shi abin yaro sai ana hadawa da dabara, ice tun yana 'danye ake tan'kwara shi, jiya Anisa ta ke ce min wai ta ce ya kai mata cartoon ya 'ki wai wani American film zai kalla, a ce a shekarun Mahir har ya san kallon film 'din turawa... " da ta ga kamar bai yadda ba don ya san Mahir sai ya yi sati bai kunna TV ba, sai ta 'kara da:
"Har da zagi ta uwa ta uba 'dan nan ya min wai ni ba uwarshi ba ce, in je can da agolar 'ya ta in fita a harkarshi. " Ta fa'da tana 'ka'kalo hawayen karya.
Da Irin wa'dannan maganganun ta sami nasarar rabashi da baban nashi na 'dan wani lokaci kafin ta raba su, rabuwa ta har abada.
Yana isa gida mai gadi ya sanar da shi, matarshi Anisa ta ce a gaya masa ta tafi birthday 'din 'kawarta,anjima wai ya yi mu su takeaway a restaurant din da suka saba yi. Sai lokacin ma ya tuna yana da aure, da za a tambayeshi me ya sa ya yi auren ba zai iya fa'da ba, ya san dai yana da aure, kuma ba jin da'dinshi ya ke ji ba.
Ya shiga gida yana mai yanke hukuncin da yake ganin is the best for him, sai yi nisa da gida kawai, zai bar 'kasar baki 'daya maybe hakan zai sa ya manta da Najma, zai sa ya yarda Najma ta mai nisa, ba tashi ba ce, ta Jameel ce.
Ya nemi biro da takarda yana mai rubuta mata wani sa'ko ,Sannan ya 'dauko travelling bag 'dinshi ya ha'da wasu kaya a ciki, ya lalubo international passport 'dinshi yana tunanin wace 'kasa zai tafi, zuciyarshi ta gaya mai 'Cyprus '.
Yana zura passport din ne a cikin wani aljihu ne ya ga wata takarda a ciki, ya 'dauko da niyyar karantawa zuciyarshi na dokawa, rubutun Daddyn shi ne a jiki,"I am Sorry " kawai aka rubuta a jiki sai date din ranar da aka rubuta wasi'kar; 15/03/2010. Da ya yi tunanin sai ya ga ana kwana biyu baban nashi ya rasu ya rubuta mai, ko me ya ke nufi da 'I am Sorry ' din? Ya tambayi kanshi yana mai addu'ar Allah ya ji'kan iyayenshi.
Bayan ya gama ha'da kayan nashi ne, ya kira Antynshi Salma.
"Hello Antyna. " Tana 'daga wayar ya fa'da cikeda shagwa'ba.
"Mahir kenan, sai yau aka waiwaye mu? " Ta tambaya tana jin sanyi a ranta, za ta iya rantsewa ya fi shekara bai nemeta ba, tun bayan da ya yi aure ya juya mata baya, ranar da yayanta ya rasu ne ta san ya ce mata 'Ina kwana? ' bai jira ta yi mai ta'aziyya ba, shima kuma bai yi mata ba ya ka'de rigarshi ya tafi.
"Ina wuni? Ya su Aslam? Ki sha kuruminki, yau 'dinnan ina tafe,ki yi ma Uncle magana ya taimaka ya shiga ya fita in koma Cyprus da zama ko PhD ne sai in yi, wallahi Antyna, iskar Nigeria ta yi min ka'dan... "
"Kai Mahir lafiya kuwa? Ko wani abin ne ya sami Anisan? " Ta fa'da a ru'de sai a lokacin ta yi noticing ru'dani a muryarshi.
"In na iso zan miki bayani for now a fara processing tafiyata Cyprus Antyna. " ya katse wayar yana daukan jakarshi har lokacin Anisa bata dawo ba, ya san kuma Mahaifiyarta Zuwaira ma bata nan.
***
Bayan Mahir ya bar gidan ne aka shigar da Najma gida, Mami ce ta kuma kintsa ta ta yi mata nasiha sosai, sannan Alhaji Yunusa ya yi umarnin ango ya tafi da amaryarsa, a cewarshi bai yarda da wannan bidi'ar kai amaryar ba. Da 'kyar aka 'ban'bareta daga jikin Mami, haihuwarta ce kawai Mami bata yi ba, amma tun tana shekara biyu bayan Sumayya ta auri Dr ri'konta ya dawo gurin Mami, in ba ka sani ba ma ba za ka san ba ita ta haifeta ba. Ana kaita dai gidan mahaifiyarta da take kira da 'Maama' akai-akai.Tafiyar minti goma ce ta kai su gidansu Jamil 'din, gidan da 'Maama' take a matsayin mata ta biyu, uwar gidan ce ta haifi Jameel kuma suna kiranta da 'Umma'.
Shigar da ita aka yi falon Dr, yana zaune da manyan kaya da travelling bag a kusa da shi, da alamun dai tafiya ya ke shirin yi.
Bayan ta gaishesu ne, aka 'dora da wa'azin dai da aka saba yi,sannan ya ce musu wani muhimmin aiki ya sameshi a Cyprus, a ranar zai tafi, daga can sai ya biya Denmark ya taho da Umma, ta tafi can ganin 'kanwarta da take zaune a can da ta haihu. Bata ma san wadda Jameel 'din ya aura ba, saboda auren a cikin gaggawa aka yi sannan cewa ta yi wata biyu za ta yi a Denmark 'din, da Dr ya matsa mata ta hau masifa, tun lokacin da ya auri Sumayya ta zama wata mara mutunci, bayan ta tafi da ta ci wata 'daya sai Dr ya matsa mata da kira akan ta dawo,ta tubure ta ce ba ta san zance ba, da ya isheta ta canza layi, sai ta ji kewar 'ya'yanta take kiransu da sun gama waya ta kuma canza wani layin. Wannan dalilin ne ya sa da auren Jameel ya taso bata san wasu details sosai ba, ta dai san sunan wadda zai aura Bilkisu, kuma tunda 'dan nata na sonta shi kenan, in ta dawo ya kawota su gaisa. Wannan kenan.
Sai da suka yi la'asar suka kama hanyar katsina inda gidan Jameel 'din yake, ciwon cikin nata bai lafa ba, sai ma 'karuwar da ya yi, tun tana daurewa har abin ya ci tura ta fara ciccije baki tana mutsu mutsu.
"Ke lafiya? " Jameel ya tambaya cikin izgili bayan ya yi noticing state 'din da take ciki.
Ta yi mamakin yadda ya yi mata magana, wai sunan mijinta ne da aka daura musu aure a rana-ranar.
"Cikina" kawai ta iya ce mai kafin ta fara kuka, ta yi mamakin jin hawaye na bin fuskarta, ta zaci sun 'kare.
"Mtsww yanzu ya fara? " ya kuma tambaya a hasale.
"Tun da safe" ta bashi amsa a sanyaye.
"Mtsww aikin banza, kina gani 'dazu muka je gida, ba sai ki gayawa Uwarki ta yi wa Baba magana ba, da ya baki magani ai, ni yanzu sauri nake ba zan iya tsayawa neman wani magani ba, ki daure in mun isa gida akwai Chemist a kusa da mu kya je ki siyo. "
Ita dama bata ce ya siya mata magani ba ai, bata bu'katar wani magani, da Ya Mir 'dinta ne ya san me zai mata, zai je ya hado mata tea mara Sugar ne, sannan ya tambayeta in tana da Pad, tun tana kunya har ta daina, in bata da ita zai je ya siyo mata, wataran har kuka yake yi in ya ga halinda take ciki.
Ba zai fasa biyo mata zuwa Sallahr juma'a ba,dukda ba Sallahr za ta yi ba, zai taho mata da Sallayar da siyo mata lokacin da ya je Hajj, zai tsaya ta shirya sannan su 'dau hanya su tafi masallaci, suna tafe suna zikiri, ko tilawa ko suna karanta Suratul Kahf. Da tare da yayyanta da Abbu suke tafiya, sai dai fa kafin su je su dawo za ta yi kuka wajen sau biyar, daga mai ce mata mayya, sai mai dukanta, duk haushinta suke ji wai saboda ta zo ta 'kwace musu soyayyar iyayensu."Bana son hayaniya wallahi, ki min shiru Allah ko yanzu in saka ki a motar haya. Ki bi kin cika min mota da kuka. " Muryar Jameel ta katse mata tunani, kafin ta kuma fadawa wata duniyar tunanin, tana tunano rayuwarsu ita da abin 'kaunarta ,Rayuwar Najma da Mahir.
Jameel dai ya fara nuna true colour 'dinshi, to me ya sa ya aureta?
YOU ARE READING
Najma da Mahir
Romance"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...