*17*

70 8 0
                                        

"Ka ci na kuɗinka wallahi, kar ka ƙara ɗaukar min cake ɗina."

"Cake ɗinki ko na surukarki,?" Ya tambaya yana ɗaga gira bayan ya gutsiri lallausan cake ɗin.

"Whatever" ta faɗa tana juya ido.  Wani abu da ta lura yana burge Jameel ɗin.

A kwana shida abubuwa da dama sun faru, ta yi kuka kuma ta roƙi Allah ya kawo mata mafita daga irin tsaka mai wuyar da ta tsinci kanta a ciki. Kuma wani ikon Allah sai ta fara ganin canji a tattare da Jameel ɗin, da fari ta ɗauka wani salon ɗaukar fansar tashi ne, don akwai lokacin da suka shaƙu har suka fi haka ma, lokacin da a tarihin rayuwarta ba lallai ta manta shi ba; zuwansu Gumel bikin ƙanwar Umma. To amma a  kwanaki biyu da suka wuce  ya goge mata wasuwasinta.

A parlour ya sameta bayan ya dawo daga rakiyar abokinshi Muazzam. Idanunta na kan TV amma tunaninta baya wurin. Gyaran murya ya yi har sau uku amma ba ta ji shi ba, sai da ɗan yi tapping kafaɗarta sannan ta dawo daga duniyar tunanin da ya faɗa.

"Ka yi haƙuri ban ji shigowarka bane"

"Don't mind, magana nake so mu yi in kina da lokaci." Ya jawo ɗan ƙaramin stool ɗin da ke gefe kaɗan da kujerar da take zaune ya zauna a kai yana  fuskantarta.

"Eh ba komai" ta amsa shi da ɗan mamaki a muryarta.

"Da farko zan fara da baki haƙuri akan shigowata rayuwarki ba a son ranki ba, na kuma zama silar rabuwar masoya biyu, na yi sanadin samar da rauni a zuciyoyinsu... Na roƙe ki da Allah Najma, ba don ni ba, ba don halina ba ki yafe min " Ya ɗan murza goshinshi alamar frustration, maganganun da suka yi da Muazzam abokinshi na dawo mishi kai.

"Jameel duk wanda ya biyewa duniya wallahi ya yi asara domin ko ba komai ba ce, ka duba ka ga yadda ƙaddara ta yi da Bash, mutum mai izza da iko, yau ya tashi babu ƙafa, daga ƴar tseren mota ya yi hatsari, shi kenan kuma. Duk ji da kan da yake yi da wulaƙanta na ƙasa da shi da yake yi yanzu babu. Shi ne ma abin tausayi yanzu. To yanzu me amfanin ɗaukan duniya da zafi... "

"Na biyu, zan so kaina a karo na biyu, zan baki zaɓi ba don kina da shi ba, I want us to make it work, I mean a shirye nake mu yi zaman lafiya da ke. Ina so ki manta baya, na son ba ni kike so ba, amma ƙaddara ni ta baki a matsayin miji. Ki yi haƙuri da irin wulaƙancin da na miki, give me this last chance Wifey, let me love you. Please." Ya ƙarasa zancen shi yana tsugunawa a ƙasa, idonshi taf da hawaye, nadama tsantsarta a fuskarshi.

Kuma kamar wadda aka yi wa asiri, sai ta tsinci kanta da ɗaga masa kai, alamun ta amince. To me amfanin ƙin amincewar? Ko da son Mahir zai kasheta tunda har wani ya aureta to ta haƙura da shi. An ce wai matar mutum kabarinshi, Allah ya riga ya rubuta ita ba matar shi ba ce. Abu ɗaya ta sani, zata cigaba da yi masa fatan alkhairi, kuma ko da zata so Jameel a nan gaba, ba zata yi masa ko da rabin son da ta yi wa Mahir ba. Daga ranar ne kuma suka shimfiɗa sabuwar rayuwa a gidan nasu...

"Mu bari sai mun yi azahar mu ɗau hanya, in muka yi sa'a ba lallai mu kai magariba ba zamu isa."  Muryarshi ta dawo da ita daga tunanin da ta tafi.

To kawai ta ce mai don tunanin haɗuwa da Umma na sa ta cikin ruɗani. Shin za ta yi accepting ɗinta a matsayin suruka?

*********

A ɓangaren Zuwaira kuwa tun bayan da ta ga takardar sakin da Mahir ya barwa ƴarta ba ƙaramin ruɗani ta shiga ba. Wane irin sakaci ta yi har aikin da ta shafe shekaru tana yi ya warware haka? Ta tuno kalaman  Boka Mugu shekaru uku da suka wuce:

"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki 'diga, 'digo biyu ina jaddadawa!!!, ki bawa Anisa ita zata hada ta kai masa, ba so ba ko zuciyarshi ce a jikanta ba zai aure ta ba, Anisa zai aura,amma duk ranar da Najma ta furta mai da kanta tana son shi ki Kuka da kanki don babu Ruwan Boka Mugu" Ya fada yana zare idonshi da ya sha farin kwalli.

Ta tuna ta mai alƙawarin hakan ba zata faru ba, domin ita a ganinta yarinya mai aji kamar Najma ina ita ina furtawa Mahir kalmar so?

"To amma ai Boka bai cewa ya yi kawai zai auri Anisa, bai ce auren mutu ka raba babe." Wata zuciyar ta raya mata.

"Ki kuka da kanki. Kashedin Boka ya ƙara yi mata amo a kunnenta karo na ba adadi. Anya kwabarta bata yi ruwa ba kuwa? Koma mene ne gobe zata koma gurin Boka ta ji. Bata bi ta kan Anisa da ke zaune tana aikin kuka ba ta kwanta bacci, wautar yarinyar na kai ta wuya. Wai kukan rashin mijinta take, To  akan me? Ba ita ta bi shawarar ƙawarta  ba yi family planning ba? Da a ce ta haihu da Mahir bai sake ta ba, in ma ya sakenta atleast za su ci rabonsu ta dalilin ɗan a ƙarshe ma su aika shi lahira ɗan nata ya gaje dukiyarsa. Kuma duk wannan bai isa ba, maimakon a ce jimamin irin dukiyar da suke neman rasawa take, ko kuma tunanin mafita take yi ta zauna tana asarar hawayenta a kan wani ƙaton banza...

Manage please

Najma da MahirWhere stories live. Discover now