Assalamu Alaikum, toh fah zamu cigaba da littafin nan, in da hali a dan koma a yi bita, nima sai na sake karantawa kafin in cigaba da rubutawa, amma kafin nan ga wannan a dan karanta.
Present
Sai bayan isha suka 'karaso gidan, ba laifi 'dan madaidaici ne mai 'daki uku(kowanne da toilet) sai parlour da kitchen a jikinshi. A waje kuma akwai bq da kuma 'dakin maigadi a kusa da gate.
Ko answer gaisuwar maigadin bata yi ba ta nufi gidan, sauri take ta 'karasa ciki ko za ta samu ta tsaftace kanta, shi Jameel dama ya da'de a cikin gidan ko tsayawa ya 'dan taya ta da kaya bai yi ba, yana yin parking ya bude gidan ya shiga.
"Maa Shaa Allah" ta furta lokacin da ta shiga parlourn, don ba karya iyayen nata sun yi matu'kar 'kokari, da ya ke 'yar gata ce, kowa ya gwangwajeta. Haka kawai ta ji ranta ya sosu, ta so a ce gidansu ne ita da Ya Mir dinta, tana tuno lokacin da take ce mai ita a gida babu abinda ya fi burgeta kamar katon kitchen, shi kuma ya ce ya fi son garden.
"Astagfirullah" ta furta a fili da ta tuna ita matar aure ce, auren da bata san a wane matsayi yake ba.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta nufi wani corridor da take tunanin zai sada ta da dakunan da ke gidan. Na farkon ta bude, babu komai sai katifa guda daya a ciki, sai ta jawo kofar ta rufe ta bude na biyun da yake a gaba, karar ruwa ta ji a ciki alamun da mutum a toilet, da ta kai dubanta kan gado sai ta ga kayan da Jameel ya saka a ranar, wannan ya tabbatar mata da cewar dakin Jameel ne. Dakin da ke kallon na Jameel din ta bude, kuma ba don ciwon cikin da ya dawo mata ba, da ta yi tsallen murna don ta san ba aikin kowa bane sai na Maamanta, an yi mata komai to her taste.
Bata bata lokaci ba ta cire lafayarta, ta binciko abubuwan da take bukata ta nufi toilet. Alwala ta dauro bayan ta yi wanka duk da dai ba Sallah za ta yi ba. Tana fitowa gabanta ya yanke ya fa'di da ta yi arba da Jameel. Ya sauya kawa zuwa na barci sannan har yanzu gashinshi a 'dan ji'ke ya ke alamun wanka.
Ta manta towel ne kadai daure a jikinta sai bayan ta lura da kallon kurillar da yake jifanta da shi, ba shiri ta rarumo lafayarta da zummar daurawa wanda kafin ta daura tsawar da Jameel ya daka mata ta yi sanadiyyar faduwar lafayar.
"Ke Mahaukaciyar ina ce? Banza jaka, an gaya miki ni sa'anki ne da za ki nemi ki wani rufe jikinki don ina kallo? An gaya miki akwai abinda zan gani a jikinki ne? To bari in gaya miki ban aureki don komai ba sai don in rabaki da wancan Banzan, na san kin manta lokacin da ya mare ni a kanki ko kin manta? To na aureki ne don in rama ba wai don ina son ki ba, in mayar da ke karamar bazawara." Ya tsaya ya sha ruwan da ke hannunshi kafin ya cigaba.
"Amma kin 'bata min shiri saboda gobe na yi niyyar in sakeki bayan na yi abinda zan yi da ke a yau, kwana nawa kike yi?"
"Sha biyar" Najma ta bashi amsa cikin gunjin kuka jin maganganu masu zafi da yake jifanta da su, dama ba sonta yake ba ya raba ta da masoyinta? Wannan wace irin zuciya ce ?
"To ki shirya, ranar da kika cika kwanaki sha shida a gidannan zan sake ki, banza kawai." Daga haka ya jefeta da ledar abincin da ya sa maigadi ya siyo musu, zuciyarshi tana raya mishi kamar ba zai iya sakinta a lokacin da ya ambata ba, kamar akwai wani abu da ya ke neman hanashi.
*****
Sai magriba ya isa gidan Salma a Wuse II, jirgin yamma ya bi, kuma ya yi sa'a suna sauka a airport ya tarar da Hafiz 'dan Salma na fari ya zo daukanshi."Wata sabon gani" cewar Hafiz bayan ya karbi jakar Mahir.
"Hmm yau dai na huta da gorin da ake min ga ni a birnin tarayya." Mahir ya bashi answer yana kawar da kanshi daga kallon natacciyar da take ta daugo mai hannu. Shi baya son naci, tun a jirgi ya ke fama da ita, ta fiya surutu, gata ba ta da kunya, komai ya zo bakinta fadi take. Ya tuno yadda ta dameshi dazu a jirgi.
"Hey mind exchanging seat? I think I'll be more comfortable on yours" Ya ji muryarta mai sanyi ta doki kunnenshi, ba wai muryar Najma bata da sanyi bane, bai dai taba jin mai sanyi irin wannan bane.
Bai yi magana ba ya tashi ya bata seat din, ba ya jin yana karfin yin magana, to mai zai ce? Bayan lokacin da ya kamata ya yi maganar bai yi ba, lokacin da ya kamata ya furta wa Najma yana son ta bai yi ba, yanzu me zai ce?
"Are you mute?" ta tambayeshi bayan ta zauna, ya kuma gode mata a zuciyarshi tunda ta cetoshi daga tunanin da yake yi na matar aure.
"No" ya furta a ta'kaice yana mai kallon agogon da ke manne a tsintsiyar hannunshi.
"Wow! What a melodious voice you've got, it can melt a mountain you know." ta fada da dreamy tone tare da kanne idonta daya(wink).
"Tana da kyau"
"Yes! I know ina da kyau, ka san wani abu? Ban san handsome guys irinka suna fadawa mace tana da kyau ba." sai da ta bashi answer tukunna ya farga, ashe a fili ya furta tana da kyau din.
"Munaya" ta fada mai tana mi'ko mai hannu.
"Nice name, ni kuma Mahir" ya fada bayan ya kalli hannun nata da ya sha lalle da zobuna.
"Wow, Mahir baka gaisawa da mata kenan, so nice of you, ni kuma ka ga a UK na taso but na ji Dad dina yana cewa zamu koma C..."
"Munayaa! Kai na yana ciwo, za ki iya yin shiru ki barni in huta?" Mahir ya tambaya bayan ya rintse idonshi, baya son ya yarda cewar ta fara yi mai kama da Najma.
"Sure, Allah ya kara sauki" ta fada a bit disappointed.
"So kwana nawa zaka yi mana?" Hafiz ya katse mai tunaninshi da tambayar.
"I have no idea, zan iya yin 1 week ko fi ma, ya danganta, saboda za a sabunta min Visa ne, ina so ne in koma Cyprus ne da zama.
"Cyprus kuma?me ya sa? Kai kadai ko harda Anty Anisa?" Hafiz ya jero tambayar bayan ya kunna motar.
"It's a long story, but let me cut it short, na gaji da Nigeria, na rasa komai, bani da kowa? Duk abinda nake so rasa shi nake yi, gwara in koma can tunda dama a can na yi masters dina sai in dora PhD kawai, maybe in iya gina wata rayuwar da babu Najma a ciki." Ya fada muryarshi na rawa.
Da Hafiz ya ga kamar Mahir din na bukatar hutu sai ya yi shiru, ba zai ce ya san duk abinda ya ke faruwa ba, yakan ji mahaifiyarshi na yi wa mahaifinshi complain akan abinda yake faruwa, sai ya yi mai addua kawai. Bai rasa kowa ba yana da su, ga 'kanwarshi Fatima, da 'karamin 'kaninshi Aslam, uwa uba ga Mamanshi da Babanshi, they are here for him.
Toh fah ga Munayah ta faso, what do you think?
Team #Najma
Team #Najmeel
Team #Mamun

YOU ARE READING
Najma da Mahir
Romance"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...