A gurguje
Shekarar Najma 'daya cif, Sumayya ta sami kanta da yin 'baki har guda uku, ba'kinda suka yi nasarar canza rayuwarta ,suka bu'de sabon babin rayuwar Najma da Mahir.
Tana cikin gyara kayanta ne ta tsinci takardar da Babanta ya aiko mata, gabanta ya fa'di tunawa mahaifinta da ta yi, duk da ba sha'kuwa a tsakaninsu sosai mahaifinta ne kuma tana son shi ,ta goge 'kwallar da ta zubo mata ta bu'de takardar.
"Assalamu Alaikum 'yar auta a gidan Labaran, ban san lokacin da takardar nan za ta riske ki ba, amma ina fatan duk lokacin da kika sami damar karantawa, ki nemi wani gurbi a zuciyarki ko ya yake ki yafe min laifukana a gareki, ki kuma nemarmin yafiyar yayarki, na san ban cutar da ita kamar yadda na miki ba, Na sani ni butulu ne, na ci mutuncin mahaifiyarku, na san ba'kin cikina ne ya kasheta, sai dai har yanzu ban san me ya sani aikata haka ba, ina son ku wallahi,sai dai ban san dalilin muzguna muku da na yi ba.
Ina mai baki hakuri akan auren ba zata kuma na dole da na yi miki, ina ji a jikina na kusa mutuwa ne, kuma na san in har na tafi na barki a hannun Hansai ba da'di za ki ji ba, na za'bi Yunusa ba don komai ba sai dan abokina ne, na san halinshi kuma na san ba zai ta'ba wula'kanta jini na ba, 'dan adam tara yake bai cika goma ba, za ki ganshi da wasu halaye marasa kyau amma duk da haka mutumin kirki ne, ki kula da kanki kuma ina barar addu'arki, Allah ya yafe mana gaba 'daya.
Daga Labaran Bala.
Tana gama karantawa ta yi shiru, ta fi minti talatin a daskare, ba ta san ma mai ya kamata ta yi ba, da tana da ikon dawo da hannun agogo baya, da taje ta sami Babanta ta gaya mai ta yafe mai kafin ya rasu,ta ta je ta sami Yaya ta saka ta yafema Baban nasu kafin ta rasu, da ta gaya mai matarshi Kausar ta yafe mai kafin ta rasu, da ta gaya mai abokinshi bai cika duk abubuwan da yake tunanin yana da su ba, da ta gaya mai ya saketa sakin wula'kanci, ya sheganta 'yarsa ta cikinsa, ya yi sanadiyyar shigarta mayuyacin halinda Allah ne ka'dai zai fitar da ita.
Kuka take, ba za ta iya tuna ranar da ta yi kuka makamancin wanda take yi ba a yanzu, kukan kewar kowa nata take, ba ta da mai rarrashinta kuma, sai da ta yi mai isarta ne 'karasa gyara kayan tana mai addu'ar neman gafara ga mahaifinta, mahaifiyarta da yayarta har ma da duka musulmi baki 'daya.
Ta zaci ta gama jin abinda zai daki zuciyarta sai dai kuma abinda ta ji Hansai da Zuwaira na fa'da ne ya kuma girgiza sauran abinda ya rage mata, ba su san tana nan ba sun zaci ta tafi wanki, kuma da ke 'dakin Labaran aka bata ya 'dan yi nesa da su ba lallai sun jiyo kukanta ba.
"Zuwaira, komai na tafiya yadda nake so, yanzu bani da burin da ya wuce ki auri mai ku'di yadda zamu huta, tunda ajalin Lado ne ya kaishi ga aurenki gashi cikin sauki mun kawar da shi. Ni dai boka Mugu ya gama min komai(Astagfirullah)."
"Hansai ai nima ba ki ga farin cikin da nake ji ba, ni fa da na ji shiru auren Sumayya bai mutu ba na zaci cin ku'dinmu kawai ya yi. "
"Lallai ma, to tunda ya kunna wutar gaba a tsakanin Labaran da Kausar me kuma ba zai yi ba, ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha,na rantse da Wanda ke busa min numfashi ko zanyi yawo ba kaya sai na ga bayan duk wani jinin Kausar,matar nan 'kiri-'kiri ta 'kwace min miji, ba don na yi da gaske ba da ban san mai zai faru ba. "
Haka suka cigaba da tonawa kansu asiri ba tare da sun san tana ji ba, suka gama suka shirya da niyyar zuwa gurin boka don a samowa Zuwaira miji mai kudi.
Tana zaune a 'dakin bata san awa nawa ta kai ba, ta san dai kiran Sallahr azahar ne ya tasheta. Ta kalli Najma da ke ta faman barci sannan ta 'dauki buta ta fita da niyyar shiga ban 'daki.
Fitarta ta yi daidai da shigowar su Hansai, ta ji wani abu ya tokare mata ma'koshi, kamar ta shake su su mutu kowa ya huta.
"Dama Ba ki fita ba? " Hansai ta tambaya tana mata kallon tuhuma, tana fatan a ce ta fita din kar su je ko ta ji abin da suka ce 'dazu.
YOU ARE READING
Najma da Mahir
عاطفية"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...