*2*

766 51 5
                                    

Yau ta kama ashirin da tara ga watan Ramadan, equivalent to 12 August, 2000.Da ga jin August ka san lokacin damina ne, Marka Marka wadda sai a jera kwana sha biyar ana ruwa.

Wani bakin hadari ne a garin na Kano unguwar Dorayi karama da ke karamar hukumar Gwale. Iska ake kadan kadan yayinda yanayin garin sai da san barka don ko ga mai jin barci, zai yi harda munshari.

"Mahir! In ka bari na zo nan na sameka wallahi za ka ci mugun duka, ba azumin ka 28 ba, yau na karshe ai sai ka daure, In ba ka kai markaden ba wa zai kai? Ga hadari ya hado in ruwa ya sauka kai zamu kwada mu yi buda baki? " Wata farar mata ce ke ta wannan sababin ta fito daga kitchen rike da wani dan karamin bokiti. "

"Yaya fitsari nake ji fah yanzu zan dawo. " Cewar Mahir da ke matse kafafu shi a dole fitsari yake ji. "

"Minti biyu na baka in ka ga dama kar ka fito. "

Tafiya ya yi da gudu ya banka wani daki ko sallama babu.

"Wai Mahir sau nawa zan gargadeka akan sallama ne? "Cewar wata mata da ta baje a kasa tana cin gyada.

"Ahh Maman baby yau kuma baby gyada take son ci? "Cewar Mahir yana zama kusa da ita.

"Eh to ya za a yi"Ta bashi amsa tana janye gyadarta don zaman Mahir a gun har ya ci biyar.

"Kawata ta amana yau ma ruwa na zo ki bani tun dazu in na je kitchen zan sha sai Yaya ta kunno kai. "

"Ka ji tsoron Allah Mahir shekararka 10 amma ba ka daina azumin moda ba,tsakaninka da Allah azuminka nawa? "

"Maman baby ban fa bagala ba, kuma 5 na yi ai na yi kokari gwara in mori dama ta kan ta Wuce ai.

"Ni dai duk sanda da Yaya ta kamaka ba ruwana, kar ka ce da sa hannuna. "

"Maman baby ni fa bana so a ga wata" Kallonshi ta yi da mamaki, shi dai ba aZumin nan yake ba, me damuwarshi da ganin wata

"Ka ji Mahir ba bagala ake cewa ba 'balaga'ne kuma me ya sa ba ka so a ga wata? "

"Allah maman baby so nake sai kin haifi baby musa kayan sallahr mu tare, anko ma zamu yi don ki ji" Ya ida zancen yana kallon katon cikinta wanda haihuwa ko yau ko gobe.

"Kai dai ka yi min addu'a Allah ya saukeni lafiya kawai. "

"Allah Maman baby in kika haifi namiji mun bata da ke, kar ki ce ban gaya miki ba tom."

Da wannan kashedin samun wurin nashi ya tashi ya nufi hanyar dan karamin fridge din dakinta, ya daddaki ruwa sannan ya fice yo markade.

Ko da ya dawo daga markaden drivernsu ya samu a kofar gida yana jiransa, nufarshi ya yi da kallon tambaya.

"Baba Idi ina wuni, ya na ganka da yammar nan lafiya dai ko? "

"Eh Yaya ce dama ta ce na dauko wasu abubuwa sannan in taho da kai asibiti, inaga kanwar nan tata ce... "

Ai bai karasa zancen ba Mahir ya doka wani tsalle, tare suka diro da bokitin markaden sai dai fa kowa da nashi wurin, tuni markaden ya malale a kasa amma gogan namu Mahir ko a jikinsa tini ma ya shige owner's seat farin ciki shimfide a fuskarsa.

Sai washegari wato ranar sallah ta haihu, ba wata wata kuwa aka kintsa ta ita da babyn sannan aka bawa 'yanuwanta damar ganinta.

Suna shiga ward din da take, Mahir ya yi arba da abar da yake matukar so a duniyar nan, Babyn Maman Baby.

"Maman baby kin cika alkawari, kawata ta amana kin biyani wallahi. " Ya fada yana daga mata tafin hannunshi suka ko tafa Suna dariya.

"Bani matata in dauketa, yau anko zamu yi dama na fada miki. "

Kuka ta canyara wanda ya tsorata Mahir matuka, ba shiri shima ya fara kukan harda majina.

"Ka ji dolon banza, me haka? " Mamanshi ce ta kwadeshi gami da maka mai harara.

"Yaya ba ta so in dauketa, Maman Baby ba cewa kika yi Baby matata bace? "

Ita dai Maman baby daga mai kai ta yi, tunanin da take daban, asirin da ta dade tana rufewa yau zai tonu.

"Sumayya ya na ga har yanzu Yunusa shiru ne lafiya kuwa? "Yaya ta tambayi kanwartata cikin nuna kulawa hade kuma da damuwa.

"Yaya na yi kuskuren boye miki halin da nake ciki, Yunusa kora ta yayi ba cewa ya yi in dawo gida haihuwa ba, ya ma yi rejecting cikin wai ba nashi bane. "

"Ba nashi bane? To na uban waye? Mu zai zubawa kasa a ido? Ba laifinshi bane laifi na ne. "Yaya ta fada cikin fada idanunta na kawo ruwa.

Ba su gama jimamin abinda suke ciki ba Yunusan ya yi sallama shi da matarshi ta farko Suwaiba.

"Na ga ita Yarinyar ma ta raba fada shari'a ta zo karshe kowa ya ga wannan ya san ba jini na bace, ni baki ne, kema kuma Sumayya baka ce, in dai ba mahaifinta ne fari ba, ba yadda za a yi ta yi wannan hasken. "

"Na sake ki Sumayya kuma tsakanina dake Allah ya isa, dama ba sonki nake ba kin sani, kaddara ce ta hada ni da ke kuma ta raba mu, ga wannan kya siya mata ko pampers ne kafin dan iskan ubanta ya zo gareta mun barku lafiya. "

Daga wannan Yunusa da Suwaiba ya fice taga dakin bai samu arzikin magana saboda gaba dayansu ba sa cikin Hayyacinsu a lokacin.

"Ki kwantar da hankalinki Sumayya bari in je in siyo kayan tea Mal idi ya manta da su kafin in dawo a san me za a yi, kar ki damu don wani kato ya ce ba ya sanki kin ji? Yayarki kadai ta isheki insha Allah wataran za ki yi dariya har ki gaji, kuma yarinyar da ya sheganta insha Allah za ta zamo tauraruwa a nan gaba, ni na yarda da ke, Kuma ina fatan Allah ya yarda da ke. "

Har Yaya ta kai bakon kofa ta dawo ta sunbaci Kanwarta da kyakkawar Babynta. Tana fita aka tsuge da wani ruwa mai karfi, ba a fi minti biyarba Mal Idi ya shigo dakin a guje yana haki.

"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un, bangon gidanmu ya rushe Hajiya, Allah ya yi wa Yaya cikawa, ginin nan sabo da ake yi ne ba a gama ba ya rushe kuma harda ita a cikin wadanda ya fadowa, Insha Allahu aljanna ce makomarta" Bai duba halin da take ciki ba na jego, duk da bai san da sakin da aka mata ba ,bai kamata ya sanar da ita mutuwar tilon yayarta tata ba, wadda ta zame mata Uwa da Uba da ma danginta baki daya.

Da me za ta ji ne?

"Allah ya jaddada rahama a gareki Yaya, na rasaki a yau, sai dai Allah ya musanyamin da makamanciyarki, Allah ya jikanki ya gafarta miki ya kuma raya Bilkisu Najma bisa tafarkin musulunci. " Daga wannan furucin ta yiwa Najma kiran sallah a kunne ta janyo Mahir da tun zuwan Yunusa yake kuka ta rungume tare da jariyar da ke ta tsala kuka.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now