In aka ce ta fadi yadda aka yi ta yi sati daya a gidanta ba za ta fa'da ba, alarm 'dinta ne ya tasheta daga barci, Kusan yanzu ta fara sarewa da yanayin kaddararsu ita da Mahir,komai da ya shafeta, in one way or the other sai ya shafeshi. Alarm din nata ma shi ya saka mata. Lokacin da Abbu ya siya mata waya bayan ta gama secondary school ne, dama ya dade yana mitar ba kullum take tashi Sallahr Asuba ba, ana kawo wayar kuwa ya saka mata alarm. Tun daga lokacin take 'ko'karin tashi.
Ba ta san kuka take ba sai da hawaye ya 'diga a hannunta, ya ci a ce ta yi hakuri haka, toh amma in ta tuna da Jameel ba sonta yake ba saboda fansa ya aureta sai ta ji duniyar ta mata zafi.
Gashi abokan shawarar tata dama su biyu ne, Mahir da Jalila. To yanzu ina ita ina kaiwa Jalila 'karar yayanta? Bayan ya gama nunawa duniya irin son da yake mata, ko mutuwa take tana tashi ba wanda zai yarda Jameel baya son ta.Duk da Jalila bata goyi bayan auren nata ba, a cewarta sun fi dacewa da Mahir sannan kuma she was too young, ita in so samu ne Najma ta shiga Uni ko a level 3 ne sai ta yi aure amma da ya ke Abbu ba 'dan boko bane sai ya matsa akan lallai sai ya aurar da ita ta yi girma haka a gida.
Share hawayenta ta yi kafin ta sauka daga kan gadon, kunna karutun Qur'ani ta yi kafin ta fara gyara da'kin nata duk da ba wani datti ya yi ba. 'kira'ar Sheikh Sa'ad Al-Ghamidi ce, Suratul Nisa'i,tana aikinta tana bi tunda dama ta haddaceta tun tuni. Da ya ke ta san fassarar ayoyin sai ta ke ji ina ma a ce Jameel ya san irin matsayi da gatan da Allah ya yi wa mace, cusguna mata da ya ke yi a gidansa ya kan ɗaure mata kai, baza ta ce shi jahili bane, tunda kusan za a ce ta rayu a gidansu na wani lokaci, ta san irin tarbiyyar gidansu, bata san me ya sa ya zama haka ba, duk da a 'dan zamanta a gidan ta fahimci yana bin maganar abokansa, kwananta biyu a gidan ya fara kawosu, a nan suke lunch harma dinner, kuma wani samun wuri su suke fadar abinda za su ci ta dafa musu. Da ta so ta yi mai complain sai da ya kusan zaneta a gidan. A gabansu ya mareta ranar da ta dafa musu Macroni instead of Taliya, bayan ba laifinta bane, cewa suka yi suna so su ci Pasta. Kuma wani abinda ya daure mata kai ba wani a cikin abokan da ya yi yunkurin hanashi sai ma ihun da suka rika yi suna zugashi, wai ya fara gane hanya ya zama namijin duniya.
Lokacin da ta kai kan aya ta 11, wani lokaci a can baya ya fado mata, bayan sun dawo daga Da'kasoye da kwana 'daya suna hira da Mahir tana gaya mai abinda ya faru da 'kawarta Jalila. Kawai sai ta sami kanta da fashewa da dariya, dariya mai hade da mamaki, za ta iya cewa rabonta da ta yi dariya irin haka tun lokacin da ta ji an daura auren Mahir da Anisa, a lokacin dama ya daina kulata, a bakin Jalila ta ji.
Past
" Ya Mir ba za ka gane bane, wai fah shara ma bi- da -bi ake yi, kuma wai sai sati-sati, ga toilet ma sai yi wata ba a wanke ba. Ni kam suna bani mamaki." Ta fada tana jinjina kai hade da tabe baki.
"Bari kawai, daina tuna min mun ta'ba kwana a gidan ai ni da Dad lokacin kina 'yar 'karama, da 'kyar na iya karyawa a gidan, gashi dai suna da yawa har da maza magidanta amma kwata-kwata ba su san abinda ya kamata ba."
" Kar ka so ka ga fuskar Lila da ta fada a kayan wankin nan..." kafin ta ' karasa ta kuma fashewa da dariya a karo na ba adadi.
"Wallahi ba ruwana, ki cigaba da yi mata dariya ke da ita, kin san halinta ai."
"To ni me za ta min? Ni na ce kar ta bi Umma Denmark ne? Ita fa har mamaki ta yi wai da suke zaune haka da yawa a gidan, kowa fa daki daya ne da shi; da shi da matarshi da 'ya'yan ai ya musu ka'dan." Ta kuma fada tana mai neman game a wayar Mahir.
"Hmm toh da aka ci saa ma kowa yana da 'dakin, kin san gidan gado ne ai, da cewa suka yi za su raba gidan biyu su bayar da wani haya, daga baya ne kuma suka ga hakan ba zai yiwu ba suka hakura."
"To wai ni banda Maama ne a gadon? Na ga ita bata zaune a can." Ta tambaya tana mai cuno baki.
"Harda ita mana, kawai dai tun da basu so su sa su a cikin harkar ba, tun kafin ma Yaya ta rasu balle ma bayan ta rasu, ai su kam sun hakura."

YOU ARE READING
Najma da Mahir
Romance"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...