Ta sauke ajiyar zuciya tana mai kallon Mahir, yaron sai ya kuma bata tausayi, ya ri'ke hannun Najma yana sauke ajiyar zuciya akai-akai.
"Babansu Jalila ko za ka yi wa Yaya allura? Ko kuma ka yi mata 'karin jini, 'kila jininta ne ya 'kare shi ya sa ake cewa ta rasu, ka je ka duba ta don Allah ko zata tashi. " Mahir ne ya yi maganar a karon farko tun bayan da aka ce Yaya ta rasu.
Haka kawai zuciyoyin Sumayya da Dr suka matse guri guda, suka kalli juna sannan suka kalli Mahir da ya yi maganar, idonshi cike da ro'ko yana kallon Dr da hope ko zai je ya tashi Yayar.
"Babu abinda zan iya yi abokina, ka yi mata addu'ar dacewa da aljanna, muma in muka dace sai mu je mu sameta a can. " Dr ya matsa ya ri'ko hannun Mahir din ya sauko da shi daga gadon asibitin, ya rungumeshi yana mai jin tausayinshi. Ya san shi tun kafin ranar, abokin 'danshi ne Jamil, yakan wuni a gidanshi wataran ma sai dare Sumayya take zuwa ta tafi da shi gida, da alama Sumayyan bata ganeshi bane, amma shi ya santa sosai, ba shi kadai ba har ma zuciyarshi ta santa, ita ce mace ta biyu da yake jin zuciyarshi ta amincewa, ta farkon ita ce matarshi Shafa'atu.Ko da ya ji labarin ta yi aure bai ji da'di ba, amma yana ganin wata damar ta sameshi kuma ba zai yi wasa da ita ba, zai bata lokaci ta yi jinyar zuciyarta ne kawai.
"Ina ga zan sallameki yanzu, za'a yi necessary preparations a taho da gawar Marigayiya a ambulance, mu je sai in saukeki a motata, na yi sending ma Ahmad text message, so na san by now shima zai fara shirye-shiryen yadda za a kaita makwancinta. "
"Sai yanzu ta gane Dr din, Babansu Jalila dai da Mahir ya ke ta zance. " "Yana da kirki" ta ayyana a ranta tana mai tashi daga gadon a sanyaye.
Tafiya sukeyi akan titin da dan gudu, duk da titin a cike yake da mutane saboda masu zuwa sallahr idi bai hana su samin hanyar wucewa ba, dalili kuwa jiniyar ambulance din da ke gaban motarsu.
Sumayya na ta mamakin yadda fuskokin mutane ke cike da annuri, farin ciki zaune a fuskarsu saboda ranar sallah, sai dai ita sabanin haka ne a fuskarta, babu walwala ko kadan a fuskarta, hawayen ne dai babu,ta yi kukan ne har ta gaji, Mahir dai ya 'dan samu barci a motar, ya dora kanshi a kan kafadarta, har lokacin ajiyar zuciya yake.
Suna isowa Dr ya kar'bi Najma da niyyar kaiwa matarshi ta ri'keta kafin a kimtsa Bilkisu, ya yi niyyar ha'dawa harda Mahir sai dai gogan namu ya nuna bai san zancen ba, fafir ya 'ki, ya ringa ihu kamar Allah ya aikoshi ba shiri ya rabu da shi.
Sumayya na shiga gate din gidan ta ci karo da Ahmad, Mahir ya tafi da gudu ya rungumeshi yana 'kara 'karfin kukanshi, a 'dan lokacin nan har ya fita hayyacinshi, idanunshi sun yi ja, kukan ne dai ba ya yi a fili sai dai na zuci.
"Ya hakurinmu? An sami kai kalau kuma? " Ta tsinci muryarshi da ba komai a cikinta sai rauni, sai ta ji ya bata tausayi, rashin mata kamar Yaya ba abu ne mai sauki ba.
"Da godiya Alhamdulillah Ya Ahmad, Salma fah? Ka sanar da ita? " Ta bashi amsa tana share hawayen da take tunanin sun 'kare.
" Eh na sanar da ita, kowane lokaci tana iya isowa, Mahir cikani in je in sanarma liman in sakko insha Allah za a kaita."
"Daddy kaima ba za ka iya tashinta ba? Waye zai mana tuwon sallah to? Gashi jiya na zubar mata da markade ko hakuri ban bata ba. "
Sumayya kuma fashewa ta yi da wani kukan, Ahmad kuma ya raba Mahir da jikinshi yana yin hanyar waje,don in ya tsaya shima zai iya saka kukan, kafin ya fita Salma ta sako kai, tana ganinshi ta rungumeshi tana kuka kamar ranta zai fita, dama ta yi missing dinshi, ga kuma mutuwar da aka yi, zai iya cewa a duniyarshi daga ita(Salma), sai Mahir suka ragemai, tun tana shekara tara mahaiyarsu ta rasu, Babansu kuwa burinshi ya nemi kudi kawai ya tarasu, tun bayan da Mahaifiyarsu ta rasu bai 'kara aure ba, dama rabonsu ne ma ta kai shi ga yin auren,baida lokacinsu sam, kullun cikin yawon kasuwancinsa yake daga yau yana wannan 'kasar gobe yana waccen 'kasar.
"Salma yi shiru mana, kina so in yi mene? Bara in je in sanar da Imam rasuwarta, ki shiga ke da Sumayya ku yi mata wanka,na ga ma'kota ma na ta shigowa. " Da wannan zancen ya fita ya nufi masallacin da ke bayan layinsu.
*
"Sumaii don Allah ki ce min mafarki nake, da gaske wai kin haihu? Wai kuma Yaya ta tafi ta barmu? ""Salma nima na kasa yarda, duba ki ga kamar za ta yi magana, fuskarta da murmushi ma, kina gani? "
"Bayin Allah da kun daina surutun nan an shiryata,babu abinda tafi bu'kata sama da wannan." Wata ma'kociyarsu ta yi maganar.
Cikin ikon Allah aka kammala shiryata, aka bu'kaci makusantanta da su je su yi mata addu'a.
"Bilkisu, kin tuna ranar da na fara ganinki? Ranar da kika bani wallet dina da na yar, halinki na gaskiya da taimako da kika nuna ya ja ra'ayina akanki, ba zan ce bamu ta'ba samin sa'bani ba amma ban ta'ba ri'keki a raina ba, to ya za a yi in iya haka koda na so? Halinki na gari ba zai barni ba, indai aljannarki a 'kar'kashin 'kafata take to na 'daga miki matata, Allah ya ha'damu a aljanna, Allah ya haskaka kabarinki, halinki na gari ya biki,Allah ya bani ikon ri'ke tilon 'danmu..." A fili Ahmad yayi addu'ar da alamu ba ma a hayyacinsa yake ba, kafin ya 'karasa kuka ya ci 'karfinshi, ba zai iya tuna lokacin da ya zubarda hawaye ba tun girmanshi, amma to ya zai yi? Matarshi sanyin idanuwarshi ce fa ta rasu kuma ta tafi kenan ba za ta dawo ba.
A bangaren Sumayya ma haka abin yake;
"Allah sarki Yaya, kin tuno lokacin da muke guduwa makaranta muce muna da lesson kawai don kar mu yi aikin gida, kin tuno lokacin da kike min wayo da alawa don kawai in zauna a makaranta, kin tuno al'kawarin da kika min na cewar zamu je gida yawon arba'in, Yaya zan yi kewarki, daidai da rana 'daya baki ta'ba barina na yi maraicin mahaifiya ba, baki ta'ba bari na yi kewar mahaifi ba, ke ce kika maye min gurbinsu, ke ce 'kawata, abokiyar shawarata, yanzu mutuwa ta min adalci kenan? Yaya akaina kika rasu, da mijina bai koroni ba da a gidana zan haihu, da baki rakoni asibiti ba, da gini bai fa'do miki bah... Allah ya jaddada rahamarshi a gareki, Allah ya yafe laifukanki, insha Allah aljanna ce makomarki Yaya. " Da 'kyar aka janyeta daga kan gawar tun tana kallon Mahir da yayi 'kuri yana kallon gawar mahaifiyarshi har duhu ya mamaye dakin ta fadi a sume sai waje aka yi da ita.
Mahir ne ya matsa kusa da Babanshi kafin ya ce:
"Daddy, ka ga ita Yaya tana jin magana ba kamar ni da bana ji ba, ka tayani bata hakuri, wallahi Yaya azumina biyar ba ashirin da takwas ba, duk sauran na mo'da nake yi, jiya ma da kika ce in je marka'de na ce ina jin fitsari 'karya nake yi, 'dakin 'Kawata na je na sha ruwa har gya'da ma na ci, kuma na zubar miki da marka'de, Yaya na san bana ji amma na yi al'kawari in dai kika tashi zan shiryu, zan ringa yin homework ba sai an sani a gaba ba, zan daina yawo kuma kinga gashi an ma haifi Baby, kuma an saka mata sunanki,kuma za a ringa kiranta da sunan da nake so 'Najma',kuma 'kawata ta ce matata ce, ki tashi ki ga ankon da za mu yi, ba na fa'da miki kaya iri 'daya zamu sa ba ranar sallah? "
😩Allah sarki our Yaya, Allah ya jiqan musulman da suka rigamu gidan gaskiya, in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani.
Vote, Comment and Share.
YOU ARE READING
Najma da Mahir
Romance"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki...