*7*

369 27 2
                                        

Cikin watanni hu'du abubuwa da dama sun faru,Sumayya  ta yi shirin komawa 'kauyen da'kasoye da ke 'karamar hukumar Bunkure a jihar Kano ta dabo tumbin giwa.Dama 'yan garin ne, lokacin da ku'di suka zaunawa Labaran ne ya sai musu gida a unguwar Zoo road da ke a jihar Kanon dai, bayan rasuwarsa ne aka sayar da gidan saboda rabon gado. Su Sumayya ba wani samun abin arzi'ki suka yi ba, Hansai da 'ya'yanta da duk kafin mutuwar Labaran suka yi aure suka danne. Dama Labaran dinne yake ciyar da su, da ya rasu kuma suka ga gwara su koma 'kauye su kama noma,ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

Jinyar kwana hu'du Labaran ya yi ya rasu, su Bilkisu basu sani ba ma sai wata wasi'ka da ya aiko Habu takanas ya kawo wa Sumayya, a lokacin ne Alh Yunusa ya ga matar tashi da Habu, bai tsaya ya ji ba'asi ba ya dauki zargi ya sa a ran sa, bayan rashin yarda da kishi irin na Yunusa, harda 'karin mugun asirin Hansai na san raba auren dan ita gani take an 'dau 'yarta Zuwaira an bawa wani banza manomi ita Sumayya ta je gidan maikudi. Allah ya yi dai ba a lokacin auren zai mutu ba, sai ranar da ta haifi 'yar da bambancin ta da Yunusa haskene sai kuma hancin Sumayya da ta dauko.

Ta kalli 'yar tata da take ta barci, sannan ta kalli hanya tana jin sun kusa isowa garin nasu.

A gidan Bilkisu ta zauna na tsahon wata hu'dun da ta dauka, in ta ce ga yadda ta yi coping da rayuwar gidan ba tare da yayarta ba ta yi 'karya, ita da Salma suka zauna ta ci sa'a kwana uku da rasuwar Bilkisu mijinta ya tafi wani conference a 'kasar Cuba, haka suka zauna kullum hirar Yaya suke, da Yaya tana nan da tuni an yi kaza da kaza. Ta bangaren Ahmad kam abin ba sauki, ba ya dawowa gida sai can dare, ba shi da aikin yi sai tunani, ranar weekend zai 'dauki Mahir su tafi park ko ziyarar 'yan uwa, yakan 'dauki Najma ya yi mata wasa in Mahir ya bashi damar yin haka don kuwa in dai ba barci Mahir din yake ba, ko kuma Sumayya ce za ta 'dauketa, sai an kai ruwa rana kafin ya bawa kowa ita, har kirari ake musu da ga Zara da wata. Har goyata yake ba ruwanshi ya tafi gidansu Jameel, ko a jikinshi in an tsokaneshi don kuwa ko tankawa ba ya yi, Mahir mai surutu da rashin ji ya dawo shiru-shiru yanzu, in ka ji bakinshi to Najma yakewa wasa.

Ana kiran Sallahr magariba ta isa gidansu, tana jin bugun zuciyarta na 'karuwa lokacin da ta yi tozali da 'kofar gidan,da kwatance ta zo gidan don bata ta'ba zuwa ba, a gidansu na zoo road aka haifeta kuma a nan ta taso har aka yi mata aure.

Da sallama ta shiga gidan, wani wari na mata lale marhaban, da duk alamu kuma daga ban'dakin gidan yake fitowa, wata mata ce ta amsa mata sallamar wadda ba tantama matar 'daya daga cikin yayyanta ce.

Hansai ce ta fito daga 'ban daki ri'ke ta buta tana sauke numfashi, kafin ta fara sababinta da ahalin gidan suka saba da shi.

"Wai Mariya ba ke ce da shara ba yau? In zan iya tunawa wancen satin ai Tani ce ta yi shara, ke dama kin fiya rinto kullum sai satin shararki ya zagayo kike ciwon ciki, bari Ayuban ya dawo zan sa ya min maganinki tunda ke mijinki ka'dai kike shakka, Ja'irar banza kawai. " Ta ajiye butar tana waiwayawa kuwa ta yi ido hu'du da Sumayya.

"Wa nake gani kamar Sumayya? Kai jama'a ikon Allah,ya ha'kurinmu kuwa, ai da zan taho tare da su Murtala sai kuma jiki ya matsa min, shi ya sa ma ba ki gan ni ba,ya yaronta kuwa Mahir? " Hansai ta fa'da cikin borin kunya don ko a waya bata kira Sumayya ta mata ta'aziyya ba. Yaranta dai sun je har gidan Bilkisu, sai da suka yi sati biyu suka dawo.

"Ina wuni Baaba,hakuri da godiya Alhamdulillah, yi ha'kuri fa na yi muku zuwan ba zata. " Sumayyan ta fa'da ta nemi inda ba datti sosai a gidan ta shimfida 'dankwalinta ta zauna don ta ga alama ba bata wurin zama za su yi ba.

Tana kallon Zuwaira a zaune kan tabarma sai shan kamshi take, ri'ke take da jaririyarta da ta girmi Najma da wata Shida, sunan mahaifin tsohon mijinta Lado aka saka mata, wato Aisha amma ana kiranta da Anisa.

"An sami mai wankin bandaki, dama babu mai wankewa, da fatan dai za ki da'de? " Tani matar Murtala ta fa'da tana ta sosa kanta wanda babu makawa in dai ba amosani ne a kan ba to kwarkwata ce.

"Kai Tani daga zuwanta,ai kya bari ta 'dan huta ko, ku wallahi haukanku yawa gareshi. " Zulai matar Habu ta fa'da tana fifita wutar murhu, da alama ta 'dan fi su hankali.

"Ko zan sami ruwan alwala, ko la'asar ban yi ba wallahi? " Bilkisu ta tambaya tana kwance goyon Najma.

"La haula fi sha'atillahi, ku tayani tubawa 'yar tsana ce wannan ko kuma 'diyar mutane kika sato baiwar Allah? " Gambo matar Yawale ta doka tsalle ta 'buya a bayan Ramma matar munzali, dama ita akwai tsoro, balle ga duhun magariba ya ha'du da hasken Najma.

"A'a wallahi, 'ya ta ce, sunanta Najma, haskene dai Allah ya bata." Sumayyan ta tsaya ri'ke da 'yar tata an rasa mai ri'keta, suna a haka ne Habu ya dawo daga masallaci da suka gaisa kuma ya kar'bi Najma, shi dama ba ruwanshi, yana da hankali ba laifi.

*******
Bayan sallahr isha'i ne Ayuba ya kira gaba 'daya ahalin gidan.

"Dama muhimmin abinda ya sa na tara ku a nan bai wuci ba'kuwar da muka yi ba a yau, kowa ya san yadda muke kai gwauro mu kai Mari kafin mu samu a sami abinda za mu ci, don haka ba wani 'boye-'boye, Sumayya abincin kwana biyu kawai zamu iya baki, daga nan sai ki san inda dare ya miki. " Ayuban ya koro jawabinshi yana huhhuro hanci shi a dole Babban yaya.

"Yaya Ayuba in ka ce haka a matsayinka na yayana kamar ba ka min adalci ba, yanzu a matsayin ba'kuwa ma ka 'daukeni? To babu wai 'boye-'boye, aurena ya mutu, yayata kuma da nake zaune gurinta ta rasu, bani da inda ya wuce nan. " Ta fa'da tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, sai dai fa banda zuciyar Hansai harma da Zuwaira,burinsu ya cika auren Sumayya ya mutu.

"To tunda kin kasa zaman gidan aurenki, sai dai ki kama sana'a, matan gidan nan duk da akwai abinda suke yi, kema ki yi shawara ko Wankau ne sai ki fara, kya ringa 'dan taimakawa. " Daga haka ya tashi daga wurin, taro ya watse aka barta da tunanin makomarta.

*********

Satin Sumayya 'daya a gidan amma in ka ganta sai ka yi mugun tausaya mata, ta 'kara yin 'baki, ta yi wata uwar rama, bata san 'kazanta shi ya sa ta ga ba zata iya jure sharar sati-satin da ake yi ba a gidan, haka za ta yi shara, ta wanke toilets biyun da ke gidan sannan ta tafi 'debo ruwan da zata yi wanki da shi, dake 'kauyen ba wai 'kauyen 'kayau bane, akwai  'yan gayu da basa wanki da suke bata ta yi musu akan duk set 'daya naira talatin, haka ta amince ta kar'ba ko ba komai ta samu na siyawa Najma Pampers.

Da yamma in ta dawo haka za a sata ka'din audugar da su Munzali suka kawo, in ta gama ta 'dora da girki don a cewar Hansai, girkinta ya fi da'di.

Kullum cikin dare takan tashi ta kai kukanta ga Allah, ta yi kuka na fili da na zuci, takan yi tunanin da ace Yaya ba ta rasu ba, ko kuma da mijinta bai saketa ba da ba haka ba, sai kuma wata zuciyar ta ce mata haka Allah ya rubuta zai faru da ita ta zama mai tawakkali.

Note;:'Kauyen Da'kasoye da na sa ban san ko akwai shi ba a gaske,na rasa sunan da zan sa ne shi ya sa na saka.

Najma da MahirWhere stories live. Discover now